← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 242

Sashe 190

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙin karɓa ta yi ta tsare shi da kallo, ya san me take yi wa dan haka sai ya zuba drugs ɗin a saman wani small plate dake wajen, sannan ya ɗauko ruwa ya buɗe mata bakinsa, ya ajiye mata su ready kafin ya juya ya nufi hanyar fita abinsa, wato idan ta ga dama ta sha, in kuma bata yi niyya ba sai ta barshi ko ohonsa, ai jikinta ne zai gaya mata. Anya ba dan ma babynsa yasa yake damuwa da ita ba kuwa?. To mu je dai zuwa.

Ganin fita zai yi yasa ta yi gaggawar miƙewa tsaye, muryarta na rawa ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka tsaya ina san yin magana da kai". A tsorace ta yi maganar, dan tana fargabar abin da zai iya faruwa a tsayawarsa ko buɗar bakinsa. Tamkar ba da shi ta yi magana ba, ya cigaba da tafiyarsa. Ai a miliyan ta watsa da gudu ta tare gabansa, har sai da ya ji wani irin shock jin yadda ta yi gudun, ya ɗan ji fargabar kada ta faɗi. Meyasa ya damu da ita haka? Meyasa kuma yake kula da ita har haka? Meyasa baya san wani abin ya taɓata ko kaɗan ne? Akwai ayar tambaya fa a lamarinsa!.

Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi, ya haɗe gerar sama da ƙasa, kwata kwata yaki yarda ya kalleta, with harsh voice ya ce. "Bani hanya in wuce!"....... Marairace fuska sosai ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri, na san na yi kuskure, amma na tuba ba zan sake ba!"........ Ƙara daure angry face ɗin ya yi, murya a kausashe ya ce. "Kuskure?! Da wani abin ya same ki shi ma zaki kirasa da kuskure ne?! Kin san risk da kika gefa kanki damu bakiɗaya a ciki kuwa? Kin san yadda ake farautar rayuwarki kuwa? Kin san halin da kike ciki kuwa? Kin san matsayin lafiyarki a wajena kuwa?!".

Tin da ya fara magana idanunta a kansa, bata taɓa ganin ya yi magana cikin zafa har haka ba, hasalima baya ɗaga murya a magana sai yau, da alama ta yi babban kuskure ne ba karama ba.
"Ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba ko da sunan wasa?" Cikin marairacewa sosai ta yi maganar. Nisawa ya ɗan yi, yadda ta marairace murya tasa ya ji wani irin a cikin ransa. "Shin kin san mutanen da suka biyoki daga fitarki har izuwa in da kika je kuwa? Kin san rayuwarki tana gab da zuwa karshe a lokacin da muka isa gareki kuwa? Ko kin ɗauka na damu ne saboda ciwon da kika jama kanki na ruwa da ya dakeki?". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu ya damkar rigar jikinsa, karfi yasa wajen tsaga rigar gida biyu, jifa ya yi da ita gefe tare da sanya hannun nasa ya yi mata nuni wide chest ɗinsa da gabaɗaya yankar wuka ne a wajen, sai dai ya sha treatment sosai, almost yanka 4 masu zurfi ne a wajen, ga ɗaya a saman shoulder ɗinsa wajen damatsan hannunsa. "Diba abin da kika ja mun, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu wani maganar ake yi a kanki ba wannan ba, kin yi zatan saboda abin da ya faru a tsakaninmu ne yasa na ɗaukeki daga gidan uncle? To idan ma haka kike zata kin yaudari kanki, ina san ki san cewa a gidan uncle rayuwarki cike take da barazana, ko kin yi zatan ban san attacking ɗinki da aka yi a ɗakinku daren ranar bane? Dik ina sane da komai, that's the reason why na ɗauke ki daga gidan, amma dik baki yi tinanin komai ba kika sa kafa kika fita". Cikin ƙunan rai ya yi maganar!. Ta bashi haushi sosai!!

Wani irin zaro idanu ta yi a lokacin da ta ga yankar dake jikinsa, ta tsorata sosai, ashe yana kan gaskiya fushin da yake yi da ita, ashe ta tabka babban kuskure na fita da ta yi ba tare da izininsa ba, yanzu ta ja mashi ciwo, ta kuma ja dole ya canza masu gida, ta ja mashi abubuwa da daman da bai bayyana mata ba, ciki har da rasa abokin aikinsa da ya yi, sun kashesa, sun zo harbinza da bindiga ba tare da saninsa bane babban yaron nasa ya tare masa, harbin ta same shi Allah ya yi mashi cikawa, dik a bayanta da suka bi, da ita za'a kashe Allah yasa bai ajiyeta ƙara zube ba, dik motsinta yana sane da shi, lokacin da ta fita daga gidan watch dake hannunsa ta buga mashi alarm na an buɗe gate na gidan, Allah yasa bai yi nisa ba shi ne ya juyo ya dawo, dan in baku manta ba yana fita ba'afi da 10 mins ba ta fita ita ba, so bai yi nisa da ita ba, da yana nesa ma ai da ta jima da mutuwa. Shi da farko ma bai yi zatan ita ce ta fita ba, ya yi zatan ko wasu ne suka shiga cikin gidan, sai da ya juyo ya dawo, can ya hangota a hanya tana tafiya!.

Lokacin da ya biyo bayanta ya so ɗaukarta tin time da ta fita arearsu, amma sai ya lura da wata black car dake biye da ita a baya, hakan yasa ya kira babban yaronsa da ya zo da wata mota mai tinted su bi wannan mota. Mutanen dake bibiyarta sun cigaba da binta suna san ta matsa daga idanun mutane su ɗauketa su aiwatar da nufinsu a kanta, shi ma kuma ya cigaba da binsu dan ya kamasu, abin da yasa bai yi gaggawar bayyana ya kamasu ba shi ne dan bai san su nawa bane, watakila bayan wannan mota akwai wani a ɓoye bai sani ba, hakan yasa suka cigaba da binsu da taƙa tsantsan. Lokacin da ta fita daga cikin mutane sai suka yi ƙoƙari kamata, amma sai suka ga kamar asirinsu zai iya tonuwa, wannan dalilin yasa sai suka yi yunƙurin harbinta daga ɗan nesa da ita kenan, a zuwan idan suka harbeta sai su gudu kawai, Allah yasa Ramish ɗin ya fita shi da yaronsa suka tinkaresu, a nan suka yi wannan faɗa har suka jijji mashi ciwo, suna tsaka da faɗar ne ɗaya ya zari gun zai harbi Ramish kenan babban yaronsa ya tare suka fasa mashi ƙwaƙwalwa, haƙiƙa Ramish ya ji zafin mutuwan yaron nasa, saboda sun haura sama da shekaru 7 suna a tare, sun saba kaman ƴan uwa.

Waiwaye adon tafiya🔥

Ina ranar da suka je wajen cin abinci a tare da shi har aka yi ta yi masu hotuna? Waɗan nan hotuna su suka baza media har masu nikaf suka san in da suke, a take suka tura mutane suka biyo bayansu, a nan ne suka rinƙa bibiyarsu har suka ga arear da suke, shi ne suka cigaba da gadin fitowar Leesharh ita kaɗai, sai a wannan lokaci Allah ya basu dama, to kun ji a ta yadda suka yi suka san in da suke har suka bi bayanta.

Ta shiga tsananin tashin hankalin da yasa gabaɗaya ilahirin jikinta ya fara kerma..... "Yah Ramish ka yi hakuri, kwata kwata ban kawowa rai'na akwai abin da zai iya faruwa dani dan na fita ba, ina mai baka hakuri kuma ina mai jajanta maka a kan rashin da ka yi". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah, haƙiƙa ta ji babu daɗi matuka a kan abin da ya faru, hannunta na kerma tana san taɓa ciwon nasa ta kara bashi hakuri, dik ta bi ta ruɗe kamar wata zararriya. Kan kace me hawaye sun fara zarya a saman face ɗinta, jikinta dik ya yi la'asariyar jemage. Yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa, bai sake ce mata komai ba. Hannunta na rawa sosai kamar wadda aka sanyawa lantarki, cikin tsananin damuwa ta ɗaura a saman wide chest ɗinsa, hawayen face ɗinta suna tsananta gudu matuƙa.

Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa jin yadda ta taɓa shi. Slowly ta ɗago da kallanta a kansa, while shi ma ita yake kallo. "Sannu ka ji? Ni na tsani kaina, ban san meyasa a koda yaushe nike aikata irin waɗan nan abubuwa ba, kwata kwata bana amfani da ƙwaƙwalwarta da tinanina, kullum sai na aikata abin da zan zo ina danasani, na shiga uku na, wai menene yake bibiyar rayuwata haka ne? Shin na yi wa wani laifi ne? Wani zunubi na aikata?". In out of control take surutan nata, tana magana tana kara tsananta kukanta...... Lokacin guda tsananin tausayinta ya mamaye zuciyarsa, hannu yasa ya riko hannunta dake saman kirjinsa, muryarsa a ɗan sarke ya ce. "Ya isa haka, komai da ya faru ya rigada ya wuce, je ki yi dinner ki sha magani sai ki kwanta ko?".

Kai ta fara girgiza mashi tana wani irin kuka irin wanda zuciyar mutum yake a kusa ɗin nan.. "i can't eat anything Yah Ramish, na tabka babban kuskure, ni ban san menene ma ya shiga kai'na ba, ni mahaukaciya ce kawai wanda bata da tinanin kanta, kullum cikin jefaka a cikin masifa nike, na tsani kai'na". ..... "Aesh! Stop saying all this, ke yarinyar kirkice mai zuciyar zinari, dik abin da kike aikatawa rashin samun ishasshen ilimi ne da kuma ƙarancin shekaru ga rashin natsuwa da kwanciyar hankali, amma tabbas ke yarinyar kirkice, ke ɗin jaruma ce, ba kowace mace zata iya kwatanta abubuwan da kika yi ba, cikin mata dubu da wuya a samu goma da zasu iya abin da kika yi, mahaifinki fa suka kama, amma dik da haka kin jure kin ce ba zaki yi masu aiki ba, Allah zai kula da babanki, In Sha Allah babu abin da zai same shi, zai dawo gareki cikin aminci". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.......... "A'a Yah Ramish, ni mahaukaciya ce kawai, kuma zan tabbata a haka tin da bana tinani da ƙwaƙwalwata". Tana magana tana girgiza kai, tamkar wadda ta zauce, ta fita a hayyacinta sosai!.
Chapter 190 · 0% Book details