← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 242

Sashe 47

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mairo kuwa kuka kawai take yi da hawaye bibbiyu, Mahnoor ma tana jin dik abin da yake faruwa, amma taki leƙowa, saboda bata san ganin wani tashin hankali a kan wanda take ciki a halin yanzu.

Sai da Ibrahim ya fita ya samo wasu manyan maza su biyu, sannan suka zo da kyar suka iya kama bappa. Allah sarki abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya, dan yadda yake birgima sai ya baka dariya, hannunsa dikka biyu a kansa, dan daga kai ya zuba ruwan, tamkar zai ɗaye fatar kansa saboda sosawa, ji yake yi kawai ya yi ta dirje kan nasa a ƙasa ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji.

A yanzu ma bai san su wanenen a kansa ba, wlh kuka yake yi sosai, hawaye dik ta wanke mashi fuska. Mairo dik tinaninta yana da wani ciwo ne da bata sani ba.

ArÉ—o da ya gane menene sai ya ce da Ibrahim a kawo mashi É—anyar kashin shanu, dan shi ne maganinsa.

Jin Arɗo ya ce a kawo ɗanyar kashin shanu yasa Ibrahim ya fahimci karatun, ransa ne ya yi mummunar ɓaci, a kule ya ce. "Waye ya saka mashi karara kenan?". Ya yi maganar yana kallon Mairo, da yake akwai zuciya da saurin fushi sai nan take idanunsa suka yi ja ransa ya ɓaci.

Mairo da hawaye sun gama wanke mata fuska ne ta fara girgiza mashi kai tana faÉ—in wlh ba ita bace kuma bata san wacece bace. Ibrahim zai sake yin magana ArÉ—o ya umarcesa da ya yi sauri ya kawo É—ayar kashin shanun nan da wuri kada su rasa bappan.

A fusace ya fice daga gidan, a ransa ya kudurta babu abin da zai hana shi cin uban koma wanene ya saka wa bappa wannan abin........... Lallai Nenne zata sha duka a hannun yayanta kenan.

Da kyar suka kama bappa suka kaisa É—aki, a saman batarman amarya Mairo suka kwantar da shi.
Sanya waɗan nan maza biyun Arɗo ya yi da su danne mashi bappan da karfi, haka suka danne hannunsa da ƙafafunsa, Allah sarki yana jin kaikayi sosai hakan yasa da suka danne shi babu halin sosawa sai ya fara zaro idanunsa da suke jajir kamar wuta yana wani irin miƙa yana san kwace kansa, azaba yake ji Allah sarki, wlh dik wanda ya gansa a wannan hali sai ya tausaya mashi, abin akwai azaba ne sosai.

Wlh ko leƙowa Nenne taki yi, tamkar bata a cikin gidan. Suna ɗauke bappa izuwa cikin ɗaki ta samu hanya ta fita gidan a miliyan sai gidan Arɗo. Ta je gwaggonta ta ɓoyeta a cikin ɗakin, wato waɗan nan biyun anyi mugaye, kamar waɗan da suka fita daga tsatson Black Tiger............🤔

Da kyar su ArÉ—o suka iya ceto bappa ta hanyar yi mashi wanka da É—anyar kashin shanu, suna tsaka da yin wannan aikin ne tamkar saukar aradu suka fara jin kukan jirage a sararin samaniya.

Ai a miliyan Mahnoor ta fito waje daga cikin É—akinta, dan tasan waÉ—an nan jirage su suka rabata da mijinta, ta manta ma bata goge hawayen fuskarta ba, dama Mahreen ma ta tashi daga barci tin lokacin da bappa yake ihu, Mahnoor É—in ce ta hanata fita, so yanzu sai suka fita waje da gudu a tare.

Tamkar dai a baya yadda suka zo suka ɗauki Jaish, haka yanzu ma jirage ta sama motoci ta ƙasa, kuma a kusa da kofar gidan bappa suka faka motocin.

Waje Mahnoor da Mahreen suka fita, yau Mahnoor babu tsoro, dan zuciyarta mijinta kawai yake san gani, burinta ta sanya idanunta a kansa, shiyasa bata tsorata da jirage da motocin ba.

GabaÉ—aya mutanen kauyen a wannan karon ma fitowa waje suka yi dan ganin su wanene suka zo. A lokacin su ArÉ—o sun kammala shafe bappa da kashin, hakan yasa bappa ya nitsu tsit kamar wanda ya yi barci, tabarman Mairo kam ya lalace da kashin shanu.

Fitowa ArÉ—o suka yi, dan suma su je suga su wenene?. Kowa a kauyen sai rarraba idanu suke yi, yau shine ganin motonci na biyu a kauyen.

Manya manyan bodyguards ne suka fara fitowa daga cikin motocin, da yake dikkansu larabawa ne, sai su Mahreen suka yi masu kallon mutane guda, wai suna kama sosai.

GabaÉ—aya yan kauyen sai da suka ja da baya lokacin da bodyguards É—in nan suka bayyana, wasu jiga jigai da su.

BubbuÉ—e kofofin motocin suka yi gabaÉ—aya. A hankali uncle Jahiz ya fara fitowa daga cikin motar. Ya zo ya tsaya a kusa da É—aya daga cikin motocin, yau yana shirye cikin Arabs dressing, har da alkyabbarsa ya É—aura saman shigar tasa, ya fito a balarabensa sak.

Like wow unexpected momma ta fito daga cikin É—aya daga cikin motocin wanda uncle Jahiz yake tsaye a kusa da shi, tana fitowa guyson ya biyo bayanta, da kallo É—aya zaka yi mashi in dai kasan shi ka gane bashi da cikakken lafiya sosai.

Mahnoor tana É—aura idnaunta a kan momma da guyson nan take ta gane dik yadda aka yi Æ´an uwan Jaish ne, dan jini ba wasa ba, ita kuwa Mahreen da hankali bai gama isarta ba kallon Jaish ta yi wa guyson, kun san na gaya maku guyson yana da tsawo sosai, amma bai kai Jaish ba, kuma Jaish ya fisa cika gaskiya, amma ita kallon Hamma Jaish ta yi mashi.

Kowa ya zaro idanu waje yana kallon waÉ—an nan kyawawan taurarin, barema guyson da kusan rabin Æ´an kauyen suke yi mashi kallon Jaish, har sun fara manta yadda Jaish yake. Dik hankalin kowa a tashe, wasu sai kuskus suke yi suna gulmar bappa, wai bappa ne dik ya fara É—auko masu wannan annoba dangin aljanun ya kawo masu kauye, da bai É—auko Jaish ba ai da hankalinsu a kwance, yanzu ga shi sai zirya motoci suke yi a kauyensu suna É—aga masu hankali.

Wasu kuwa addu'a suke yi Allah yasa bappa aka zo kashewa tin da shi bashi da aiki sai yayuɓo mutane ya kawosu gidansa ya ajiye. Sai mugun fata suke yi mashi.

Jama'a ku tafawa mata......... Meya kawo Momma Jimeta? Mu koma baya mu leƙa KINGDOM OF POWER mu ji ta ya aka yi suka zo kafin mu dawo muji dame suke tafe.

Jama'a nace ku kara tafawa mata........

Bayan dawowar Jaish da kwana biyu, sai da suka barshi ya huta, sannan ne momma ta buƙaci da tana san sanin in da ya afka tsawon wannan watanni da ba'a gansa ba, King ne ya ce mata e gaskiya hakan kam yakamata, yakamata su san in da ya je.

A lokacin su commander Zafar sun shirya tsab zasu tafi yaki, ba yadda Aunty MieMie bata yi ba a kan King ya dakatar da wannan yakin su yi tsastsauran bincike tukun nan, amma ina ransa a ɓace, zuciyarsa taki sauƙa, hankalinsa baya jikinsa, ya ce babu ja da baya, umarni yake badawa ba shawara ba, kada ya sake jin bakinta a cikin wannan magana, hakan yasa ta ja gefe ta yi shiru, amma wa King kawai, ta nuna mashi ta bar zancen, amma bata bari ba, ta dai umarci su commander Zafar a kan ta basu nan da kwana biyu dik in da Zunaira take su nemota, idan ba haka ba kada su dawo kingdom ɗin nan, shi ne abin da ya faru.

A tinanin king umarninsa suka tafi aiwatarwa, amma neman Zunaira suka tafi, saboda dama dan Zunaira za'a je yakin ai, idan aka dawo da ita ba shikenana ba zance ya mutu, idan kun lura ita Aunty MieMie bata san yaki sam sai in ya zama dole, dik da taurin zuciyarta akwai imani da tausayi a cikinsa, tasan yaki yana haifar da matsaloli sosai, waÉ—an da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu.

Guyson ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga, sai dai baya magana, dik yadda suka so ɓoyewa Momma rashin lafiyarsa sai da ta gane, dan ta rasa sukuninta, ta shiga damuwa, hakan yasa King ya sanar da ita cikin nitsuwa ta hanyar da yasan ba zata ji raɗaɗi sosai ba.

Aikuwa faɗa mata ɗin ya yi amfani, ta buƙaci a dawo mata da shi gida ta yi jinyarsa, a turo nurse su zo su rinƙa kula da shi a gabanta tun da ita babu halin ta je hospital. Hakan aka yi, dan dik abin da zai faranta mata shi King yake yi a yanzu, baya san ganinta a cikin damuwa, dan ma dawowar Jaish ya rage mata abin da take ji a ranta sosai.

Jinyar guyson da ta fara yi ne tana faÉ—a mashi kalmomi masu karfi dan nuna tawakkali da godiya ga Allah, sai Allah ya taimaketa ta fara shawo kansa, kunga kuwa faÉ—a mata rashin lafiyarsa ya yi amfani, tin da ga shi ta dalilinta ya É—an samu lafiya har yana iya yin magana.

A daren rana na huɗu da dawowa Jaish Tunisia, dama ya yi kwana ɗaya a Nigeria, so a rana ta huɗu da dawowarsa momma ta buƙaci da su zauna su yi magana a kan daga ina su uncle Jahiz suka ɗaukosa, dik ta damu tana san jin hakan, kun san mufa mata batu na gaskiya muna da sanin yakamata ato, taga yakamata ta san daga ina yaronta ya fito ne?.

Uncle Jahiz ne ya fayyace masu komai yadda ya kasance da yadda Ramish ya gano in da yake har suka je suka É—aukosa. Dik cikin parlourn wanda kowa da kowa yana cikin except Jawad da Chuchu da har yanzu Chuchu jikinta bai warware ba, suna hospital, sai kuka take yi taki dainawa, ita dai a dawo mata da Autarta.

A gabaÉ—aya parlourn nan babu wanda ya gane aibi a cikin abinda su uncle Jahiz suka aikata, kowa sai godiya yake yi wa Allah, sai murna suke yi, shi ma Jaish yana zaune kusa da Momma, sai satar kallonsa Fanan take yi, tana san yi mashi sannu da dawowa, amma tana tsoronsa sosai.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Amma Jahiz wani irin abu ne wannan zaku je ku É—auke shi ba tare da kun nemi waÉ—an da suka rikesa kun yi masu godiya ba?".

Muryar momma ce ta dakatar da dikka wannan godiya da murna da suke yi É—in.

Mummyn Chuchu ce ta amsa da. "Gaskiya nima naga abin bai kyautu ba sam".
Chapter 47 · 0% Book details