← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 242

Sashe 136

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A maimakon ta yi mashi sallama irin ta addinin musulunci ma sai ta wani kashe murya ta ce. Excuse me. Bata jira umarni ba ta turo kofar kawai ta shiga, tana ta faman yauki kamar hawainiya.

Tana sanya kanta cikin ɗakin ta ja birki a bakin kofar ta tsaya, lokaci guda cup ɗin hannunta ya suɓuce ya faɗi kasa ya tarwatse, gabaɗaya cappuccinon ya malale a ƙasa. A miliyan ta zaro idanunta gabaɗaya waje, tamkar zasu faɗo ƙasa, cikin wani irin karuwin murya ta ce. "Wow, handsome, gorgeous and sexy guy with sexy body". Babbar magana!!!.

Ba komai yasata yin wannan zabura da sambatun ba face Smart, kyakkyawa kuma kakkarfar surar jikinsa ya ruɗar da ita, ya fito daga wanka kenan yana sanye da bathrobe na Jaish a jikinsa, so bathrobe ɗin ta yi mashi gajere dan ya fi Jaish tsawo, bata gama rufe mashi cinyoyinsa ba, kun san mutumin da balai'n kyau, ga arab hairnsa a jike yana ɗigan ruwa, sajensa ta kara kwanciya luf, fuskarsa ta kara haske sosai, hakan yasa ya tashi kanta matuƙa.

Anya a jikokin Akka a mata ba Sarina bace ta yi gadon abar kuwa? Jarabar yarinyar nan dayawa yake.

Yana tsaye a gaban mirror yana shiryawa, Auta tana kwance a saman bed É—insa ta yi barci, shi kuma guyson ya tafi wajen momma tun É—azun.

A hankali ya ɗago idanunsa ta cikin mirror ya yi mata kallo guda ya kawar da kallonsa, cigaba da abin da yake yi ya yi tamkar bai san da halittarta a wajen ba. Ganin hakan yasa zuciyarta ta saƙa mata ai ta matsa kusa da shi ya samu damar shakar kamshin perfume ɗin nata kafin ta cigaba da santin kyan jikinsa, har tinani take yi a ranta gata kwance a saman lion chest ɗinsa tana wasa da ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa saboda jarababbiya ce ta karshe yarinyar nan.

Ta manta ma da batun ta ɓarnatar mashi da cappuccino, ta ɓata mashi ɗaki dan jaraba amma dik bata bi ta kai ba, cikin yanga ta fara taku tana jin faduwar gaba, amma haka ta daure ta isa gabansa.

A kusa da shi ta tsaya na Æ´an sakanni, sai da zuciyarta ta tabbatar mata da ya shaki kamshin perfume É—in, sannan ta kara matsawa kusa da shi, Sarina bata tsoro kuma bata da hankali my people's, ko da yake Mammienta ce ta ce mata in dai ya shaki kamshin shikenan ta yi mashi dik abin da take so bashi da bakin yin magana sai abin da ta ce kawai.

Dan haka tana ganin alamar ya shaka ta matsa dab da shi, yana ƙoƙarin zuba lotion a hannunsa dan ya shafa a jikinsa kawai sai ganin hannunta ya yi ta rike robar man, a tinaninta zai ɗago ya kalleta ne dan ta rike robar, sai taga akasin haka, bata san shi daban yake da kowa ba, ba komai yake ɓata idanunsa dan kalla ba.

"Yah Omerish ni yakamata in zuba maka man ka shafa ai, idan kana so ma ni zan iya shafa maka ai, tin da kai nawa ne". Cikin salon kirsa da kisisina ta yi maganar tana wani make murya kamar akuya mai jego.

Shiru bai yi kamar yasan da wata halitta a wajen ba, a ransa yana tinanin wai a cikin kannensa ne a ka samu fitsararriya mara kunya har haka? To me aikin Jaish kenan da bai gyarawa shegiya zama ba? Dama su Jaish haka kenan suka saki gidan kowa yana yin abin da ya ga dama basa cin kaniyarsu su gyara masu zama? Lallai da sake, dole ya sako tarbiya kuwa, dan ba zai É—auki wannan iskanci ba, me banbancin kannen nasa da Heleena da ya É—aurawa karar tsana kenan? Ai basu da wani banbanci, ya gyarawa Heleena da ba abin da suka haÉ—asu ma zama bare kannensa?

Kunsan da farko ita ma Heleena ta so ta kawo mashi iskanci ta rinƙa taɓa jikinsa, watarana kawai ya ware rana ɗaya ya ci uban hegiya daga lokacin ta haɗa malaman jikinta ta natsu, shiyasa kuka ga tana tsoronsa kamar ta mutu, bugu ta ci a hannunsa.

Yana tsaka da tinani unexpect ya ji saukar hannunta a saman hannunsa da yake rike da robar tana faÉ—in. "Yah Omerish bari ma kawai in murza maka man da kai'na". Tashin hankali, lallai Sarina ta wuce yadda ake tinani.

Sake mata robar ya yi ya zame hannunsa, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a tinaninta aikin Mammienta ya ci, ta samu kan Smart, sai ta wani ji bargo mai sanyi ya lulluɓe zuciyarta. Kawo robar man kusa da ita ta yi, tana ƙoƙarin zuba man a hannunta da nufin ta murza mashi a jikinsa tana wani fari da ido unexpect ta ji lokaci guda ta dai'na gane komai, sai ta ji kamar bata duniya, irin mutum ya ji komai ya tsaya mashi cak, shi kansa robar man dake hannunta sai ganinsa ta yi a can tsakiyar ɗakin, wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta ta tafi ta zube ƙasa.

Ba komai ya ja mata hakan na face wani irin mari da Smart ya É—auketa da shi, tass kake ji, kunnuwanta gabaÉ—aya sun dai'na jin sautin komai.

Bai bari ta dawo cikin hayyacinta ba yasa kafa ya yi ball da ita sai da ta tafi ta bugu da jikin bango. Daga nan ta ƙarisa dai'na gane komai gabaɗaya. Taku biyu ya yi ya isa in da take, hannunta da ta sanya a saman nasa lokaci da ta karɓi robar man ya take da kafarsa, ga shi in da ya taka ɗin ta wajen kashi ne, hakan yasa ta ji wani irin azaba ya ziyarceta.

Da karfi ta kurma wani irin ihu mai sautin gaske, É—auke kafarsa daga kan hannunta ya yi ya take bakinta da take yi mashi ihu da kafar tasa, take bakin nata ya fashe sai jini. Belt ya É—auko daga dressing room na É—akin, yadda kuka san wanda yake jibgar katan gardin namiji haka ya fara saukar mata belt É—in nan a jiki.

Ihu ta fara kurmawa mai sautin gaske, ko a jikinsa tamkar wanda aka saukarwa da wahayin duka haka ya yi mata lilis har sai da ya ji zuciyarsa ta É—an samu natsuwa, sannan ya dakata da dukan nata, dik ya fashe mata jiki, ga shi ba kayan mutunci bane a jikinta bare su É—an saukaka mata zafin belt É—in, ga belt É—in da kauri, ta zanu ba karya.

Ga shi Jaish baya part ɗin bare su ji ihunta su kawo mata agaji, yana can hospital shi da Mahnoor, shiyasa Sarina ta daku babu wanda ya kawo kata agaji. Ihunta ya tashi Auta daga barcin da ya ɗauketa. A tsorace ta miƙe zaune a saman bed ɗin. Ganin zane Sarina yake yi yasa Auta ta fara ruwan hawaye.

Yau Sarina sai da ta kira ainahin sunan Mammiensu na yanka saboda jibgar da ta sha. Bakin bed Smart ya koma ya zauna, cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa a kan ta tashi ta zo gabansa. Ai tuni tsawansa yasa ta dawo cikin hayyacinta, dan muryarsa a kaifafe take. Wai a haka ma Smart fa bai ɗauki zafi ba, ransa bai ɓaci ba, da ransa ya ɓaci ai sai dai wata ba Sarina ba, ace a cikin kannensa a samu mai irin halinsu Heleena kuma yana raye? Tab wlh dik sai ya gyara masu zama kafin ya bar kingdom of power.

Sam ta kasa iya miƙewa da kafafunta, da jan jiki a kasa ta iso gabansa, sai kerma jikinta yake yi, bakinta ya kumbura suntum saboda take ta da ya yi, gabaɗaya singalalin hannunta sun yi ruɗu ruɗu da belt ɗin, abin ku da farar fata, tini jikinta ya zama jajir kamar jan gauda.

A gabansa ta ƙariso tana kuka ƙasa kasa. Ko kallon in da take bai yi ba ya umarceta da ta yi mashi kneel down ta ɗaga hannunta sama, daga nan har wayen gari ba zata bar wajen ba, in kuma ta yi koda motsi ne sai ya kakkaryata, daga karshe ta rufe mashi baki tsit baya san ya ji komai ƙanƙantar sauti ya fita daga gareta.

Yau dai Sarina ta faɗa koma. Wayarsa ya ɗauko domin ya kira Jaish ya zo ya faɗa mashi wanenen uban Sarina a cikin familynsu? Dan a cewarsa uban nata ma yana da buƙatar a gyara mashi tarbiyarsa, dan bashi da tarbiya shi ma, saboda idan yana da tarbiya a cewarsa da zai bawa Sarina tarbiya yadda yakamata, dan haka daga ita har ubanta yau zai gyara masu zama, irinsu ne ke ɓatawa larabawa suna...... Tashin hankali, lallai Smart ya dame su King ya iskancin, kam bala'i uncle Abbas zai bawa tarbiya lallai akwai cakwakiya.

A lokacin da ya kira Jaish wayar tana cikin mota shi kuma yana cikin hospital ya je kiran nurses, so bai yi picking ba. Jefar da wayar a gefensa ya yi tare da miƙewa ya shiga dressing room domin ya shirya ya zo ya kwanta, sai lokacin da Jaish ya kirasa zai iya sanin hukuncin da zai yi wa Sarina, dan yanzu wannan duka da kneel down ɗin dik ba hununci bane, ta dai yi ne zuwa yasan ubanta sai ya san kalar hukuncin da ya dace da su.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Da kyar Jaish ya iya driving suka isa hospital É—in, ko da ya kashe motar sai da ya É—auko good 5 mins a zaune shiru ita kuma tana kwance a jikinsa, sannan ya buÉ—e kofar motar a hankali, kafafunsa ya fara zurowa wajen da ita a jikinsa ya fito, da hannunsa É—aya ya tura kofar motar ya nufi hospital É—in.

Har zai shiga sai ya lura da yanayin kayan jikinta, to kun san su da kishi ko da ba matansu ba bare matansu, hakan yasa ya fasa shiga ya juyo da ita, cikin motar ya mayar da ita tare da fita ya nufi cikin hospital É—in shi kaÉ—ai yana wani lumshe idanu yana kame jikinsa wajen guda, da kyar ma yake tafiyar.

A dai'dai wannan lokacin ne call É—in Smart ya shigo wayarsa, Mahnoor tana ganin call É—in har ya katse, shi kuwa nurses mata guda biyu ya je ya taho da su a kan su zo su dubata a ciki.
Chapter 136 · 0% Book details