← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 242

Sashe 148

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ciza laɓɓansa master ya yi, ya so ne dama Ronnie ya zo da nufin su kaure da faɗa ya janye masu hankali har gungun matanen can su yi wa Daular zobe su rufesu da yaki ba tare da sun farga sun shirya ba, amma sai Sweetie ta hana shi, ya ji zafin hakan kuma ya kara tsanar Sweetie sosai.

"Bro kai da kanka ka bawa warriors É—in umarnin da su shiryawa yaki kada ka daka ta wannan kazamin mutumin". Cewar Sweetie, tana bala'in tsoron master Devil idan baku manta ba tun farkon zuwanta birnin, sai dai kuma yanzu wutar tsanansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta saboda lalatar da yake yi, and tana tare da Ronnie, dan haka tana jin kwarin gwiwar zaginsa dan Ronnie ya fisa karfi kuma zai tsaya mata.

"Babu wanda ya isa ya bawa warriors ɗin nan umarni a nan sai ni". Cewar master, dik abin da yake yi fa yana so ne ya ɗauke masu hankali har a cin masu. Ronnie zai yi mashi martani Sweetie ta hana shi, daga karshe ta ja hannunsa suka haye saman dogon stage dake wajen domin su yi magana da warrios ɗin. Jikinta har kerma yake yi ta ɗauko wani katan laspeaker ta miƙa mashi domin ya yi magana. Karɓa ya yi kafin yasa hannu ya buga belt ɗin dake wajen mai sautin gaske domin ya samu attention na warriors ɗin.

Aikuwa yana bugawa gabaÉ—ayansu suka juyo a kansa, kan kace me dik sun haÉ—u a gaban stage É—in, da gudu master ya hauro sama shi ma da nufin ya dakatar dasu, shirinsa shi ne ya capke Ronnie da kokawa ya dakatar da su.

Ronnie ya fahimci hakan, dan haka sai da ya bari ya hauro yasa kafa da karfi ya takesa a kirji da karfi a in da ya yi baya baya ya ganganra kasan stage ɗin, ya faɗi ƙasa a gaban warriors, cike da bada umarni ta cikin laspeaker Ronnie ya ce da mayakansu na Robbot guda biyu da su kama master su jefa mashi shi a cikin prison na empeir ɗin. Tsalle Sweetie ta buga tare da cewa. "Good my bro".

Warriors biyu ne suka capki master suka wuce da shi, ga shi robbot ne bai isa ya gwada masu fin karfi ba, kuma Ronnie shi ne mutum na biyu bayan Black Tiger da aka shigar masu da su rinƙa bin umarninsa a cikin kwakwalwarsu, dan haka tin da ya ce su kai master prison ba makawa sai sun kaisa.

Attention ɗinsa Ronnie ya bayar a kan sauran warriors da sun haura sama da 3k a wajen, cike da bada umarni ya ce su yi maza su shiryawa yaki basu da isasshen lokaci an kawo masu hari. Sannan ya ware wasu warriors da zasu iya kai 300 ya umarcesu da su tattara mata, tsofaffi da yara, su tarasu waje guda, su basu karisa kada su bari wani abin ya samesu. Daga karshe ya wari wasu warriors ɗin ya umarce da idan yakin ya ɗauki zafi fiye da tunaninsu to fa su tashi jiragen eagle dromes na yaki su fara ɓarin wuta daga sama. Yana kai karshen wannan magana bai gama rufe baki ba suka fara jin rugugin tashin wuta daga cikin empeir ɗin.

Cikin É—aga murya Ronnie ya ce ku je, daga haka ya riko hannun Sweetie da gudu suka sauko kasan stage É—in suka nufi cikin empeir É—insu wajen Black Tiger kenan.

Wato idan ka yarda da Allah wlh cikin sauki zai kare ka daga sharrin dik wanda ya nufeka da sharri ba tare da kasan ya yi ba, kun dai ga aya a kan Floris, ta nufi Sweetie and Ronnie bayin Allah da sharri, to da yake su Allah kawai suka rike ga shi ya juyar mata da aniyarta a kanta, my people's me kuke tinanin yasa Black Tiger a cikin wannan hali? Ya kuke tinanin wannan yaki zai kasance babu Black Tiger? To mu dai bari mu je wani part É—in mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥

Zaune Auta take a gaban tabkeken s-p na gidanta da Smart ya mallaka mata, tana sanye da short army trouser mai shegen kyau da ya tsaya mata a iya gwiwa, sai kuma white shirt daga ta sama, ta yi shiru haÉ—e da buga uban tagumi tana tinanin Hoorain.

Manya manyan ƙosassun dolphin fish ɗinta suna ta wasa a cikin ruwan, sai fito da kansu waje suke yi suna taɓata dan ta zo su yi wasa amma taki kulasu, tana cikin damuwa, kun san dolphin idan ka saba wasa da su da sun ganka za su yi gaggawar fitowa saman ruwa, so ita a koda yaushe suka zo France ita da Jaish tana wasa da su sosai, ita ma tasa Smart ya saka mata su ɗan wasa, amma wannan karon sai ga shi taki kulasu, sai tsalle suke yi su fito su koma.

Hoorain kawai take tunani baiwar Allah, ta yi rama sosai, yau kwananta biyu a gidan nan tare da Smart and Pretty, sai dai ko kaɗan bata san a wace duniya take ba, ga shi tin da suka dawo Smart bai natsu ba bare har ya san halin da take ciki, baya zama saboda aikinsa, wani lokaci sai cikin dare yake dawowa,lokacin kuma sun yi barci. Ita kuma Pretty dama ba wani cika damuwa da abubuwa ta yi ba, bama zata fahimci halin da take a ciki ba bare har ta tausaya mata ko ta bata shawara. Ji take tamkar ta sanya hannu bisa kanta ta kurma ihu ko zata samu sauki, wayar da Smart ya bata wanda zata rinƙa kiransa idan tana buƙatar wani abin sai ruri yake yi ta ɗaura shi a saman kujerun dake kawayen da wajen, da alama ta yi nisan da bata ma jiyo ringin na wayar ba.

Guyson ne kuma yake ta kiranta, dan ya gaza samun kwanciyar hankali da sukuni, jiya ita ta kirasa da number da yake ta haddace numbersa, ta ce mashi ya dubi girman Allah ya je ya haÉ—ata da Hoorain a waya, da farko yaki yarda, daga baya da ya fahimci zata iya cutuwa sai ya ce tabbas zai je koda dad zai jefashi cikin prison ne, to shi ne yake ta kiranta yanzu bata É—aga ba hankalinta ya yi nisa.

A can cikin gida kuwa, Pretty ce tsaye a gaban dressing mirror na É—akin Smart, bata san cewa bedroom É—insa bane, ta tashi daga barcinta kawai ta je ta afka cikin É—akin a garin neman hanyarta na san fita waje ta duba Auta, ta san Auta tana yawan zama a wajen dolphins É—in nan, sai dai bata iya fitar da kanta wajen ba, sai dai su je a tare da Autar, saboda hanyar yana da sarkakiya sosai.

Ganin kanta a cikin wani bedroom ɗin yasa ta fara kewaye a ciki tana zuba ƙauyancinta, taga bedroom ɗin ya fi nasu haɗuwa da ƙawatuwa sosai, ta ga abubuwan da bata taɓa gani ba, Allah ya yi zata zo France, dan suna rike da hannun juna ita da Auta a lokacin da Smart ya ja hannun Auta suka baro kingdom of power, sai Auta bata saki hannunta ba ta jata suka tafi a tare. Time da suka je airport Smart ya nuna ba zai tafi da ita ba, sai Auta ta ce ya kyaleta kawarta ce kuma suna san juna, dalilin da yasa ya zo da ita kenan.

Leke leke ta shiga yi mashi kamar ya aikata, kun san ita Pretty kifin rijiya ce, ba kamar Sweetie take ba, wayonta da sauki, ga bala'in tsoro ba confidence, sai shegen shagwaɓa da cin abinci. Amma idan baku manta ba ita ɗin gwana ce wajen iya fitina, bata ganin abu bata taɓa ba. Dan haka sai ta shiga yi mashi taɓe taɓe, dik abin da ta gani sai ta taɓa.

Cikin taɓe taɓen nata ne hannunta ya kai ta buɗe drawer mirror, tsautsayi dai baya wuce ranarsa, Smart yana rufe drawer da password, idan ya buɗe ya ɗauki abin da zai ɗauka, da ya tura drawer zata sake shiga password, so yau da ya tura drawer sai bata turu da kyau ba bare ta shiga password, hakan ya bata damar buɗewa.

Wasu robobi ta gani a ciki kamar na zuba magunguna haka, tsabar fitina da kiran ajali wanda in ya kira dole a amsa sai tasa hannu ta ɗauki roba guda ɗaya, har da ɗan saka karfinta wajen buɗe robar da ta ɗauko. Tana buɗewa wani abu ya fita kamar hayaki haka, shakarsa ta yi a take ta saki robar ya faɗi ƙasa.
Lokacin guda jini ya fara gangaro mata daga hancinta da kuma hakinta, ji ta yi tamkar am shake mata wuya wuya da karfi, hannunta dikka biyu ta kai ta riki wuyar tata tana kwalalo idanu waje. Da kyar ta iya juyawa tana san barin wajen, sai dai ko motsa kafafunta ta ƙasa bare ta iya tafiya.
A take a wajen ta yanke jiki ta faɗa saman kirjinsa, dan yana tsaye a bayanta, da ta juyo ta fita a cikin hayyacinta ne yasa bata iya gane akwai mutun a kusa da ita ba. Shi kuwa dama ya fito daga wanka yana cikin dressing room yana shiryawa zai fita, to ya fito daga dressing room ɗin kenan yaga ta ɓalle marfin robar, shi ne ya kariso wajen ya tsaya a bayanta, ta cikin mirror dake gabansu yake kallan yadda jini ya fara zuba daga hancinta har izuwa bakinta.

Fararen kaya tas ne a jikinsa, da ta faɗa jikin nasa kaf ta ɓata shi da jini. Allah ya cecesa yana sanye da face mask a fuskarsa, dan shirin fita ya yi, da wlh a tare zasu mutu da ita, dan in ya shaki wannan chemical ɗin shi ma ba zai tashi ba, dama sai sun saka face mask, hand's gloves da wasu irin riguna na leda kafin suke buɗe chemical ɗin, kun tuna yadda suke aiki a wajen haɗa makamansa ko? To haka suke yi kafin amfani da waɗan nan shegun chemical, kisa suke yi nan take, ita kuwa da fitina da rashin sani ta je ta buɗe.
Chapter 148 · 0% Book details