← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 242

Sashe 176

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wife kin kusa tabbata da gaske a matsayin wife É—in nawa". Ya faÉ—a cike da murnan hakan. Ita kuwa zaro idanu waje ta yi a hanzarce ta ce. "Yah Abdussalam me kake nufi?"....... Ya É—an yi mamakin jin tambayar tata, sai dai kuma ya yi tinanin ko bata san shirin da ake yi bane, dan haka sai ya ce. "Daddy bai sanar dake cewa ya bani ke bane? Kinga ya tabbata da gaske zaki zama wife na, abin da na jima ina mafarki kenan, burina ya kusa cika!". Cike da fara'a sosai a saman face É—insa ya yi maganar, yana kwance a saman bed É—in kakansa the most powerful King, wato mahaifinsu momma King Badeen kenan, ya tada kai da laps na kakan nasa ne yake wannan surutu, sai shafa arab hairnsa King Badeen yake yi yana siririn murmushi irin nasu na manya, da alama shi ma ya ji daÉ—in wannan haÉ—i da za'ayi, dan sai albarka yake ta zubawa abin.,........ Tab magana ya je wajen manya, akwai matsala kuwa, dan ni dai na duba banga hanyar ruguje wannan magana ba, dan King ba zai iya kallan idan sirirkinsa King Badeen ya ce ya fasa bawa Abdussalam na gida Zunaira ya É—auka ya baiwa bare ba, akwai case kuwa, shin Smart zai yi nasara kuwa? Shirin su momma zai yi aiki kuwa? King zai yi azumin kaffarar nan kuwa? Rantsuwa dai ya riga da ya yi, uhm Allah sarki assistant commander Hoorain sorry, alkalamina bai yi maka adalci ba ko? Ba laifina bane, laifin King ne!!.

Idanunta ne suma ciko da zafafan kwallah sosai, cikin natsuwa ta ce. "Daddy bai faɗa mun ba Yah Abdussalam". Da kyar ta iya ƙarisa kai karshen maganar....... "Ayya ina ga wani abin ne ya sha gabansa, amma da zai faɗa maki, kila shirye shiryen da suke yi ne ya ɗauke hankalinsa......".

A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "Shirye shiryen me suke yi kuma?". Ta yi tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kunnuwanta ba zasu iya É—aukar cewa shirye shiryen bikinsu ake yi ba, sai dai kuwa kash, abin da take gudunwa bata tsira ba, dan kuwa da buÉ—an bakin Abdussalam cike da murna ya amsa mata da. "Shirye shiryen bikin mu mana, baki san nan da 3 days za'a É—aura auren ba ko? Wlh na matsu wannan rana ta zo in mallakeki, sai naga lokaci ma ya dai'na gudu, baya sauri a yanzu..........". Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon wani irin ihu da ta zunduma tana faÉ—in. "No dad no, please don't do that to me!!".

Da farko ta yi zatan zata iya jurewa har su kammala waya da Abdussalam ba tare da ta nuna mashi bata san shi ba tun da Smart ya ce mata ta kwantar da hankalinta in dai yana raye sai ta auri zaɓin ranta, to amma da ta ji saura 3 days aurensu sai ta karaya, tuni ta firgice ta fita hayyacinta, ta haukace. Wurgi da wayar ta yi ta diro kasan bed ɗin, sai hello Abdussalam yake faɗi, amma ina bai san ta wurgar da wayar ta yanka waje da gudu tana kuka ba.

Bata zame ko'ina ba sai bedroom na Smart, a lokacin yana aikinsa ita kuma Pretty tana cin abinci. Babu ko sallama a haukace ta afka masu cikin É—akin. Da gudu ta tafi ta faÉ—a saman jikinsa a kan bed É—in tana sakin kuka mai sautin gaske. Cike da mamaki yake binta da kallo, dan shi É—in mai natsuwa ne sosai, so komai nasa a natse yake yi, dan haka bai wani tashi hankalinsa ba, ya bita da kallo na Æ´an mintunan da basu gaza biyu ba. Sai da ya ga kukan nata ba mai karau bane, sannan yasa hannu ya É—agota tare da ture laptop É—insa gefe guda. Daidai lokacin ita ma Pretty ta taso da gudu ta nufo su, dan dik wannan shirmen nata tana jin kaunar Auta a ranta.

Ɗagota ya yi tare da raba jikinsu, sai ya zamana suna fuskantar juna, cikin natsuwa ya ce. "Is okey my sweetheart, yi shiru na ji meyake faruwa kin ji ko?". Ina kai ƙasa yin shirun nan ta yi, tamkar ranta zai fita haka take kuka, da kyar voice ɗinta yake iya fita ta faɗa mashi abin da yake faruwa. Lallashinta ya hau yi tare da kara tina mata alkawarin da ya ɗauka mata, ba makawa in dai yana raye Hoorain zata aura ba kowa ba, dan haka ta kwantar da hankalinta, daga karshe ya rufe da cewa zai karɓi wayar hannunta, ba zai sake bari ta yi magana da kowa ba, dan kada su rinƙa kiranta suna faɗa mata wasu maganganu har su ɗaga mata hankali.

So mugun wasa, cikin sauri ta tari numfashinsa da cewa. "Yah Omerish idan ka karɓi wayata da wani waya zan yi magana da Hoorain?"....... Ya fahimci sweetheart ɗin nan nasa ta yi nisa, ita dai Hoorain kawai, dan haka sai ya ce mata akwai wayarsa ai, dik time da take so ta zo ta ɗauki nasa ta kira Hoorain ɗin, amma bayan Hoorain bai yarda ta kira kowa ba........ "Yah Omerish har da Yah Omar kada na kira?". Cike da fargabar kada ya hanata waya da guyson ta yi tambayar. Ai kuwa kai ya jinjina mata, harda Guyson ɗin kenan, abin ya sosa ranta sosai, dan guyson wani ɓangare na bugun numfashinta ne, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin yayan nata idan tana san zaman lafiyarta.

Miƙewa ya yi ya ɗauki wayarsa ya nufi waje, dan ya je ya yi waya da King, a nan ya barota ita da Pretty yana jin zuciyarsa babu daɗi, dan wlh ya tsani abin da zai ɓata ran Zunaira.............. Me kuke tinanin zai cewa King, kuna ganin wannan al'amari zata canza kuwa? Uhm muje zuwa. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nasa tare da tada kai da lap ɗin Pretty tana tinanin me rayuwa zai sake zuwan mata da shi, ita kuma Pretty ta hau shafa arab hairnta!!.

Shin kun san meyasa gabaɗaya litattafaina stars ɗina mata basa taɓa haura 13 to 14 years suke aurensu? Kun san dalilina na yin hakan? Saboda a kullum burina shi ne na yi koyi da manzan Allah (SAW) kuma kuma na kwaɗaita maku yin koyi da shi. Manzan Allah ya ce ku aurar da ƴaƴanku mata tun suna ƙanana, su girma a ɗakin mazajensu, bature masu jajayen kunnuwa kuma ya ce maku aurar da yara ƙanana tauye masu hakkinsu ne, wai a barsu su girma su san ƴancin kansu, uhm Allah mai iko, akwai wanda ya kai manzan Allah sanin hakkin ɗan adam ne? Akwai wani malami da ya isa ya gwada mashi sani ne? Dik duniya da kuke gani da dik wani cigaba da ake samu wlh kwaikwayo ne daga abubuwan da Allah ya halitta turawa da masu kimiya suke yi, zan kuma tabbatar maku da haka, so dik duniya babu wanda ya kai manzan Allah ilimi, dan kuwa masu tinƙaho da ilimin ma wato masu jajayen kunnuwa daga iliminsa da ya koyar suke satar nasu fasahar. Sannan kuma halittun Allah suke kwaikwayo su bunƙasa shi, to shi kuma manzon Allah Allah da kansa ya koyar da shi, kenan karatun waya fi a nan? Dan haka shi ya fi sanin hakki mutum fiye da kowa, amma a haka ya ce ku aurar da yaranku tun suna ƙanana, su kuma masu jajayen kunnuwa sun hure maku kunne sun kwaɗaita maku ku bar yarinya ta yi karatu ta girma ta san ƴancin kai, Uhm aikuwa wanda bai ji bari ba ya ji oh oh, zaku ga sanin ƴancin kai idan ta zo tana gogayyar kafaɗa dake, kina ta bari tana faɗa maki tasan ƴancin kanta tasan me ya dace da ita, sai ma ta tuna ta fiki sanin abin da yakamata, ga shi nan ai kuma muna gani, yarinya ta nuna ta fi uwarta sanin abin da ya dace ta yi. Ba ace kada a bawa mata ilimi ba, dan ilimin mace ilimin al'umma ne, amma ta samu ilimin a ɗakin mijinta, idan anyi aure ma ai ana karatu. Babban illame garemu kin abin da manzan Allah ya faɗa, shiyasa ga shi nan zinace zinace dik ya ishi al'umma, lesbian da sauransu, ƴaƴa sun girma suna son aure kun ce sai sun yi karatu, da zarar yarinya ta fara period dik wasu kofofi na sha'awarta yake buɗewa, a wannan lokaci aure kawai take so, a nan ne idan baki yi hankali ruɗin samari haɗe da kawaye ya jefata ga halaka, ni dai ina mai baku shawara, a kullum ku kasance masu amfani da maganar MANZAN ALLAH, babu ruwanku da abin da duniya zata ce, kun gannin nan zancen duniya bata gabana, a ko'ina faɗar Allah da manzonsa nike ƙoƙarin bi. To ni dai fatana kullun na rinƙa kwaɗaita maku koyi da fiyayyen halitta, dikkan rubutuna ina yinsa besa koyarwar manzon Allah, kuma dik idan kuka natsu kuka duba darusa ne a gareku. Allah ya bamu ikon koyi da fiyayyen halitta. And lastly har ya gama rubuta littafi a rayuwata star ɗita ba zata taɓa haura 15 years ba In Sha Allah, na baku satar amsar yadda zakuna gane Stars mata na littafaina, ba zasu taɓa haura 15 years ba........😅

STORY🔥♥️

🔥🔥KINGDOM OF JUSTICE🔥🔥

Wato RAWANIN ADALCI kenan, shi ne sunan masarautar nan na Queen Zarina, wasu suna kiranta da kingdom of justice, sai dai kuma sunane saɓanin aiki, dan kuwa babu koda kwayar zarra na adalci a cikin wannan masarauta, mulki suke yi mai cike da zalinci wato mulkin kama karya, babu adalci a tafiyarsu, babu tausayawa bare jin ƙai. To meyasa kenan sunan masarautar ta kasance na adalci?. Muje zuwa zaku ji tarihi a nan zaku fahimci daga ina aka samo matsala ta sauyawar abubuwa.

Fadar Sarauniya wato Qeen Zarina, ita ce zuciyar masarautar zaluncin. Babban katafaren gini ne da ya kai girman wata gari gabaÉ—aya.
Chapter 176 · 0% Book details