Sashe 58
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Ronnie ya ji wani irin faɗuwar baba, a take tsikar jikinsa ta mimmiƙe lokacin da ya ga walwalin fararen idanunta ta wurga mashi kallo da su, ga shi ta cikin mirror ne, abin sai da ya ɗan razana zuciyarsa.
"Ronnie yaushe ka shigo?". Ta jefa mashi tambayar ta zage tana ta ƙoƙari dole sai ta kama gashinta mai bala'in tsantsin da yaki kamuwar nan ta ɗaure, gashin yaki kamuwa ta samu ta ɗaure shi, har wani nishi take yi wajen ƙoƙarin kama shi, sai dariya Floris take yi mata tana tsokanarta da raguwa bata iya komai ba.
Jin ta ambaci Ronnie yasa Floris ta yi saurin kai kallonta a wajen kofar, yana tsaye cikin kayan barcinsa sak irin na jikinsu ita da Floris, sai dai na shi ash colar ne, na Sweetie milk color, na Floris black color, ya harÉ—e hannnu a kirji yana kallansu.
"Beb yaushe ka shigo bamu sani ba?". Floris ta jefa mashi tambaya. Yana ta kallan kayan jikin Sweetie bai amsa masu ba, sosai Floris ta ji wani abin ya soki ranta, kamar ta ji zafin kallon Sweetie da yake yi har ya kasa iya amsa mata maganarta.
Abin ya sosa mata zuciya, sai ta miƙe da nufin ta fita ta basu waje, tin da ta kalli yanzu shi idan yana tare da Sweetie baya kallan kowa bare har ya gansa da daraja!!.
"Floris ina zaki je?". SweetiE ta faÉ—a itama kallanta a kan Ronnie, ita tana kallan face É—insa shi kuma yana kallan zubin kyakkyawar halittarta mai tafiya da imanin namiji mai lafiya.
Rai a ɓace a ɗan kule ta ce. "In da ya dace da ni zan je Sweetie".
Gashin kanta ya ki ɗauruwa ne ta sakesa ya watse a gadan bayanta dan ta gaji, sai faman haki take yi ta ce. "To ki dawo da wuri"................... Sweetie duniya, sarai tasan ran Floris ya ɓaci ne, amma da yake ta san ta kan tsiya dik yadda suka zo mata a haka take binsu, wasa wasa ita ma ta iya tsiya sosai, sai ta nuna bata san ma Floris ta yi fushi ba, ta nuna abin bai dameta ba har da cewa ta dawo da wuri.
Kin amsa mata Floris ta yi, ranta ne ma ya kara ɓaci, wato ko hakuri ba zasu bata ba, sai ma suka nuna kamar basu san tana ɓacin rai ba, lallai dole ta san matakin da zata ɗauka a kansu, ba zata zuba masu idanu su rinƙa kunsa mata bakinciki ba.
Da ta zo wucewa a kofar É—akin, matsa mata hanya Ronnie ya yi, kallansa a kan Sweetie ya ce. "Dama Angela tana nemanki".
Ya ilahi, wani irin bakin bargon bakinciki ne ya kara lulluɓe zuciyar Floris, wato har da Ronnie ma faɗi yake ta je bai wani damu da ranta a ɓace ba ko? Lallai ma sun walaƙantata, dole ta nemi hanyar ɗaukar mataki.
Bata bashi amsa ba shima tasa kai ta fice da sauri, tana fita ta rushe da kuka mai taɓa zuciya, da gudu ta biyo ta saman escletor, bata ma jira ya yi kasa da ita ba ta taka stairs ɗin da gudu ta sauko ƙasa.
A babban parlour ta wuce master Devil dake zaune saman sofa tana jiran Jack akwai aikin da Black Tiger ya basu, so yana zaune yana jiransa ta zo da gudu tana kuka ta wuce, da kallo ya bita yana mamakin meyasakata kuka kuma? Ya dai san ita ce sanyin idaniyar Ronnie, in ka taɓata to ka taɓo karar kwanarka, amma yau take kuka da hawayenta kuma Ronnie yana cikin gidan nan? Anya lafiya kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.
Ɗayar bakar zuciyarsa ce ta amsa mashi da kila Ronnie ɗin ne ya bakanta mata rai, kila da shi suka samu saɓani, in kuwa haka ne kana da damar shiga jikinta ko dan fansar da kake san ɗauka a kan Ronnie. Jinjina kai ya yi tamkar yana magana da mutum mai rai, sai ya ji ya yi na'am da wannan shawara da zuciyar tasa ta bashi, a hankali cikin zuciyarsa ya furta................ "Now is my time Ronnie, wait for me am coming".
Shi kuwa Ronnie tana fita ya tako izuwa in da Sweetie take, hannu yasa a nitse ya fara tayata tattara gashin nata ta ɗaure, yana jin wani love period a tattare da shi mai matuƙar nishaɗantarwa.
"Ronnie meyasa ka kori Floris?". Sweetie ta jefa mashi tambaya.
"Very very sharp brain, kai Sweetie ke karshe ce, yanzu waye ya faÉ—a maki na koreta ne da gangan?". Ya kai karshen maganar tare da tsai da idanunsa a kan É—an bakinta ta cikin mirror dake gabansu.
Kunga yadda suke tsaye a gaban mirror nan suke kallan kansu, haka Black Tiger yake tsaye a gaban nasa mirrorn yake kallan dik abin da yake faruwa a gabaÉ—aya faÉ—in birnin Black world.
"Ai daga ganin yadda ka yi mata na fahimci da gangan ka yi hakan dan ta fita, akwai wani abin special da zaka faÉ—a mun baka san ta ji ne?". Cewar Sweetie.
Jinjina mata kai ya yi, tamkar wanda yake a cikin maye, rage tsawonsa kaɗan ya yi, a dai'dai kunnenta ya saita ɗan bakinsa.................. "So special sosai ma zan faɗa maki, haƙiƙa ke yar baiwar ce Sweetie, Allah ya yi maki baiwar kaifin ƙwaƙwalwa ga iya magana mai daɗi, ga fahimtar halin da mutum yake a cikin cikin ƙanƙanin lokaci, kin cancanci a yaba maki, ba zan taɓa bari wannan kaifin ƙwaƙwalwa taki ta salwanta a banza ba, tabbas idan kika yi karatu jama'a da dama zasu ci riba a tare da ke, al'umma guda zasu karu da iliminki".
Tin da ya fara magana idanunta a kanta tana jin tamkar gizo ko mafarki take yi, hakan yasa ta É—an zaro mashi ido ta cikin mirror, ba zai iya ganin cikin kwanciyar idanunta ba sai ya lumshe nasa yana cigaba da jawabi.
Sai da ya kai aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin matsuwa da jin me yake nufi ta ce.
"Ronnie to me kake nufi da kalamanka?".
"Zan faÉ—a maki wani lokaci, yanzu dai ba shi ne a gaba ba".
"Menene a gaba to?". A matse da san jin komai dallah dallah ta jefa mashi tambayar.
Kara yin kasa da kansa ya yi, ya manna ɗan bakinsa da kunnenta, ya yi ƙasa da murya matuƙa yadda sai shi da yake furta maganar da kuma ita da ake yi a kunnenta ne kawai zasu iya jin me suke ciki, with his full confidence ya fara magana kamar haka.
"Ina yi maki albishir da ina san shiga addininki dan kuwa shi ne na gaskiya na yarda d.........."
Katse shi ta yi ta hanyar juyowa da karfi garesa, she was so surprised over, she didn't expect that wonderful word from him, she can't forget this days in her life koma da wasa ya yi mata!.
Zata yi ihun ban mamaki ya yi sauri rufe mata baki, ƙasa sosai ya kara yi da murya. "Kada ki kuskura ki yi hakan, ina san ki sani dik abin da muke yi yaya yana kallanmu, kuma yana jinmu, raɗa a kunne ne kawai ba zai ji me na faɗa ba, dan haka ki kiyaye, ki yi shiru ki saurareni".
Wani irin tsuma ta ji jikinta yana yi, tamkar ana mincininta, burinta kawai ta daka tsalle ta yi murnar ta yi nasara, amma ya zata yi? Dole ta yi shiru ta danne kada murna ya koma ciki idan Black Tiger ya jiyosu, har wani ciza laɓɓanta ta yi saboda irin tsananin farincikin da yake ratsa mata zuciya, tamkar mai jin sanyi haka take jin jikinta yana yi mata.
Sarai ya lura da tsananin farincikin da ta shiga, hakan ba karamun kara mashi kwarin gwiwa ya yi ba, ya yi farinciki matuƙa shi ma, kuma tin da ya yardanwa kansa zai shiga addinin Musulunci ya fara jin kansa a wani irin ni'ima, nishaɗi da farinciki na ban mamaki, yana jinsa tamkar ba shi ba, wani irin sakayau yake jin jikinsa yadda kuka san wanda ya kwashi shekaru yana ɗauke da wani kungurmin dutse mai nauyin gaske sai yau aka sauke mashi shi, ya ji komai tana yi mashi daɗi, shi kaɗai idan ya zauna sai ya tsinci kansa da sakin murmushi, wannan ne ya kara bashi kwarin gwiwa ya yarda da babu abin bauta da gaskiya sai Allah, lallai suratul iklas gaskiya ce, lallai ne Allah shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya. My best part again!! Lallai ne Allah shi ne abin bauta na gaskiya, ka bisa ka more, akasin haka ka ɗanɗani madarar azaba!!.
Cigaba ya yi da cewa. "Zan karɓi addininki saboda na yarda shi ne na gaskiya, na yarda Allah shi ne abin bauta ba Yesu ba! Sannan na yarda da dik abin da kika faɗa mun hakan ne, sai dai ina neman wata alfarma guda ɗaya a gareki".
A hanzarce ta yi yunkurin yi mashi magana, hannunsa na saman bakinta tin da ya rufe mata É—azun, tana san amsa mashi da wace alfarma ce wannan, sai ya yi saurin kara rufe mata baki da kyau.
"Kada ki damu, ba sai kin amsa mun ba, nasan so kike ki ji wace alfarma ce, ko baki amsa ba zan sanar dake, ni dai ki yi shiru ki saurareni kada ki yi wata magana".
Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sai kara tsuma jikinta yake yi, tana jin tamkar ta rumgume shi da karfi saboda daÉ—i, tabbas idan Ronnie ya musulunta zasu iya cin karfin wannan yakin, shi kaÉ—ai kusan kaso 40 ne cikin É—ari na wannan fafutukar.
"Wannan alfarma ba komai bace face ki taimaka mun mu canza yayana, mu yi ƙoƙari ya shiga addinin Musulunci, tabbas yayana yana da zuciya mai kyau, kema idan kika ji tarihin tasowarsa zaki yarda da hakan, yana da san taimakawa mutane, sai dai yana da wata ɗabi'a ɗaya wadda ita ta haifar mashi da bakar zuciya a cikin kirjinsa!!".