Sashe 63
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsa. Shi kuwa sai magiya yake yi mata yana rantse mata da Allah akan bashi bane, sambatu kala kala yake yi mata. Ko Pretty da gigin giyar yarinta yake É—ebanta ta fahimci zallar gaskiya a tattare da shi bare ita Auta da tasan shi fiye da kowa, amma ya zata yi? Ta shiga ruÉ—anin da ba zata iya tsayar da zuciyarta a waje guda ta yanke abin da ya dace da ita ba.
Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, akwai tsananin ciwo zuciya ta zargi masoyin da ta fi kauna sama da komai ya cutar da ita ko ya ci amanarta, wannan zuciya ta kan iya kamuwa da ciwo, kuma da matikar wahala ta iya sake yarda da wani.
Kuka ita ma Pretty ta fara yi tana cigaba da ambatar Auta ta tashi, ta daina yin kuka................ Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda ta rikiɗe da yin tari mai sauti mai kuma karfi har tana kwarewa, cigaba da bata hakuri ya yi yana kara rantse mata da Allah bashi bane.
Bata kulasu ba, ta yi wannan kukan har sai da ya isheta, sannan ta tsagaita dan kanta. Yana ƙanƙame da ita, tin yana sambatu shi ma har ya ƙasa iya cigaba da yin magana ya yi shiru.
Pretty tin tana kuka har ta yi shiru dan dole. Dan sun lura Auta ba zata ji rarrashin nan da suke burin yi mata ba.
Sai da suka ji ta dakata da kanta ne Hoorain ya yi saurin ɗago da kallonsa a kanta, da kyar murya na rawa ya iya ce mata. "Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri, wlh bani bane, kuma ba zan taɓa iya cutar dake ba, please trust me!".
Shiru ta yi kamar ba zata tanka mashi ba, idanunta a datse gam, jikinsa dik sai kerma yake yi, da kyar ta É—aga hannunta izuwa saman hular yakin dake face É—insa dai'dai saitin kumatunsa. A hankali ta waro idanunta a kansa, sun yi jajir kamar wuta saboda ta sha kuka har ta goge Allah.
"Hoorain na san ba zaka yi mun karya ba, saboda baka yi baka saba ba, ina da tabbacin a kai'na kuma ba zaka fara ba, dik abin da yake fitowa daga bakinka zuciyata ta shaida zallar gaskiya ce kawai, na yarda da kai, amma zuciyata tana cikin tashin hankali da ruɗanin wanenen mai kama da kai da ya yi yunƙurin kasheni? Meyasa sai a siffarka za'a zo cutar dani? Dan kawai zuciyata ta shaku da kai? Shin akwai wanda shakuwarmu ta tare mashi wani abin ne ko ta takura mashi?".
Lalllai sai ka saurara da kyau zaka iya gane me Auta take faɗe, saboda yadda voice ɗinta ya dashe na kukan da ta sha. Tabbas ya ji maganganunta dikka shi kam, dan a matse yake da buƙatar san jin ta furta mashi ko da kalma ɗaya ne, dako yake yi dama shiyasa ya kasa kunne ya saurara da kyau.
Hannunsa dake cikin hand gloves ɗinsu na mayaƙa ya ɗaura mata a saman face ɗinta, zafafan hawayenta yake san goge mata amma kuma yana jin shakka shakkar yin hakan ba tare da ta bashi izini ba, dan haka sai ya ce. "Ina neman alfarma da ki bani izinin in share maki hawaye kafin na baki amsar tambayarki!!".
"Meyasa kake san goge mun hawayena?". Ta gefa mashi tambaya.
"Saboda bana san ganinsu a face É—inki, da murmushi mai kwantar da hankula face É—inki ya dace, kuma da shi muka sanki, bamu san wani abin bayan cool murmushi a kan face É—inki". Idanunsa a kan face É—inta yau kam ya yi magana.
"Da gaske Hoorain zuciyarka bata san ganin hawayena?". Cike da mamaki haÉ—e matsuwa da san jin amsar da zai bata ta yi tambayar.
Jinjina kansa ya yi. "Tabbas zubar hawayenki babban tashin hankali ne wanda zai iya zama barazana ga zuciyata, bana san shi, hankalina yana tashi sosai kuma rai'na yana sosuwa matuƙa idan naga kin haɗe rai ma ba sai an kai ga kuka ba".
"Meyasa kake jin hakan a kai'na?". Ta jefa mashi tambayar ne cike da yakinin abin da take san ji daga garesa zai furta mata ko ranta zai yi sanyi, tabbas ta yarda da shi, tasan baya yi mata karya, sai dai har yanzu zuciyarta yana cikin ruɗanin da Allah ne kawai zai iya warware mata, daɗin daɗawa da ace shi ya yi yunƙurin kasheta tin farko da tabbas ba zai taimaketa a cikin wannan dajin ba, tabbas daga haɗuwarsu izuwa yanzu da ya jima da gama ƙarisa hallakata ya jefar da ita, amma ransa ma ya sadaukar ya cecesu, ya kuma yi jinyarta, sannan ya zube gwiwowinsa a kasa yana neman ta tsaya ya mayar da ita gida, kai gaskiya ko iya waɗan nan hujojin sun isa a gaskata cewa bashi bane ya yi niyar kasheta, to yanzu tambayar a nan ita ce wanenen ya yi niyar kasheta? Sannan kada ku manta yana Kingdom of justice, wato wajen Queen Zarina kenan, to ya aka yi hakan? Lokaci ne zai warware mana komai In Sha Allah, muje dai zuwa!!.
"Ban san dalili ba, abin da nasani kawai shi ne bana san tashin hankalinki"..
Allah sarki, jin ba abin da ta yi tsammanin ji daga garesa bane yasa ta sauke wahalallen ajiyar zuciya tare da jawo yawu mai wuyar haÉ—iya ta haÉ—iyesa da kyar, ta yi tinanin zai ce saboda yana santa yasa baya san tashin hankalinta, sai ta ji akasin haka. Jikinta ne ya kara mutuwa sosai, yanzu ta gama yardanwa kanta da gaske baya santa, dama ranar ta ji yana faÉ—awa su Ansar baya santa, ashe ita kaÉ—ai take dakon kaunarsa. Fahimtar hakan yasa wasu zafafan hawaye masu É—umin gaske suka fara wanke mata fuska da gudun gaske.
Bawan Allah, ya so faɗa mata amsar da take san ji, ya so ce mata saboda santa yasa baya san ɓacin ranta, sai dai tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, yana jin kamar ba zai iya furta mata ba, dan yana ganin kamar ba zai sameta ba, kamar ko ya faɗa mata a banza ne, ba za'a bashi ba kuma ita ma ba lallai ta yarda ta aminta da shi ba dik da yana ganin kamar tana san shi kuma abokansa suna yi mashi wannan hasashe na tana san shi ɗin.
Dagewa ta yi da karfinta ta yunkuro zata bar jikinsa. Cikin sauri ya rikota, ƙasa ƙasa a nitse ya ce. "Zaki fama ciwonki idan kika tashi fa".
Tabbas ya fahimci amsar da ya bata ne ta sosa ranta har take san barin jikinsa, amma sai ya yi kamar bai fahimta ba, dik dan ya yi ƙoƙarin tsare kansa daga shiga bala'i.
"Kada ka damu Hoorain, a yanzu na samu kwarin gwiwar son mutuwa fiye da rayuwata, babu wata amfanin zamana a duniya tin da burina ba zai cika ba, ka barni ciwon ya fama kawai na mutu............"
Bata iya ƙarisa maganar ba kuka ya cikarfinta sosai wanda ya tilasta mata yin shirun dole.
Wani irin bargon sanyin jikine ya lulluɓesa, sai ya ji ya yi nadamar faɗa mata hakan da ya yi, yanzu bata da lafiya, kamata ya yi ya faɗa mata kalamai masu sanyi da zasu kwantar mata da hankali, ba ya tsaya biyewa zuciyarsa ba.
"Ranki ya daÉ—e ki yi hakuri, ki sani rayuwanki shi ne namu, kada ki yi mana wasa da shi kin ji?".
Pretty dai kallansu kawai take yi, sun yi nisan zango cikin larabcin da suke yi, dama ita ba sosai ta iya ba, sama sama ne haka, ta fi iya turanci a kan Larabci, Sweetie ta fita iya larabci, dan haka sai ta dai'na fahimtar abin da suke faÉ—e dan sun yi mata nisa, kawai ta hau aikin binsu da kallo.
"Hoorain ina san ka dai'na yaudarar zuciyata haka nan, ka barni dan Allah, wai me na tsare maka ne ma da kake wahalar da ni?". Cikin kuka ta yi maganar.
Sam bai gane maganar da take yi ba, shi ya rasa ya zai yi, dan gaskiya ya san ko mutuwa yake yi ba zai sameta ba, yanzu haka mutuwa yake kwana yana wunin yi a cikin zuciyarsa dik a kanta, to ina ga ya furta mata soyayya sun kuma kara shakuwa da juna? Me kuke tinanin zai faru a lokacin da za'a rabasu?.
"Dik wani abin da bakya so daga yau na dai'na yi, ba zan sake ba kin ji?". A sanyayye ya yi maganar.............. "Ka tabbata dik abin da nikeso zaka yi?". Kai ya gyaÉ—a mata alamar ya tabbata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da zame hannunta daga face É—insa, a hankali ta yunkura zata bar jikinsa.
"Akwai in da kike san zuwa ne in kai ki?". Ya jefa mata tambaya. "A'a zan sauka daga jikinka ne kawai ina ga sai ya fi mun daÉ—in faÉ—in abin da nike san ka yi mun".
Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, sannan ya sauketa ƙasa a hankali cike da kula yana ce mata sannu. Zama ta yi a ƙasa suna fuskantar juna, tana matuƙar jin azabar ciwon da yake jikinta, amma haka ta daure.
"Yaushe zaka mayar da ni gida?."
Tambaya ta farko da ta fara jefa mashi kenan.
"Yanzu haka a kan hanyar gida muke, ƙoƙarin mayar dake nike yi, sai dai muna da nisa sosai, zamu iya yin kwana biyu a dajin nan kafin mu iya fita". Cikin girmamawa ya bata amsar.
"Ka zauna da kyau to sai mu yi magana". Ta faÉ—a a sanyaye.
Matsawa kusa da ita Pretty ta yi suka manne da juna. Kallo É—aya Hoorain ya yi wa Pretty ya kawar da kansa, ya maida kallansa a kan ruwan dake gudu a gefensu, yana satar kallan Zunaira ta witsiyar ido.
"Ranki ya daÉ—e nafi san in tsaya a kanki dan tabbatar da babu wani abin cutarwa da zai tinkaro in da kike". .
Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Kada ka damu, babu wani abin cutarwa da zai cutar da mu In Sha Allah, yanzu dai zauna".
Ba musu ya zauna, amma bai so hakan ba, sai ya lankwashe kafafunsa ya ƙarisa zama daga durkushen da yake.