Sashe 208
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tin da momma ta samu labarin mutuwar Hoorain ta shiga tantama da tashin hankali, zuciyarta na ayyana mata akwai wata babbar dalilin da yasa King ya gwammaci gara Hoorain ya mutu a kan ya auri Zunaira, sosai momma take zargi da biyu ma King ya saka Hoorain ɗin gadin hall ɗin dinner dan zuciyarsa ta buga a lokacin da zai ga Auta da wani, abin ya tsayawa momma a rai, shiru ta nutsa cikin tinaninta tana tariyo rayuwar baya, ɗauko tinanin ta yi tin daga kan lokacin da matar commander take raye, ita dai tasan ma tin kafin commander ya aureta kamar ita ce kuyangarsu ba kuyanga Zubaida ba, wato ita ce wacce King ya amincewa da ta rinƙa zuba mashi abinci tana kuma girkawa kamar yadda ya aminta da kuyanga Zubaida a yanzu!
Take ƙwaƙwalwar momma ya fara shiga ruɗani, sai a lokacin kuma ta tina ita fa bata taɓa kallan face ɗin Hoorain ba a tsawon rayuwarta! Wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji a lokacin da ta tina bata san face ɗinsa ba! Saura kaɗan kwakwalwarta ya kama da wuta a lokacin da tinanin dalilin mutuwar mahaifiyar Hoorain ya ratso cikin kwakwalwarta, yanzu ta fara tantama a kan mutuwarta, anya kuwa ba kasheta kawai aka yi da gangan ba? Meyasa da ta ɓace babu wanda ya sake yin maganarta bare ma har ya nemota? Meyasa King bai tsaya tsayin daka sun nemota ba tin da amintacciyarsa ce a lokacin?.
Kai ganin ƙwaƙwalwarta yana ƙoƙarin tarwatsewa ne yasa ta miƙe ta nufi wajen Smart, dan wannan tinani ya fi karfin kwakwalwarta. A ɓangaren su mummyn Chuchu dik tinanin da suke yi kenan, wato meyasa King zai tsani Hoorain har haka ne wai?.
Gida ya rikice da koke koke, gidan biki ya koma gidan mutuwa!.
Kwance momma ta isko Smart, ya ja bargo har zuwa saman chest ɗinsa, hannunsa rike da phone ɗinsa yana latsawa. Ya yi nisa cikin abin da yake yi, har momma ta shigo bai ji shigowarta ba, a kusa da shi ta zauna, ganin hankalinsa ya yi nisa a taɓa waya yasa ta kai hannu ya karɓi wayar. Sosai ta ji mamakin ganin yadda ya zabura zai kwace wayar, sam bai yi tunanin ita bace. Yana ganinta sai ya kara ɗaure fuska tare da komawa ya kwanta yana ɗan kawar da kansa gefe.
Bata yi magana ba, amma ta sha jinin jikinta ganin yadda ya ɗaure fuska, alamar ransa a ɓace har yanzu kenan. Juyo da screen ɗin wayarsa ta yi dan taga me yake gani da ya zabura dan an kwace wayar haka. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallan screen ɗin, sai kuma ta dawo da kallonta a kansa, lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, cike da zolaya ta ce. "Wannan ita ce sirikar tawa ne?".
Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma gyara kwanciyarsa da ya yi zai ja bargo ya rufe har face É—insa. Rike bargon ta yi, cikin sigar tausasawa ta ce. "Æacin rai ne ya sanya ni yin wancan furicin, ba wai dan wani abin ba".
A ɗan takaice ya ce. "Amma dai ke kanki kinsa daddy ba'a a kan dai'dai yake ba ko? Meyasa ba zaki yi ƙoƙarin mai da shi hanyar dai'dai ba!"........ "Omerish wannan sarauta ce ba siyasa ba, sarauta da siyasa akwai banbanci matuƙa, kai siyasa ka sani baka san sarauta ba, karfin izza da isa a sarauta yake ba'a siyasa ba, ba komai ake juyawa da karfi a sarauta ba, dik abin da ka gani sai dai ka bishi a haka yadda yake a dokance.........".
Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Babu wata dalili da zata sanya in yi shiru in bar iyayena a kan hanyar halaka, and babu wata dalilin da zai sa in yi shiru a kan saɓon Allah ana aikata ɓarna ba dai'dai ba!!". Ya kai karshen maganar yana sake mata bargon. Ɗan matsawa kusa da shi ta yi. "Zaka iya dawowa nan?". Ta yi maganar tana nuna mashi saman laps ɗinta da hannu. Shiru ya yi mata kamar bai ji ta ba. "Zan faɗa maka wata magana ne"......... "Momma zaki fara ko? Please ki barni in more ɓacin rai'na".
Kai ta ɗan girgiza. "Naki gaskiya, zo ka ji wani magana". Ta yi maganar tana jan dogon hancinsa............. Ajiyar zuciya ya sauke... "Momma dayawan mata sun iya kalaman yaudara, shiyasa bana haɗa hanyata da mace, haka mom take mun irin wannan abin, idan dad ya ɓata mun rai bata barina in more ɓacin rai'na bare in yi fushi in ki kula dad, sai ta zo ta mun kalaman yaudara tasa na manta, shi ne kema zaki mun abin da take mun ko?".
(Malam Smart mu dai mata ba kalaman yaudara muka iya ba, tausasawa da tausayi muka iya, ko ya kuka ce my people's?🤨🤓😇)
Da hannu ta kara nuna mashi saman laps ɗinta ba tare da ta yi magana ba, dan dole ya dawo da kansa samansu ya kwanta yana kallanta. Kyakkyawar dark black curly hairnsa ta fara shafawa, ta lura ransa ya ɓaci sosai, sai ta nemi kawar da zancen da suke yi ta hanyar cewa. "Wannan ce sirikar tawa?".
Ɗayan hannunta ya riko cikin nasa, yana ɗan rarrabe yatsun hannun nata ta amsa da. "A'a kawai dai na ajiye hotonta ne, amma bamu da wata alƙa".
Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Ka tabbata kawai ka ajiye hoton ne?". Kai ya gyaÉ—a mata alamar e. "To meyasa ka ajiye shi kuma meyasa kake ta kallanta?"...... "Kai momma zaki fara ko? Ni kam ma dake da mom ban san wace ta fi wani ba, ni fa ba kallanta nike yi ba"......... Kallan gefen ido ta wurga mashi, da sauri ya sake cewa. "Da gaske momma ba kallanta nike yi ba".................. "Omerish har na shigo É—akin nan fa baka san na shigo ba saboda ka shagala da kallonta, in baka faÉ—a mun gaskiyar wacece ita ba wace zaka faÉ—awa?". Cikin sigar tausasawa ta yi maganar.
Yatsanta na tsakiya ya riko, ring da Jaish ya sanya mata ranar ya fara ƙoƙarin zaresa daga hannun nata, sannan ya ce. "Momma kawai kyau take mun, and ina san wasu ɗabi'u nata, that's all". Ya kai karshen maganar tare da cire ring ɗin. "Kana sonta ne?". Ta jefa mashi tambayar. Da sauri ya girgiza mata kai kamar wani baby. "Momma ni fa ki rabani da sharrin mata, kina ganinsu ƴan yaudara ne, ya na kare dake da mom ma, bare in karawa kai'na wata".
Ita momma sam bata damuwa da yanayin maganarsa without a respect, saboda tasan ya yake tin yana karami, a koda yaushe tana bibiyarsa, to tasan ba wai raini bane, haka ya iya magana.
"To shikenan na ji baka sonta, yanzu dai ta shi ka yi lunch ka ji? Zuwa dare zan zo mu yi magana, ina da magana mai mahimmanci da kai". Ta faɗa tana bin hoton dake saman screen ɗin nasa da kallo, saboda ita kanta ta yi matuƙar burgeta, ta fita sosai a hoton, sai murmushi take yi dimples ɗinta sun lotsa, ga eyesball ɗinta su tura olive sosa, kamar ka saceta ka gudu!.
Jinjina mata kai ya yi haɗe da sakin hannunta ya karɓi wayarsa. "Ki sa Jaish ya kawo mun lunch ɗin a yanzu". Ya faɗa yana miƙewa daga saman laps ɗin nata, dama yunwa yake ji, kawai baya san kulasu ne yasa bai bi ta kan lunch ɗin ba. Ya kuma cire mata ring ɗinta, dan ya ɗan kama hannunta har ya yi mata shaida, shiyasa ya cire kamar yadda a baya Jaish ya cire ya canza mata.
"Allah ya yi maka albarka". Shi ne abin da ta faɗa kafin ta miƙe ta nufi waje. Da kallo ya bita yana jin wani irin kaunarta tana kara narka zuciyarsa, yana san mahaifiyar nan tasa over!.
Komawa ya yi ya kwanta shiru yana cigaba da kallon hotonta. Kamar daga sama ta witsiyar ido ya ga alamar mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. A hanzarce ya juyo da kallansa. Ɗan binta da kallo ya yi kafin gently ya ce. "Wai ke baki iya sallama bane?". Ya yi maganar kallansa a kanta cak. Turo mashi baki ta yi. "A ina zan ajiye maka abinci ya yi mun nauyi sosai a hannu". A maimakon ta bashi amsa sai ta faɗi abin da take da buƙata.
"Ina Jaish da nace ya kawo mun abincin?". Ya tambaya yana wurga mata harara...... Shiru bata amsa mashi ba, dan tana ganin bata da alaƙa da wannan tambayar tin da ita bata ma san wanene Jaish ɗin ba, kawai momma ta shiryata ta ce ta kawo mashi abinci.... Ganin ta yi shiru yasa ya fahimci nufinta, yanzu yana iya karantar shirunta sosai. Kai Pretty duniya, wato tana bawa Smart sabon karatu. Bin kayan jikinta da kallo ya yi, a ransa ya ce dik yadda aka yi momma ta sanyata saka wannan kaya, arabian abaya ce mai shegen kyau launin dark purple, ta yi masifar kyau sosai, sai dai kan nan dai babu ɗankwali, ta saki gashi har baya. A ransa ya ce shegen kyan bala'i ne da ita, kowani irin dressing ta yi kyau yake yi mata tamkar dan ita aka yi kayan! Ya zauna a jijinta zam zama har sai ka ji sha'awar irin dressing ɗin a ranka.
Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta dongwarar mashi da try É—in abincin a tsakiyar bedroom É—in, a cewarta tin da ba zai faÉ—i in da za'a ajiye mashi ba ai tana da damar ajiyewa a ko'ina tin da ba shi ya bata hannun nata ba da zata tsaya tana rike da abincinsa tsawon lokaci, ga shegen nauyin tsiya, dama da kyar ta É—auko shi, ba dan Momma da Allah ba zata É—auko ba!.