← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 242

Sashe 193

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar guyson ne tasasu kai kallansu a bakin kofa dikka har da Mahnoor ɗin. Ai yana sauke idanu a kanta bai san time ɗin da ya kwashe da dariya ba, har da rike ciki yana duƙawa ƙasa. Kallan mamaki ta bisa da shi, ta rasa gane me yake yi wa dariya. Ai Momma ma bata san time da murmushi irin nasu na manya ya kubce mata ba ganin yadda guyson yake dariya, dama tun ɗazun dariya kamar zai haukatata, da kyar ta iya dannewa ta ɓoye, sai ga shi guyson ya zo ya sanyata murmusawa.

ÆŠan tsuke fuska Mahnoor ta yi tana bin guyson da kallo. Cikin dariya ya ce. "Aunty Mahnoor wace mahaukaciyar ce ta yi maki wannan make up É—in? Kin ganki kuwa? Ko aljana Bilkisu sarkin kwalliya bata gwada maki hauka ba yau". Ya kai karshen maganar tare da kara kwashewa da dariya mai sautin gaske.

A hanzarce Mahnoor ta kai hannu ta shafi face É—inta, jin alamar kwalliya yasa ta yi gaggawar É—ago ido ta kalli Jaish. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta kamar ba shi ba.
"Yah Omar kana nufin kwalliya aka mun?". Ta faɗa tamkar zata yi kuka. "Aww dama baki san da kwalliyar ba?". Cikin dariya ya yi maganar!. Takaici kamar Omaid ya kifa mata mari, shi kallan wawuya yake yi mata, ya tsani wawta a rayuwarsa. Miƙewa tsaye ta yi, jiki ma ɓari ta isa wajen guyson. "Yah Omar wlh ban san anmun kwalliya ba, faɗa mun ya na yi?!". A rikice take maganar.

Har lokacin dariya taki sake shi. Hannunta ya riƙo tare da janta suka nufi gaban tampatsetsan mirror Momma. A wajen ya tsayar da ita tare da nunata ta cikin mirror da hannu yana cigaba da dariya ya ce. "Look at you". A hanzarce ta kai kallanta kan mirror. Ai a miliyan ta wani irin zaro idanu waje, take kuma ta ji wani irin kunya ya kamata, gabaɗaya face ɗinta uban kwalliya na mahaukata. Kunya tamkar ta natse ƙasa, ta gagara juyowa ta kalli su Momma, sai dariya guyson yake cigaba da yi, ta tsaya a wajen tsit kamar daskararren man shanu.

Kallan Jaish Momma ta yi tare da cewa. "Me ta yi maka da ka yi mata irin wannan kwalliya haka?". Ƙasa ƙasa ta yi maganar ta yadda babu wanda ya ji sai ita da shi ɗin. Nan fa shi ma kunyar rashin kunyar tasa ta motsa, ƙasa ya yi da kai, kamar yana tsoron yin magana ya amsa da. "Babu kawai na tina abin da ta taɓa yi mun ne a garinsu". Cike da mamaki Momma ta bishi da kallo. "Kenan yanzu ka tina wacece ita a gareka?". Kai ya ɗan jinjina alamar e ya tina, kuma ba tin yau ma ya tina ba, tin ran zuwan Smart, akwai wani rana da ta shiga ɗakinsa a lokacin yana rike da wayarsa, idan baku manta ba har ya miƙe tsaye yana kallan wayar kuma yana kallanta, tin a wannan rana ya tina rayuwarsu na kauye, ba komai yasa ya tina ba face kallan video bikingsu da ya yi a media, ranar da aka yi bikin in baku manta ba na ce maku akwai masu vivo wato ƴan gayun kauyen da suka rinƙa ɗaukarsu a video, to a wannan rana ya tina wacece ita a garesa ta sanadiyyar wannan video, amma ya yi shiru bai nuna mata kamar ya tina komai ba, sai dai zuciyarsa ta gagara hakura har sai da ya nemi Mahreen ya kalleta ba tare da saninta ba, kaunar Mahreen a jininsa take wlh, dan ita ta fara kula da shi a kauye, kowa ya gujesa ban da ita, shiyasa take ta daban a ransa!.

Ganin ta gagara motsawa a wajen ne yasa guyson ya riko hannunta tare da cewa. "Let me escort you ki je ki wanke face ɗin naki a part naku sai mama Haulat tai maki wani make up ɗin mai kyau". Sam bata yi musu ba ta bisa, dan dama so take yi ta bar wajen. Kunyar momma yasa ta gagara motsawa. Ta kasan ido Jaish ya bisu da kallo har suka fita, sannan ya miƙe tsaye. "Momma ina zuwa". Tsabar farincikin da Momma ta shiga na tina Mahnoor a rayuwarsa da ya yi yasa ta gagara yin magana, sai sakin cool murmushi kawai take yi, shi ma ya lura da yadda ta shiga farinciki, ya ji daɗin abin matuƙa.

Bayan su Mahnoor ya bi, dama ba wani fita da zai yi, kawai ya biyota ne ya ga yadda zata kare da ƴan gida, wato a fakaice dai ya rama abin da ta yi mashi, ta sanya shi jin kunyar bappa matuƙa, tamkar ya natse cikin ƙarƙashin ƙasa a wancan ranar, to shi ma yau ya rama kunya tamkar ta natse cikin ƙasa.

Lokacin da ya shiga bedroom É—in har guyson ya wanke mata fuskar yana tayata goge shi da towel, ya ce ta zauna a saman mirror chair bari ya yi mata wani kwalliyar mai kyau, dan shi ma ya iya make up sosai zamansa da Sharifat a Dubai, so ta zauna zai yi mata wani kwalliyar mai kyau.

"Waye ya ce ka wanke mata fuska Omar?". Daga bakin kofa suka jiyo voice É—insa, a tare dik suka kai kallansu a kansa, yana tsaye ya É—aure fuska tamau,wai irin sai ya ja mata rai sosai kafin ya fahimtar da ita yasan wacece ita a garesa, yanzu ba zai faÉ—a mata ya tina komai ba.

"Yah Jaish baka ga kwalliyar bashi da kyau bane? Shiyasa fa na wanke mata zan yi mata wani". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar!...... "A haka nike san ta rinƙa kwalliya kullum, kada ka sake wanke mata, kuma a haka zata fita, in bata san a ganta sai dai kada ta fita daga nan ta zauna, amma ni irin kwalliyar nike so". Ya kai karshen maganar tare da shigowa ciki, bilhakki da gaskiyarsa fa ya zage yake maganar, wai irin kada ma su zaci wasa yake yi. Kallan juna suka yi ita da guyson, take idanunta suka cika da kwallah, kenan sai dai ta yi ta zama a cikin ɗaki ba zata fita wajensu Chuchu ba?. Ga shi ya ce irin kwalliyar kawai yake so, wannan ai ba kwalliya bace, hauka ce. Shi ma guyson sam bai ji daɗin batun ba, amma da yake yayansa ne ya zartar da hukunci, sai kawai ya yi na'am da hukuncin, ya kuma yi dabara ya zame jikinsa ya gudu abinsa, ba ruwansa da shiga tsakanin ma'aurata.

Yana fita suka ci karo da Mahreen zata shigo part ɗin, dan tin jiya bata haɗu da Mahnoor ɗin ba. Sai da gabansa ya faɗi, take wani irin fargaba ya lulluɓesa. Sai dai kuma sai satar kallonta ta katsan ido yake yi, Chuchu ƴar wanka ta tsantsara mata kwalliya mai shegen kyau, ta wani kele cikin riga da wando arabiyans dress, ta yi rolling na veil a kanta, gata fara launin kayan dark ash, sai kyanta ya kara bayyana, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm kamar zai ɗiga, sai wani turo shi take yi, kamar ma bata san rufe shi sosai, sai wai yauki take yi bata san taka kasa.

Kamar wani maras gaskiya ya ce mata. "Sannunki". Yana magana cike da Æ´an kame kame, kamar fa tsoronta yake ji, shi kaÉ—ai ya bi ya dibirbirce. Harara ta dallah mashi wadda ta sanya shi haÉ—iyar yawu da kyar, cike da gadara ta ce. "Kada ka sake yi mun magana, kai É—an iska ne ni kuma mai mutumci"..... Kai innalilahi, wai kunji ita mai mutumci, to ai mutum baya cewa ga abin da yake da shi, dik wanda yake da abu ba sai ya faÉ—a ba, mutane da kansu zasu faÉ—a mashi yana da kaza, dik mai cewa yana da shi to bashi da shi ne, in yana da ba zai faÉ—a ba, yanzu fisabilillah kunga Mahreen ta yi kalar mutumci? Innalilahi wannan yarinya zata kashe mutum da dariya, ko da yake dama ance yabon kai jahilci ne, kuma hakan ce, jahilci na É—awainiya da ita shiyasa take yawan yaba mashi kanta, ban da jahilci ba zata yi ba ai, zata bari ne a yabeta!.

"Ki yi hakuri". Shi ne abin da ya faɗa mata, kai ta sa zata wuce tana wani dallar mashi harara da waɗan nan shegun idanun nata masu saka shi ya shiga shakku da zargin kansa ko ya yi mata laifi ne. Har ta ɗan yi nisa da shi sai ya juyo da kallonsa a kanta. "Ki yi hakuri Mahreen, ba zan iya dai'na yi maki magana ba, dan kina daga cikin mutanen dake burgeni nake kuma kauna". Ya faɗa idanunsa a kanta. Cak ta dakata da tafiyar da take yi, wai irin ita ma zata yi na ƴan gayun nan, cike da yanga ta juyo, from head to toe ta bisa da kallo kafin ta ce. "Ni kuma bana sanka, bana mu'amala da ƴan iska, bana san ragwayen mutane, kuma daga yau ba sunana Mahreen ba, Aunty Chuchu ta ce sunana big girl, dan haka sunan da zaka rinƙa kirana da shi kenan, big girl". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta cigaba da tafiyanta. Binta da kallo ya yi yana mamakin yadda take da shegen tsiwar tsiya, wai big girl, siririn murmushi ya saki, lallai Chuchu ma bata san zaman lafiya da take koyawa Mahreen rashin mutunci kala kala, yo in banda abin Chuchu ma Mahreen har za'a kara koya mata wani abin bayan sanka sankan rashin mutuncin da ta iya? Tab gaba akwai show kenan, lallai kuwa. A wani ɓangare na zuciyarsa kuma tinani ya fara yi a kan me zai yi ya birge wannan haɗaɗɗiyar babyn mai tafiya da hankalin mai lafiya, shi dai har yau kome ta yi birgesa take yi!.

Ya jima tsaye a wajen yana tinanin abin da zai yi ya birgeta har ta fara respecting É—insa, daga karshe ya wuce zuwa in da zai je.
Chapter 193 · 0% Book details