← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 242

Sashe 182

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hanzarce ya girgiza mata kai kamar wani yaronta, bawan Allah yanzu ma fa kuskure aka samu ya taɓa ɗin ba halinsa bane, ashe bala'i ya taɓowa kansa bai sani ba. Harara ta dallah mashi kafin ta fara zagaye shi tana binsa da kallon up and down. "Shekarunka nawa ne?". Ta faɗa tana dawowa ta gabansa, irin ita babban nan. ...... "19 to 20 haka". Ya bata amsa a sanyayye, shi dai damuwarsa kada ta faɗawa su Jaish, idan zata tsaya a iya faɗawa momma shikenan bashi da wata matsala, amma idan su Jaish suka ji me za su ce? Kuma wlh yasan idan ba lallaɓata ya yi ba kowa a cikin kingdom ɗin nan sai yasan ya taɓa mata kirji ta ja mashi raini har wajensu Omaid, to wai shi me ma ya kaisa ne?.

"19 to 20 years? Ashe ma baka wani fini sosai ba, amma ya aka yi ni jaruma ce kai kuma rago? Kenan girman banza ka yi?". (Allah mai iko🤔 wani abu sai Mahreeh, shekaru 7 fa ya bata amma wai bai wani fita ba saboda shegen san girma.)

Kai ya girgiza mata a karo na biyu. "Ni ba rago bane, kawai bana iya jure rashin lafiya ne, kuma ciwon nawa yana da tsanani sosai ba yadda kika zata ba, ban da ɓangaren ciwo babu wani abin da ba zan iya yinsa tamkar jarumi ba". Tun da ya fara magana idanunta a kan kyawawan roman lips ɗinsa irin na Auta........ "Kai ko lips ma baka da shi, ji bakinka kamar babu saboda ƙanƙata". Tana magana tana binsa da irin kallon da take yi wa su Abu a kauye.

Shiru ya yi dan bashi da abin faɗe, tun da ance bashi da baki ai dole ya yi shiru....... "Buɗe mun rigarka nima in taɓa shikenan sai in yafe maka". Ta faɗa tana kai kallanta ƙasa, ita kanta abin ya yi mata nauyin da ba zata iya haɗa ido da shi ba idan zata aiwatar da hakan, amma saboda tarihin rayuwarta bata yafiya yasa ba zata iya haƙura ba sai ta rama..... Shi kuwa, wani irin sanyi ya ji a ransa, ko ba komai zata rufa mashi asiri idan ta rama, dan haka a hanzarce ya ɓalle butiran rigar ya cire mata, kanta a ƙasa taki ɗagowa saboda iskanci ya cika ƙwaƙwalwarta, kai wlh Mahreen sai kun sakata a addu'a, ni kam Princess Teema ta fi karfina!.

Zare white singlet dake ciki ya yi, ya rage daga shi sai short, sannan ya ce mata. "To ga shi na cire maki ki rama". Tamkar zai yi kuka ya yi maganar. Slowly ta fara kallansa daga ƙasa tana haurawa sama. Ƴar ƙaniya sai da ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba, kirjinta ya bada bugun dum!!! Dum!!! Saboda kirjin nasa da ta gani, a tinaninta bashi da karfi, sai kuma ta kalli yana da murɗaɗɗen jiki, ta yi mamaki sosai, amma fa ta kasa iya yin sama da kallonta, a iya kirjinsa ta tsayar da idonta, dik rashin kunyarta ta ji shakkar haɗa ido da shi at this moment.

"Taɓa ki rama to". Ya sake faɗa idanunsa a kanta, ko kaɗan bai ji burgesa da take yi a da ya ragu a ransa ba, sai ma karuwa ya yi, yana mugun san confidence ɗinta da tsayawa a kan maganarta idan ta yi. Babu kunya ba tsoron Allah ta ɗago hannunta na ta kerma ta nufi kirjinsa da shi da nufin ta taɓa ita ma ta rama. The way tana matsar da hannunta garesa, the way hannunta yana tsananta kerma, amma dik da haka ta danne, ta nufesa. Ya zuba mata idanu kawai yana jiran ta aiwatar da nufinta ya mayar da kayansa.

Tana gab da taɓa shi sai ta dakata tare da fashe mashi da kuka mai ɗan sauti. Ɗan zaro idanunsa kaɗan ya yi, a rikice ya fara tambayarta lafiyarta kuwa? Me kuma ya sake samunta?. Kin kula shi ta yi, ta cigaba da kukanta. Matsawa kusa da ita sosai ya yi ya hau rarrashi, yarinya sai kace mai aljanu, shi yanzu to me ya yi mata da take kuka.

Yana can yana tinanin me ya yi mata sai jin voice ɗinta ya yi tana cewa. "Saboda kasan ba zan iya ramawa bane yasa ka ce in taɓa nima, wlh to Allah ya isana kuma ban yafe ba.........". Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Gudun kada tasa a gane halin da suke ciki yasa ya yi gaggawar janyota jikinsa ya rungumeta, muryarsa har tana kerma wajen cewa. "Please kiyi shiru, zan yi dik abin da kike so, amma please ki yi shiru kin ji?". Kin kula shi ta yi tana cigaba da kukanta. Damuwa da tashin hankali yasa ya yi gaggawar kamo hannun nata ya ɗaura a saman kirjin nasa dai'dai nipple ɗinsa, a rikice ya ce. "To ga shi nan yanzu ai kin taɓa kin rama, dan Allah ki yi.......".

Kasa iya kai karshen maganar ya yi sakamakon idanu da ta wurgo mashi, ga shi suna kusa kusa da juna, ta bushe mashi tamkar wadda aka zarewa ruhi, ƴar ƙaniya ta ji ta taɓa kirjin maza, tuni bakin nata ya mutu, kukan ma ta nemesa ta rasa. Ya ɗan tsorata ganin yadda ta kafesa da ido bata wani motsi, a rikice ya kai hannu ya fara jijjiga kumatunta yana ambatar sunanta. Ina bata motsa ba, a nan ya fahimci sume mashi a jiki ta yi, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rage tsawonsa ya ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa, sai faman nisawa yake yi. Ya tsira daga bala'inta!!

Yana kwantar da ita aka fara knocking na door É—in nasa, wani irin fargaba ya ji, gabansa ne ya yanke ya faÉ—i, murya na rawa ya tambayi wanenen? Daga waje Omaid ya amsa mashi da shi ne. Ai sake rikicewa ya yi, abin da yake gudu ne yake shirin faruwa, wato kannensa su kama shi da ita shikenan girmansa ya zube. Rasa me zai cewa Omaid ya yi, ga shi bai isa ya hana shi shigowa cikin É—akin ba.

My people's ko kuna da wani abin cewa? Ko kuna da dabarar da zaku faÉ—awa guyson ya yi dan ya tsira daga Omaid ya gane suna tare da Mahreen?. To idan kuna da shawara ku yi gaggawar bashi kafin in dawo daga Black world.

🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

Washegari da safe, sanye take cikin jelly dreass launin pink, ta yi masifar kyau, ta É—aure haÉ—aÉ—É—en gashin kanta, da karfi da ya ji Sweetie ta koyi yawo babu É—ankwali, aka ce zama da maÉ—auki kanwa shi ke kawo farin Kai.

Tsaye take a tsakiyar bedroom na Ronnie, kyawawan kafafunta na sanye cikin flip floor launin white color, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai, sai wani sheki yake yana wani ɗaukar hankali, sai launin dark purple lips ɗin nata ya kara turuwa sosai, idanunta sun kara kyau tamkar ta sanya kwalli alamar tana cikin farinciki sosai kenan. Ronnie dake zaune a tsakiyar bed ɗinsa sanye da pj's dress a jikinsa ne ya harbeta da wani ɗan ƙaramin throw pillow yana faɗin. "Ba zan barki ba, sai kin faɗa mun shirinki".

Yana jefo mata pillown ta yi gaggawar juyowa haɗe da buɗe tafin hannunta, take magic ɗinta ya fita ya daki pillown, kai tsaye ya koma ya daki face ɗin Ronnien. Ƙayataccen murmushi ta saki kafin ta ce. "Alhaki cuicuyo, yanzu dai pillownka ya koma kanka". Tana magana tana kara faɗaɗa murmushinta, wlh sai ka ji ba zaka taɓa gajiya da kallanta ba matuƙar tana wannan sanyayyar murmushin nata. Shi kansa Black Tiger bai san ɗauke idanunsa daga kanta idan tana yi, shi ma dai Ronnie yana kyatsawa sosai, tana bashi a jikinsa.

Cikin zafa ya miƙe tare da dirowa kasan bed ɗin. Da gudu ta watsa ta nufi waje tana faɗin. "Idan ka isa ka kamani, in ka kamani zan baka satar amsa"....... Tsayawa ya ɗan yi tare da riko waist ɗinsa da hannayensa dikka biyu, a ɗan kule ya ce. "Is better for you da ki tsaya ki faɗa mun, in ba haka ba in na kamaki i will give you a hot punishment"...... Tana ƙoƙarin buɗe kofa ta amsa mashi da. "Fara kama ni ɗin tukunnan before you think about the hot punishment da zaka yi mun ɗin"........ "Kin rai'nani ko? Yau Allah ba zan barki ba". Ya kai karshen maganar tare da bin bayanta da gudu. Tini ta buɗe kofar ta yi waje tana dariya tana kara faɗin maza ya zo idan ya isa.

A gaggauce Black Tiger ya matsar da su daga gaban mirrornsa, dama su yake kallo, wani irin farinciki yake ji idan yana kallansu, amma kuma baya san su kama shi yana kallonsu, in dai yasan za su zo bedroom ɗinsa sai kuga ya fiske kamar bai san da su a empeir ɗin ba, alhalin munahiki ɗan air daɗin ganinsu yake ji, har da wani pretending ya yi gaggawar barin gaban mirror ya dawo tsakiyar bedroom ɗin nasa, sanye yake da bathrobe, linƙaya fa zai je yi a cikin karamar pool ɗinsa dake sama, amma da yaga suna dirama sai ya tsaya kallansu.

Da gudu Sweetie ta faÉ—o cikin bedroom É—in nasa tana dariya tana kara faÉ—in Ronnie ya zo in ya isa. Da gudu shi ma Ronnie ya faÉ—o É—akin yana faÉ—in Allah sai ya kamata yau, dan dole ya gwada mata akwai banbanci tsakanin mata da maza, ta ce idan bai kamata ba shi rago ne, dan haka shi ba rago bane dole ya kamata. Bayan Black Tiger ta zo ta tsaya tana haki tana faÉ—in. "Yi sauri ka zo, gani a bayan big bro kuma our shield".
Chapter 182 · 0% Book details