← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 242

Sashe 126

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sanyin murya ta ce. "Am so so sorry, this is ur phone". Ta yi maganar tana miƙa mashi wayar.
Miƙewa tsaye shi ma ya yi, a maimakon ya karɓi wayar sai ya harɗe hannayensa a kirjinsa yana binta da kallo. Ɗan ƙasa kaɗan ta yi da kanta, kamar zata saki murmushi saboda wani irin bargon farinciki da ta ji ya lulluɓe zuciyarta ba tare da tasan dalilin farincikin ba.

Ya ɗauki a kallah 2 mins again yana ta kallanta kafin ya miƙa hannu ya karɓi wayarsa, cikin natsuwa ya juya ya nufi hanyar fita, yana tafiya yana waigota, wai a haka ma dan King ne ya yi mashi waya da ya same shi a main parlour, da ba zai tafi ya barta ba, sao ya tsaya jin wacece ita, amma King na jiransa, dan haka ya wuce yana kara waigota.

Ita ma wucewa gaba ta yi, tana tafiya tana waigosa, da alama ta ya burgeta. Saman É—aya daga cikin sofas na wajen ta zauna tana dawo da kallonta a wajen, ta fara rarraba idanu tana kara jinjina irin dukiyar da aka narka a wajen.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥

Mammie and Fanan, zaune suke suna shawarin yadda zasu ɓullowa lamarin Fanan da Jaish, mammie ta ci alwashi kuma ta yi rantsuwa da Allah sai Fanan ta auri Jaish, idan ba haka ba Jaish ɗin ya mutu kowa ya rasa, sai tsara yadda zasu wahalar da Mahnoor suke yi, yanzu Mammie ta gama tsara yadda za'ayi Fanan ta koma part ɗin Jaish da zama tare da mama Haulat kenan, ta kuma tsarawa Fanan ɗin irin abin da yakamata ta yi wa Mahnoor idan ta koma can da zama.

Ita kuma Sarina ta gama tsara mata yadda zata buga barikanci wajen samun soyayyar Jaish ko yaki ko y so, har da faɗa mata wai idan dare ya yi ta rinƙa saka sleeping dress tana zama a parlour da sunan zata yi kallo, hakan zai rinƙa jan hankalinsa a gareta, Sarina dai ta bata shawarin zama karuwar cikin gida sosai,......... My people's me kuke tinani a kan wannan shawari na Sarina? Anya kuna ganin hanya ce mai ɓillewa Fanan kuwa?.

A gefe guda kuwa, Sarina and abokanan rashin mutumcinta ne suke zaune a rest parlourn uncle Abbas suna shirya wani makircin, Omaid dai sai chatting yake yi a Whatsapp da sabuwar budurwarsa, shi kuwa Obaid sai tsarawa Sarina yadda komai zai gudana yake yi, shiri suke yi a kan yadda zasu ganawa Mahnoor azaba, tana neman da su tayata tun da kunga su suna da kunama da kwari, shi ne ta nemesu a kan wannan harka, dama kun san mutanenta ne. Obaid sai tsara mata yadda za'ayi yake yi, shi kuma Omaid yana chatting.

Sosai Sarina ta so yi wa su Obaid wayo wajen tambayarsu wanenen Omerish? Sai dai bata fito ta tambayesu wanenen shi kai tsaye ba, gudun kada su zargeta, ta fake da ce masu.

"Obaid na yi mafarki wani kyakkyawan saurayi mai cikar mazantaka da jarumta, dogo mai kama da daddy, ga shi da fuskar kwarjini da haiba, fari tas kamar momma, yana da saje irin na daddy, sai dai kwayar idanunsa irin na Auta ce wato hazel, sannan sunansa Omerish".

Lokacin da ta ambaci sunansa sai da dikkansu suka É—ago da kallonsu a kanta, lokaci guda kuma ko me suka tuna suka yi gaggawar kawar da kallonsu daga kanta suka cigaba da abin da suke yi. Ta fahimci sun yi shock da jin sunan da ta ambata, hakan yasa ta kara tsananta zarginta a kan abin da suke zargi ita da Mammiensu.

Cigaba ta yi da yi masu zabara dan su faɗa mata wanene Omerish kuma me hotonsa yake yi a wajen momma da har ta iya ɓoyewa a kasan bed ɗinta bata san kowa ya gani (kun tuna envelope da ta ɗauka a kasan bed ɗin momma? Hotunan dake ciki kenan, a jikin hoton matashin ne aka rubuta Omerish, a nan tasan sunansa). Sai dai da yake suma A ne wajen dabara da kaifin ƙwaƙwalwa sai suka shashantar da ita, suka tsara mata labarin karya wanda dole in mutum ya ji ya yarda da su. Suma da wayansu ashe.

A ɓangaren guda kuwa, Chuchu and Yah Jawad sai kashe junansu da love suke yi, yanzu hankalin Chuchu ya kwanta dan Auta ta dawo, sai kashe Yah Jawad da salan soyayyarta take yi tana rikita mashi ƙwaƙwalwa, dik abin da ta iya dange da soyayya tana iya kokarinta wajen koyar da Mahnoor, amma ita Mahnoor wai kunyar kwatantawa Jaish take ji, ga tsaronsa dake ranta, yanzu sun dawo wasan ɓuya ne ma, in yana nan bata fitowa parlour, sai ta tabbatar ya fita, kuma bata zuwa bedroom ɗinsa, saboda ta samawa kanta lafiya.

Suna tsaka da zuba soyayyarsu King ya yi wa Jawad massages a kan ya zo main parlour ya samesa yanzun nan. Dan dole ba dan ya so ba ya fita zuwa parlourn a tare da Chuchu É—in.

A wani ɓangare kuwa Pretty and Mahreen da mama Haulat ne suke zaune suna hira, mama Haulat na koya masu abubuwa dan kara wayar masu da kai. Daga gefen su mama kuwa, mama tana can kishi kamar zai kasheta, ita kuma mummyn Chuchu tana fama da takaicin abin da yake faruwa tsakanin Auta da commander Zafar, ita a ganinta ai ba laifi bane dan Hoorain ya so Auta, saboda Auta fa tana da kyan da dik wani namiji ya ganta sai ya kyasa, kuma kada ku manta mummy ƴar talakawa ce, so bata ga dalilin da zai sa a wulaƙanta talaka kaman ita kuma ta goyi baya ba.

Waɗan nan sune kaɗan daga cikin abin da yake faruwa a cikin kingdom of power ta kowani ɓangare kenan. Mu koma kan labari in da muka dosa kenan.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Cigaba kuka Auta ta yi tana kara faÉ—a mashi zasu yi nasara, ya jure saura kaÉ—an ne, dama dik abin da bawa yake so sai Allah ya jarrabcesa a kansa, to suma su É—auki wannan a matsayin jarrabawarsu. Suna tsaka da karfafawa junansu gwiwa unexpect suka ga haske ya gauraye cikin É—akin. Kafin ta yunkura domin ganin wanene sai ji ta yi an damki hannunta. Da karfi aka figeta, ta kofa aka fita da ita.

Dikkansu biyu idan hankalinsu ya kai miliyan to ya tashi, bana kaman Hoorain da ya shiga tashin hankali kamar zuciyarsa zata buga, damuwarsa É—aya shi ne za'a hukunta mashi ita, hakan yasa shi a damuwa.

Ita ma bata kanta take yi ba, hankalinta a kansa, ta kara ja mashi wani musifar, sai ta ji ta yi danasanin zuwanta wajensa, yanzu za'a kara mashi azaba kan azaba.

Ba kowa bane ya ja hannunta face King, idan baku manta ba na faÉ—a maku yasa idanu a kanta, dik wani motsinta yana sane da shi, so tin da suka fita ita da guyson suke a kan idanunsa, ya gansu sarai, yanzu haka ya kama guyson É—in ma yana main parlour, shiyasa ya yi wa su Jawad dikka massages a kan su same shi a parlourn, dan zai É—auki tsastsauran mataki a kan Auta da guyson, bawan Allah guyson dik ya sha jinin jikinsa.

King bai zame da ita ko'ina ba sai main parlour, sai kuka take yi tana yi mashi magiya a kan ya yi hakuri ta tuba ba zata kara ba.

Sam bai saurareta ba, yana zuwa ya tsayar da ita a tsakiyar parlourn, da karfi ya ɗauke fuskarta da mari sai da ta tafi ta kifa ƙasa. Da gudu Chuchu ta yunkura zata tashi ta nufi Autar. A miliyan Jawad yasa hannu ya riketa, tana ƙoƙarin kwace hannunta King ya daka masu wani irin tsawa wanda ya sanyata komawa jikin Jawad a miliyan ta lafe, tin da suke basu taɓa ganin King cikin ɓacin rai irin na yau ba.

Kowa yana cikin parlourn banda su Zee da suke ba ƴaƴan familyn ba, sannan Jaish ma baya nan, amma tin daga kan su uncle Jahiz da suke cikin kingdom of power har kansu Omaid dik suna parlourn, su Mammie, uncle Abbas dik kowa ya hallara. Dan ran King ya ɓaci.

Akka tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ita kanta bata goyan bayan wannan alaƙa ta Auta and Hoorain.

Sai huci King yake yi, Auta and guyson dik suna zube a ƙasa suna kuka, shi guyson King bai dakesa ba, taya Auta kuka kawai yake yi, ita kuwa nan take shatin yatsun king ruɗu ruɗu suka fito a face ɗinta, ta masu ne matiƙa.

Mummyn Chuchu ce ta yi ta mazan buÉ—e baki, cikin girmamawa ta ce. "Allah ya huci zuciyarka, dan Allah ka yi hakuri, ka kyale Zunaira haka, kada ka hukuntata a bisa laifin da ba yin kanta bane".

Aunty MieMie ce ta capki zancen da cewa. "Daddy ni kaina baka taɓa sanya hannu ka dakeni ba, ba ni ba, na tabbatar gabaɗaya tun daga kai'na har kan Obaid baka taɓa ɗaura hannunka a jikinmu da sunan duka ba, kuma dik mun san cewa kafi san Auta fiye da kowa, dan Allah daddy ka dubi irin san da kake yi mata, ka yi mata afuwa ka dubi irin san da take yi wa Hoorain..........".

Kasa ƙarisa maganar Aunty MieMie ta yi sakamakon wani irin kallo da King ya wurgo mata, cikin kakkausar murya ya ce. "Wlh na yi rantsuwa da girman Allah, ba zan taɓa bawa Hoorain Zunaira ba, idan zata mutu ta mutu, ba zan yi kaffara ba, wlh billahi na yi mata iyaka da shi, babu ita babu shi, idan taki kuma to tabbas zan sa a kashesa".

Ai Auta tana jin karshen maganar King bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye ba, kisa kuma? Ta maimaita a ranta, ba komai ya ɗaga mata hankali ba face tasan mahaifinta baya magana biyu, tsab zai aikata abin da ya yi niyya, tabbas zai iya sawa a kashe Hoorain.
Chapter 126 · 0% Book details