← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 242

Sashe 20

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddyna Allah ya kara maka tsawon rai da tsawon kwana, nasan yardar da ka bani yasa ka sanyani a sahun gaba wajen yin shawara domin mu tantance abin da yake dai'dai da kuma ba dai'dai ba, yardar da ka mun yasa nake jin kaina a matsayin mace zaƙwaƙura mai yin abin da ya dace, dan yardarka ga mutum ba ƙaramin abu bane, sai mutun ya cika mai sifofin kamala zai samu wannan matsayi, ina alfahari da kai kuma ina farincikin kasancewa yar cikinka, bana fatan rana ɗaya da zata zo na saɓa maganarka komai kankantarta, hakika da dikkanin ƴaƴan duniya zasu samu uba irinka to tabbas da kowa ba zai so matsawa kusa da mahaifinsa ko nan da can ba, kai ne bangona kuma farincikina, abin alfaharina sanyin idaniyata ni da ƴan uwana, duniyarmu gabaɗaya, ɓacin ranka dai'dai yake da rugujewar Daular Qahtaniyawa daddyna, meyasa zaka ɓata ranka a kan waɗan da kasan already bayinmu ne?"................. Ta kare maganar haɗe da jefa mashi tambayar tana kallonsa.

Tun da ta fara magana ransa ya fara sanyaya, yana shiga tsananin farinciki a dik lokacin da Æ´aÆ´ansa suka furta suna alfahari da shi, farincikinsa ba mai misiltuwa bane, hakan yasa ransa ta wani irin sanyaya sosai.

Fahimtar ya yi farinciki da jin kalamanta yasa ta ɗaura da cewa. "Daddyn yin yaki a halin yanzu da muke cikin nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, saboda kaga muna da baki daga ƙasashe daban daban, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu, ina neman alfarmar da a janye batun yakin nan ayi masu lamauni, nasan kai mai afuwa ne mai kuma tausayin jama'arsa ne".

Sosai su commander Zafar suka ji daÉ—in furucinta, sun kara ganin girmanta, dama can suna tsananin kaunarta saboda sanin yakamatanta suna kuma girmamata, bata da san kai, hukunci cikin adalci take yankewa.

Cike da tsantsar so da kaunarta ya ce. "To Raeesa me kike san na yi masu a yanzu kenan? Kin dai san babu wanda na tsana a duniya biyun King Abdul Mutallab da kuma King Al Mustapha".

Nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Na sani daddyna, kuma kana kan dai'dai, amma idan ba damuwa ni ka bani izinin in je in yi magana da shi".

"Kina ganin hakan zai sakaki farinciki ya kuma biya buƙatarki?".

Jinjina mashi kai ta yi tare da amsawa da e. Dawo da kallonsa a kan commander Zafar ya yi tare da bashi umarnin da ya yi mata rakiya haɗe da wasu zaƙwaƙuran warriors ɗin su take mashi baya, kada su bari komai ƙanƙantar wani abin ya taɓata.

Cikin girmamawa suka risinar da kai haɗe da karɓar umarni. Miƙewa tsaye ta yi tare da karisowa gaban King, ta duka a saman gwiwowinta cikin ladabi da biyayya ta bayyana godiyarta a garesa haɗe da nuna mashi ta yi farinciki na sauraron korafinta da ya yi ya kuma yi amfani da shawarinta.

Hannunsa ya É—aura saman kanta ya fara kwararo mata madarar albarka. Su commander sai tayata amsawa suke yi da amin ya Allah.

Tsawon 5 mins tana tsugunne a gabansa har sai da ya gama zuba mata addu'oin nasa ne ya bata umarnin ta tashi su je. Sumbata a goshi ta ɗan miƙe ta kai mashi kafin ta miƙe tsaye gabaɗaya, ta yi gaba su commander Zafar suka rufa mata baya, alkyabbarta sai jan kasa yake yi.

===========================💘

Tin daga nesa ta hango sarkin Qahtaniyawa dake a saman koshashiyar dokinsa, kai daga ganinsa kasan ya ji izza da isa malam, dukiya ta yi mubaya'a, kayan adan da aka kawata dokinsa da yake kai kawai ba karamar dukiya bace, babban sarki ne mai isa da izza, sai dai a karkashin Daular kingdom of power suke, sun taɓa bijirewa umarni da dokikin King Zuhair har ya yakesu.

Warriors sun kai 20 zaƙwaƙuran sadaukai ne suka take mata baya, tana a tsakiya, commander Zafar yana gefen damanta, sarkin Fada yana a gefen hagunta, kai daga ganin yadda take taku kasan jinin Modarawa ne yake gudana a cikin jikinta, ga jinin mulki dake ratsa jikinta, ai kunsan abin ba'a magana.

Ganinta yasa King Al-Mustapah ya buƙaci sauka daga saman dokinsa, dan ko baa gaya mashi ba yasan ita ta wakilci King Zuhair, dama yasan da wuya King Zuhair ya yarda ya basu fuskar da zasu iya shiga cikin kingdom of power ɗin ko su sami damar yin magana da shi kawai dai sun gwada ne dama, kun san ance a rashin ta yi ake barin arha.

King Al-Mustapah yana sauka daga saman dokinsa dikka sauran Æ´an rakiyansa ma suka yi kasa, suka sauka.

Step biyar tsakaninta da shi ta dakata a wajen tana kallonsa from up to down.

Cikin girmamawa ya yi mata barka da zuwa. A maimakon ta amsa sai ta yi shiru na tsawon good 2 mins tana kare masu kallo.

Har sun fidda ran zata tankasu, har sun fara tunanin ko dai King Zuhair bai bata damar ta yi magana da su bane, ko kuma wani abin ake shirya masu.

Sun luluƙa duniyar tunani kamar daga sama suka tsinkayo voice ɗinta tana faɗin.

"Menene ya kawoku nan?".

A kanta King Al-Mustapah ya tsayar da kallonsa, tsohon zumar soyayyarta ce ta taso mashi, ya so Aunty MieMie kamar hauka, amma King ya hanashi ita sakamakon tsohuwar mummunar gaba dake a tsakaninsu tun iyaye da kakani, kada ku manta jinin Modarawa basa yafiya kuma basa matuwa, in baku gaji da faÉ—a ba ko shekara miliyoyin za'ayi ana yi ba zasu gaji ba.

Dalilin haukar san ta da yake yi ne ma yasa yake bata girma kamar yadda yake bawa mahaifinta King Zuhair.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

"Dama mun zo ne muna masu miƙa wuya haɗe da mubaya'a kamar yadda muka buƙata a baya mai girma King ya ki yarda, bamu gaji ba a wannan karon ma mun sake dawowa da kokan bararmu a garesa, ki taimaka ki sanar da shi mun durkusa a kan gwiwonmu muna masu mubaya'a da kaskantar da kai, ya yi hakuri mu koma zama kamar da tsawon shekaru da suka shuɗe, wanna gaba na iyayenmu ne ba namu ba..............."

ÆŠaga mashi hannu É—aya ta yi alamar ya yi mata shiru, hakan ne ya katse maganar da yake yi.

Tin da ya fara yin magana ta fahimci akwai zallar munafurci da tuggu haɗe da sharri da zallar karya a cikin kalamansa, a yanayin karantarsa da ta yi ta fahimci shigo shigo ba zurfi yake san yi masu, so ta gane komai, shekara nawa tana tare da waɗan da suka fishi sanin duniya, zata iya cewa dik duniya bata taɓa ganin bakin bakiri irin King Abdul Mutallab ba, shi ma bai sha ta daɗi a hannunsu ba bare King Al-Mustapah ba.

Cike da isa da izza ta ce.
"Umarni nike baku ba shawara ba! Ku yi gaggawar barin nan tin kafin rai'na ya ɓaci, ka dai san ba zamu karɓi wani risinawarku ba, dan bamu da buƙata!".

Zai sake yin magana ta ɗaga mashi hannun alamar bata da buƙatar sake jin ko uppan daga gare shi, daga haka ta ce.
"Commander nan da mintuna 5 idan basu bar nan ba ku yi masu zobe ku yakesu!".

Ta yi maganar a dake ba tare da ta kalli in da commander yake ba, yana kai karshen maganar kuma ta juya cikin zafa ta bar wajen.

Har ta É—an yi nisa a tafiyar tata sai kuma ta juyo, cikin kakkausar murya ta ce. "Babu sulhu a tsakaninmu da ku har abada, ayi ta yaki daga nan har illah Masha Allah, muddin ba zaku daina zalinci ba, mu kuma ba zamu É—aga kafa ba, babu wani sauran azzalumi da zamu bari ya sarara!".

Tana kai karshen maganar ta wuce abinta, a hanzarce warrios goma suka rufa mata baya, warrios goma kuma suka tsaya a tare da commander Zafar dan su kori su King Al-Mustapah!.

========After some hour=========💘

King Al-Mustapah ya juya ya koma Daularsa, su commander an dawo cikin gida dan cigaba da shagalin biki, hankalin kowa a kwance, sai kaiwa da komawa ake yi, ana ta hidima, abubuwa sun kara tsananta, haÉ—uwa iya haÉ—uwa.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••💘🔥

Waje ya yi waje, cikin katafaren hall dake cikin kingdom ɗin aka shirya wanna gagarumim taro domin dinner bikin, haɗuwa iya haɗuwa wanna waje ya yi, an zuba sabin furniture da komai da komai, zayyana maku ƙawatuwar wannan waje ma ai ba zai yi wu ba, dan ya zarce tinaninku.

An ƙawata kujerar zaman amarya da ango sosai, gabaɗaya cikin hall ɗin matasan ƴaƴan manya manyan sarakuna da shuwagabani masu ji da kansu ne a ciki, iyaye basu halarci wajen ba, saboda abu ne na yara matasa, Auntynsu Jawad ita ce a gaba wajen kawatawa gimbiya Chuchu kwalliya, har yanzu bata san cewa Jawad aka aurawa Chuchu ba Rizwan ba, King ya bar abin sai bayan komai ya lafa za'a yi maganar, iya momma ce kawai ta san a matansa ma.

Abu fa ya yi abu, sai dai ango Jawad dik a susuce yake, bashi da kuzari ko kaÉ—an, hankalinsa dik ya karkata a kan Rizwan yanzu, amma ba karya kwalliyarsa da ya sha ta yi kyau over, dik da akwai É—an rama a tattare da shi, hakan bai hana haiba da kalama tasa ta bayyana ba, ya fito a jikin Akka É—insa, zallar madarar kyau.

Sai shirye shirye ake yi da misalin karfe 11 na dare za'a fara gudanar da dinner É—in.

To bari mu garzaya wani part kafin lokacin yin dinner ya cika sai mu dawo dan ganin yadda komai zai gudana.

=======BLACK 🌑 WORLD🪐========

Today part in this Black world is the best part amount the previous part's!! I really like this part more than your expectations 💘 because I really like islam, am very very proud to be a Muslim💘 a kullum burina in ga ina magana a kan addinina tare da manya manyan hujoji, ina faɗar niimomin addinina da fifikonsa da kowani addini, kai ba zan iya gaya maku yadda nike kaunar musulmai da musulci ba wlh, Allah dai ka kara mana soyayyar Manzon Allah, amma muna alfahari da musulunci kam ba karya!!.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Chapter 20 · 0% Book details