← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 242

Sashe 114

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce kunga laifin Ammo? Gara ta sanar da jikarta gaskiya dan su rike baby da kyau, irin wannan hidima da ya yi masu ai basa yi sake ya zulle masu ba, kai suna da gaskiya, jeki baby ki saka mana baby a kwana ya kwana yana kiran sunanki a cikin barcinsa ato, ni Princess Teema tare da my people's muna alfahari dake kuma muna bin bayanki ko ya kuka ce?.

"Tsohuwata bari in je zan dawo mu sha hira yau, tayani da addu'a kekam". Ta kai karshen maganar tare da sanya kai da sauri ta fita, a ranta take ayyana ai ba zata taɓa sanar da shi tasan gaskiyar shi mijinta ba ne ba, a haka zasu cigaba da tafiya tana ƙara narka soyayyarta a ransa har sai ya furta mata da bakinsa, yo bata san ta mallakesa bama tana rikita mashi lissafin ƙwaƙwalwa bare yanzu da tasan nata ne shi ɗin! Ai baby sunanka sorry kuwa, dan wannan jika ta Ammo da alama ita ma ba tayar baya bace.

Yana zaune a cikin motarsa ya kifa kai da steering motarsa yana jin wani irin raÉ—aÉ—i a ransa, sha'awar matar tasa tana neman kashe shi. Sam bai ga lokacin da ta nufo shi ba, sai ji ya yi ta buÉ—e kofar side É—in da yake, yana É—ago kai dan yaga wanene ta yi saurin faÉ—awa jikinsa tana turo baki.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya iya ce mata. "Baki yi fushi dani ba baby?". Ƙasa ta ɗan yi da kai. "A'a na yi, amma Ammo ta tikasta mun da in zo in baka hakuri, kuma ta ce komai kace kada na yi maka gardama saboda ba zaka taɓa cutar da ni ba, kai ba mugu bane". ....... Ka ji baby da dabara, wai Ammo ta tilasta mata, ohohoho baby sunanka sorry, dan na lura babyn nan naka dabara gareta.

"To amma ke kin yarda da hakan? Kin yarda da zancenta?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e ta yarda, sake sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce.

"I can't control myself whenever I'm in front of you, but I'm sorry. In Sha Allah, I'll learn to control myself. I know I shouldn't have done that to you, and I will change, okay, my baby? Please don't be mad at your baby."

"I will never be mad at you my baby. Please forgive me too, okay?"

Rungumeta a jikinsa ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali mai É—auke da sirrika da dama.

Hannunta ita kuma ta zura a.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Hannunta ita kuma ta zura a bayansa tana kwantar da kanta a saman kirjinsa da kyau.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara zubawa Allah godiya a cikin ransa, lokaci guda ya É—an ji yanayin da yake ciki ta É—an ragu, a kunne ya raÉ—a mata zata raka shi wani wajen?.

Da sauri ta ɗago kanta, dama sarkin yawo ce ita ɗin, dan haka sai ta amsa da e zata raka shi. Ƙasa ya sake yi da murya kafin ya ce to gyara zamanki mu tafi. Da sauri ta gyara ya kunna motar haɗe da janyo kofar ya rufe, da gudu suka danna izuwa bakin gate. Gateman ya buɗe masu kofar suka nufi waje.

Ina kuma zai kaita?. Za dai mu dawo mu bisu mu gani, dan sai munga komai.....👀🥱

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

A hankali ya juya ta ɗayar side ɗin ya zura kafafunsa kasa, kamar zai miƙe sai kuma ya fasa, kome ya tina sai ya juyo da kallansa a kanta, ɗaure fuska tamau ya yi kafin ya ce. "Momma bata faɗa maki ɗakinki daban da nawa bane?".

Kun dai san yaran momma baya san raini, shiyasa kuka ga baya shiga harkar kowa, shiyasa yaki yin aure dan ma kada mace ta rai'na shi, a gaskiya Jaish ya rai'na mata dayawa, Allah zamu yi maganinka.

Kai ta girgiza mashi tare da cewa. "Momma bata faɗa mun ba".............. Da hannu ya nuna kofar fita kafin ya ce. "Fita mun daga ɗaki, akwai ɗakuna dayawa a cikin part ɗin nan, ki ɗauki wanda ya yi maki, kada ki bari mu sake haɗuwa dake, dan bana san sake ganin face ɗinki". Ya kai karshen maganar tare da yunkurawa zai miƙe ya bar ɗakin.

Cike da tsoro ta ce. "Ni momma ta ce mun a É—akin da kake zan kwa............" Yanke maganarta ta yi saboda wani irin matsiyacin kallo da ya dallah mata, nan take ta ji tamkar an sanya kaca an É—aure mata baki, da kyar ta haÉ—iyi yawu mai wuyar wucewa.

"Bana magana biyu, idan na yi na farko na yi kenan, na biyu zai iya zame maki abin da ba zaki taɓa iya mancewa da shi ba". Cikin natsuwa ya yi maganar yana ƙara kaifafa voice ɗinsa, yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi balconynsa yana jin wani ɓacin rai, shi kansa bai san ainahin abin da ya ɓata mashi rai ba, ya dai danganta ɓacin ran da ce mashi da ta yi a nan ɗakin zata kwana, amma da ni da ku mun san ainahin ɓacin ran daga ina ta samo asali.

Wato abar tasu ta gado ce ta motsa, shi kuma baya san raini, shi ne silar ɓacin fa, amma sam bai gane hakan ba, sai wani haɗe rai yake yi............ Mahnoor da bata saba da irin halinsa na yanzu ba, idan ya yi abu ɗaya sai ta ji zuciyarta ta karaya, yanzu ma haka ne, dik sai ta ji anya ba zata hakura da shi ba kuwa? Ta jefawa kanta tambayar.

Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta lallaɓa ta miƙe, jikinta babu kwari ta nufi waje idanunta suna cikowa da kwallah. A parlour ta tsaya tana tinanin anya zata sake yarda su haɗu kuwa? Dan ya ce kada ta sake bari ya kalli face ɗinta, anya ba zata shiga ɓuya kamar yadda ya buƙata ba kuwa?.

Ta É—an jima tsaye a parlourn tana tunane tunane har sai da ta kalli babu wata mafita sannan ne ta wuce ta nufi bedroom dake kusa da nasa. Ta yi mamakin ganin akwai komai a cikin É—akin kusan kamar irin na bedroom É—insa. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bakin bed É—in ta zauna.

A ranta ta kuduri niyar ba zata sanar da momma abin da yake faruwa ba, zata yi shiru har ta ga me zai iya faruwa gaba, tana da hankali ta fahimci ba komai zata rinƙa faɗawa momma ba, yakamata tasan abin da yakamata ta rinƙa faɗa mata da wanda bai dace ba.

Shiru ta kwanta a saman bed ɗin cike da tunane tunane a ranta. Shi kuwa sai da ya gama zaman da zai yi a balconynsa har zuwa karfe 8:40, sannan ya miƙe ya dawo cikin bedroom ɗin, shikaɗai ba wanda ya taɓa shi yake ta faman ɗaure fuska kamar wanda aka cewa wutar jahannama zai zama makomansa, yana ta faman jan tsaki, sai wani haɗe gera yake yi, a fili ya furta momma tana san lalata mashi komai ta ja mashi raini dama ga Jawad ya gama zubar mashi da mutunci ya auri Chuchu, wannan abin ta kona mashi rai sosai.

Mu fa mun san silar dik wannan É—aure fuska da kake yi yaron Mommarsa, in zaka cire girman kai ka ajiye batun zata rai'naka ka daure ka rungumi Æ´ar matarka ka kawar da kai ma da ya fi maka, ko ya kuka ce my people's? Mu zaka ce baka san raini? Uhm na dai yi shiru.

Saman bed ɗinsa ya haye, har ya kwanta sai kuma ya tina da batun Auta, da sauri ya miƙe zaune, a hanzarce ya ɗauko wayarsa, call ya danna na wata number da aka yi saving da pure heart. Kara wayar a kunnuwarsa ya yi yana sauraron yadda suke zayyana mashi cewa number a rufe take. Yau kwanaki uku kenan yana kiran number a kashe, haka kawai a ransa ya ji tabbas akwai abin da ake ɓoye mashi dangane da Auta, dan kuwa ko Dubai ta tafi suna waya a kullum, ya za'ayi ya kira su Yah Ramish ma su ce mashi bata zo gidan Abu Abdussalam ba, ya kira kakansu King Badeen ya ce mashi bata nan, ya kira uncle Rahab kuma sai ya rinƙa ce mashi ko ta yi barci ko bata kusa, to gaskiya shi yanzu ya fara tantama a kan wannan lamari.

Yunkurawa ya yi zai miƙe ya nufi waje, dan ya je ya samu momma ta faɗa mashi gaskiya ina Auta take? Shi yanzu dik bai yarda da maganganunsu ba. Yan yunkurawa sallamarta ta daki dodan kunnnesa.

Ta wutsiyar idanu ya kallenta. Tin daga kan kyawawan fararen kafafunta da ya kalla ya gane wacece, dan lallenta. Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana jan siriri tsaki, a ransa yake faɗin ba dan wannan yarinyar marainiya bace babu abin da zai hana shi sakinta a daren nan, amma yanzu ma bai sanya a ransa zai zauna da ita ba, yana dai ƙoƙarin tina mafita, saboda shi dai wlh ba zai zauna da wannan yarinya ba.

A gabansa ta zo ta tsugunna, tana sanye da hijabi black color zuwa gwiwowinta, ya dai rufe kayan barcin jikinta, hannunta É—auke da cup of cappuccinon. Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma ga cappuccinonka nan".

Tsawa ya daka mata mai firgitarwa a kan ba ya ce kada ta sake bari su haɗu ba? Tsawar da ya yi mata ne har yasa ta saki cup ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse, hakan yasa ransa ta kara ɓaci har ya ɗaga hannu zai dallah mata mari, sai ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ɓuye shi a tsakanin cinyoyinta.
Chapter 114 · 0% Book details