← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 242

Sashe 1

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bismillarrahmanin Rahim.......✍️🔥🕊️

BLACK WORLD🔥😥

Dik da tsananin tsoron da take a cikin ranta hakan bai hanata É—ago kai ta fara kallonsa tun daga kan Lion chest É—insa har izuwa kan his beautiful full neck attention grabber ba.

Da kyar take iya motsa idanun nata amma ta dage sai ta kalli face É—insa kusa da kusa domin ta tabbatar da mutun ne ko ba mutun ba, because she had never seen a beauty like him.

Ta É—auki a kallah 1 mins tana kallon zanen tattoo na Black Tiger dake saman lion chest É—insa, zanen ya fita sosai, ga bakar damusar ta wage baki, waÉ—an nan garma garman hakwaran nata masu tada hankalin É—an adam sun zanu da kyau, sai da ta ji mummunar faÉ—uwar gaba na ganin hakwaran damusar.

A lokacin da ta sauke kallonta a kan heart-s romance pink lips ɗinsa sai da ta dakata cak tare da kura masu idanu tana yi masu kallon ƙurillah, ko makiyi ya gansu yasan sun kawatu sun kuma haɗu sun kai a mutu a kansu, sai wani irin shining suke yi kamar ya saka lips balm, kai kyansu ya wuci tunaninku. Ba shakka Allah ya yi halitta a nan sai dai muce Masha Allah, .

Tsabar karfin hali irin nata da kyar ta iya hakura da kallon laɓɓan nasa amma sai da ta yi gaba da idanunta izuwa saman romance nose ɗinsa da yake dogo bai zut ba, ɗan dai'dai haka gwanin birgewa, haƙiƙa skin ɗinsa ya kai a shagala da kallonsa, wannan ya babbata da gaske bai taɓa fita rana ba, ya tabbata dai tun yana karami ɓoyesa ɗin ake yi, ni sai yanzu ma na gane dalilin ɓoyesa da babansa yake yi, ashe kyansa ne ya yi yawa da zai iya ja surutun jama'a a kansa da kuma hankulan mutane, in ya fito zai hana dikkan matan da zasu ɗaura idanu a kansa yin wani aiki ya hana zuƙatansu nutsuwa, shiyasa babansa ya ɓoyesa na tsawon shekaru, amma fa a nawa tunanin ni princess Teema ato bamu san dalilin baban nasa ba, abin da muka sani dai komai da dalilin yinsa, da alama nasu dalilin ma mai karfin gaske ne.

Bin wasu kyawawan black curly sajen dake gefen kumatunsa da kallo ta yi. Ya ilahi sai ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafa ko tsoro babu, suna kwance luf a saman skin É—in nasa mai kama da madubi saboda kyalli. Ya ji hutu malam.

Dik kare mashi kallon ƙurillah da take yi yana tsaye yana cigaba da abin da yake yi tamkar bai san da wata halitta a wajen ba, kamar ba shi ne ya jawota gabansa with his magic ba.

Cak ya tsaya daga creating wannan haske da yake ƙoƙarin yi a lokacin da ya ga sauƙar idanunta a cikin kwayar nasa. Bai taɓa tunanin tana da zarrar iya sanya kwayar idanunta a cikin nasa ba, dan a cewarsa zaratan maza masu rai da lafiya ma ba zasu iya ganin face ɗinsa ba bare kwayar idanunsa, sai ga shi ita kuma ta mace ma da kallon idanun nasa, kyansu sun ruɗeta da har ta manta in da take ta kafesu da kallo babu ko kyaftawa.

Haƙiƙa hakan ya girgiza shi kaɗan, dole ya dakata da abin da yake yi domin ya dawo da kallonsa a kanta ya ga zata iya su kalli juna ido cikin ido ne? Idan har ta iya ganinsa ido cikin ido bata kawar da kallonta ba to ya zama dole ya kasheta, domin ta cika ƴar baiwa. Babansa ya bashi labarin tabbas dik wadda zata iya kallonsa ido cikin ido in ma mace ko namiji to ya sani tana da baiwar irin nasa, idan ma ya yi wasa zata iya bugesa, kuma kada ya yarda ya zauna inuwa guda da wanda zai ga cikin kwayar idanunsa babu tsoro, idan ya yi hakan tabbas ayyukansa ne zaku koma baya........ Tashin sense.

Ita kuwa ya subhanallah, sexy romance eyes ɗin nasa ta kafe da kallo ko tsoro hakan bata ji ba, ita dai taga abu mai kyau ya tafi da imaninta, idan ka kalli idanun nasa a fisge sai ka yi zaton design of fish ne saboda girmansu, amma ba haka bane, romance-s-eyes ne, ga shi shikuma ba ɗan soyayya bane, amma wlh yanayin idanunsa irin na riƙaƙƙun ƴan love ɗin nan, ga shi baya buɗesu dikka, suna ɗan lumshe. Kaifafa dasu tamkar eagle eyes.

Idan ya kalleka da su kaifinsu da gwarjinin dake cikinsu sai ya razanaka yasa ka ji faÉ—uwar gaba.

A hankali ya juyosu a kanta, suka ga juna ido cikin ido kuma kusa da kusa. Wlh yarinyar nan ko gezau bata motsa ba, kai ko kyafta idanun nata ma bata yi ba, sai ma É—an kara warosu waje da ta yi na mamakin kallon cikin nata da ya yi.

Ya ɗan ji a jikinsa, ya kuma fara yarda da cewa tana da baiwa irin nasa, domin kuwa ita ma idanunta kaifafa ne sosai, idan baku manta ba Kamran baya iya ganin cikin kwayar idanunsu, shin kun tuna hakan? To ba Kamran kawai ba, dik wanda zai ga Sweetie ko Pretty idan ba mai dakakkiyar zuciya ba babu wanda zai iya jure ganin kwayar nasu gaskiya....... DA ALAMA SUNA DA WATA ƁOYAYYAR BAIWA DA GASKE NE, TO WACE IRIYAR BAIWA KENAN? MU JE ZUWA.

Tsabar ta shahara ma har da fara ƙoƙarin motsa hannunta domin ta taɓa face ɗinsa ta kara tabbatarwa mutum ne ko aljani. Sai dai kash bayan idanun nata babu wani abin da yake iya motsawa a jikinta, ya daskarar mata da komai, da zata taɓa shi ta ji karshen rashin tsoro kenan.

Kai gaskiya Sweetie akwai karfin hali, innalilahi ni narasa ma a wani point zan ajiyeta, tab kai abin da mamaki gaskiya.

Sakin wannan madubin hannun nasa ya yi ta yi kasa kamar zata faɗi, sai kuma ta tsaya a saman iska bata kai kasa ba, amfani ya yi da scepter ɗinsa ya yi magic kafin kyaftawa da Bismillah ta ɓace daga gabansa ta manne da wall na ɗakin ta ɓangaren hagu.

Dik da haka bata tsorata ba, hasalima bata kawar da kallonta daga kansa ba, shi kuwa tuni ya zare idanunsa zaga cikin nata.

Da kyar ta kai kallonta a kan swan sofa chair dake shirye ta wajen wall glass dressing room dake cikin ɗakin, waɗan nan swan design chiar ɗin sun haɗu matuƙa ga shi sun ji dollof mai laushi da tsantsar kyau da tsada.

Komai na cikin bedroom ɗin nan white, gold and milk color ne, sai kuma jikin furniture da aka tsantsarawa kwalliya da zallar madarar gold. My people's Allah ya yi arziki ta yi mubaya'a a wannan empire ɗin, headboard na gadan Black Tiger duniya ce guda, wall headboard ce, wato kayin gadon manne take da jikin bango, a haka aka yita wanda tsawonta ya kai har tana taɓa saman ɗakin, sannan aka bi gefe gefenta da wasu kwayayen fitillu masu bada sky blue ligh mai matuƙar ɗaukar hankali, yanayin yadda aka tsara wall headboard ɗin nan sai mutun ya kwana ya wuni yana kallo ba tare da ya sani ba, saboda haɗuwarsu.

Dik wata flowers da kwalliya dake jikin wannan wall headboard É—in da É—anyar gold aka yi ta wanda nasan kun san da hakan, design of butterfly ce head na bed É—in, dai'dai tsakiyar butterfly É—in gold ce haÉ—e da wani kwai mai bada haske white light, sai ya haskaka gold É—in tana wani irin kyalli mai jan hankalin wanda ko baka yi niyar kallon gadon ba baza san lokacin da idanunka zasu kai wajen ba saboda wannan kyalli na gold É—in.

Ita kanta Sweetie bata san lokacin da ta kai kallonta saman bed ɗin tana jinjinawa girman gadon da kuma haɗuwarsa, kamar ba'a duniya ba, kamar kuma ba za'a mutu ba, shifiɗun alfarma dake saman bed ɗin kawai ya isa sanya mutun ya ji ya ƙoshi da komai saboda haɗuwarsu.

Shi kuwa sarkin azzalumai wato King Black Tiger, baiwar Allah tana can yana kalle kalle shi kuma yana sihirinsa dan ya kasheta.

Tsakar É—akin nasa ya nuna da scepter É—insa, hakan yasa nan take wajen ta zurma tamkar rami mai zurfin gaske, magic eyes É—insa ya juya nan take wasu irin kifiyoyi masu kaifi da tsinin gaske suka bayyana cike a cikin ramin har baki, kasan kifiyoyin wuta ce take ci mai tsananin azabtar da har in da suke suna jin hucinta

Wasu irin bakaken kunamu masu duhun jiki sosai manya manya da su ne suka sake bayyana a saman kan tsinin kifiyoyin nan, sai wasu snake da suka bayyana a jikin kifiyoyin sun fasa kai da baki, kiris suke jira su fara kai sara.

Har lokacin idanunta a kansa, da alama bata firgita ba.

Da scepter É—insa ya yi amfani ya janyota izuwa gaban wannan rami ta hanyar amfani da magic É—in nasa. Sai a lokacin ta kawar da kallonta izuwa kan ramin dake gabanta.

Wani irin tsorata ta yi na ganin zabga zabagn kunamun dake yawo a cikin ramin, abin mamaki kuma wutar dake ci kasan ramin baya taɓa dabbobin, babban abin da ya ɗaga hankalinta ma shi ne waɗan nan macizai da suka fasa kai suke jiran kiris su kai sara, wannan wani irin zalinci ne? Da me bawa zai ji idan aka jefashi cikin wannan rami? Shin da wutar dake ci a kasa zai ji ko dai da waɗan nan shegun baƙaƙen kunamu da bakaken kumurcin macizan? Ko da kifiyoyin dake tsaitsaye masu kaifin bala'in, hakika kuma ta wannan hanya Black Tiger ya fi yawan kashe dik wanda ya taɓa ganin face ɗinsa, cikin wannan rami yake jefa mutun hakan yasa ko gawar mutun ba'a sake gani, shiyasa tin farko nace maku dik wanda ya shiga cikin wannan part ɗin nasa ba'a sake jin ɗuriyarsa, ya tafi kenan, to ga hanya ta farko da azzalumi Black Tiger yake bi domin ɓatar da su.

Mahaukacin razana ta yi, nan take zuciyarta ya fara duka tara tara! Idanu ta zaro tana kallon cikin ramin tamkar kwayar idanun zasu faɗo ƙasa, jikinta dik a daskare ba damar ta yi motsi ma bare har ta ce zata gudu, yadda zuciyar tata take bugawa tamkar ta fasa kirjinta ta fito waje.
Chapter 1 · 0% Book details