← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 242

Sashe 35

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin hararar da Jawad ya wurga mata ne yasa Fanan ta yi gaggawar sakin hannun nata tana É—an sunkuyar da kai.

Abdussalam yana ganinsu dik abin da suke yi, dariya suka so É—an bashi, wato dai Jawad rashin kunyarsa a fili zai nuna? Abdussalam ya tambayi kansa yana kunshe murmushi.

Ita kuwa Fanan kasa ta É—an yi da kai tare da cewa. "Yah Jawad zamu koma ciki ne fa!".

Tamkar bai ji me ta ce ba ya yi shiru yana kallon Chuchu dake tsaye kusa da shi.

A karo na biyu Fanan ta sake maimaita mashi abin da ta faÉ—a É—azun.

Kallo mai kama da harara ya wurga mata, cikin sanyin murya ya ce. "Ke kika kawo mun ita ne dama?".

Kamar zata gyaÉ—a mashi kai alamar e, saboda ita ta kawota kam, amma sai taga rashin dacewar ta yi mashi hakan tun da yayanta ne, kuma tana tsoron ya hukuntata, dan haka sai ta girgiza mashi kai alamar a'a ba ita ta kawo ta ba.

Hannu yasa ya nuna mata hanya. "Jeki zan dawo da ita da kaina".........Ya faÉ—a idanunsa a kan Chuchu da ta sunkuyar da kai tamkar bata a wajen, tinanin Auta ce kawai a cikin kwakwalwarta.

"Kai malam kamar ya zaka mayar da ita da kanka? Ban gane ba?"...........Cewar Abdussalam, ya yi maganar cike da tsiya da iyashege.

"E zan mayar da ita time da na yi ra'ayi"....... With his full confidence Jawad ya mayar mashi da amsa.

"Kai ka kawota ne daman? Ji mun wani karfin hali, kinga Fanan kama hannunta ku tafi hai"........... Cewar Abdussalam, yana magana yana É—aure fuska irin shi fa da gaske yake yi.

Gum kamar gunki Fanan ta tsaya ta kasa kama hannun Chuchu saboda tana tsoro, jama'a dik sun watse sun barsu tsaye a wajen.

"Fanan kama hannunta na ce ku tafi ko.........".......... Cewar Abdussalam. Bai ƙarisa maganar ba ya dakata saboda wani irin harara da Jawad ya wurga mashi.

Murmushi Abdussalam ya É—an saki tare da riko hannun Fanan yana faÉ—in. "Zo mu tafi hai sister, kada ya fara saka mana duka".

Ba musu ta bishi suka tafi, wajen ya rage daga Jawad sai Chuchun.

A hankali ya kai hannunsa ya riko hannayenta, kamar mai raÉ—a ya ce. "Menene kuma?".

Kamar jira take yi ya yi mata magana ta fara kuka, nan take hawaye suka fara Æ´ar tsere a saman face É—inta.

A É—an rikice ya ce. "Jannat lafiya kuwa?".

Da É—an daga murya ta ce. "Yah Jawad Auta, ban ga Auta ba, tun da yamma nike nemanta ban ganta ba, tun da rana rabona da ita, ina kiran numberta baya shiga, ya zan yi da rai'na?".

Ɗan jawota jikinsa ya yi, shi kansa yana cikin damuwar rashin Autar nan, amma bai taɓa kawo mummunar abu a ransa ba, ya fi zaton tana wajen bakin Dubai tun da ta yi sabo da su sosai.

"Auta tana nan a ciki gida, muje zuwa da safe da kai'na zan É—auko maki ita".

Bata san yin ja in ja da shi ne kawai yasa ta yarda da abin da ya ce, ta kuma miƙa wuya a garesa, cak ya ɗauketa suka fito daga cikin hall ɗin.

Bai zame ko'ina da ita ba sai cikin bedroom É—insa, shi tun ba'a kai mashi ita ba ya kaiwa kansa ita.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Momma tana sallame sallah ko numfashin guyson bai bari ta ja ba ya yi sauri wurga mata tambayar ina Autarsa?

Wani irin dum dum Momma ta ji kirjinta ya buga, sai dai bata yi wani mummunar tunani ba, cikin nutswa ta ce.

"Ina jin tana tare da Jannat a wajen dinner.........."

Tun bata dasa aya a maganar ba ya tari numfashinta da cewa. "Naje wajen bata nan, Yah Jawad ma ya ce rabonsu da ita tun da rana.........."

Bai ƙarisa maganar ba momma ta zabura kamar wadda aka kwalawa guduma a kai ta miƙe tsaye, dan ita ma rabonta da Auta tun da rana, dik tinaninta tana a tare da su Chuchu ne yasa bata wani damu ba, sai yanzu ta tuna yadda ta rinƙa ganin giftawarsu Fanan and Chuchun ba a tare da ita ba, kwata kwata bata ga giftawarta ko kaɗan ba, to ina take kenan? Ta jefawa kanta tambaya.

Shi ma guyson miƙewa tsaye ya yi yana jiran amsa. Cikin ƙanƙanin lokaci face ɗin momma ta rikiɗa izuwa na tashin hankali.

Wayarta dake gefen bed ta É—auko domin ta gwada kiran number Auta.

"Momma don't west your time, her number isn't going now, before i called her more than 30 times she didn't pick the call, yanzu kuma the number was not going, switch off".

Momma bata daka ta tashi ba sai da ta gwada kiran number, a kashe suka sanar da ita, hankalinta ne ya kara tashi sosai.

A hanzarce ta nufi kofar fita, kamar ta mance da guyson a tsaye a wajen. Ganin haka yasa ya yi saurin rufa mata baya.

Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King. A lokacin har barci ta fara ɗaukarsa, jin motsin taɓa kofa yasa ya farka.

Ganin sune yasa ya yi saurin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin. Wajen switch momma ta nufa, dama iya lamp ne kunne a ɗakin, so sai ya kunna wutar gabaɗaya.

King he was very shocked na ganinsu a tare da kuma ganin yadda suka shigo momma a hargitse, da Momma ita kaÉ—ai ce ba zai ji komai ba, amma a tare da guyson sai ya zaci ba lafiya ba, dik tinaninsa ta ta'allaka a kan ciwon guyson É—in ne ya hanasu rintsawa.

A ƙage da son jin cikakken bayanin meyake faruwa yake binsu da kallo. Ita ma Momma kallonsa take yi ta rasa ta ina zata fara, dik yadda take ji a ranta take kuma tsananin tsorace a kan me ya sami yarta, hankalinta yake tashe ganin face ɗin King yasa ta ji nata tashin hankalin wasa ne a kan wanda shi zai shiga idan ya ji me ya kawosu.

Guyson ne ya katse masu kallon juna da suke yi ta hanyar ƙarisawa gaban bed ɗin, tamkar zai rushe da kuka ya ce. "Daddy Auta bata nan, mun duba ko'ina amma bamu gan.........."

Wani irin birki ya ci tare da haɗiye sauran maganganun a cikinsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face idanu da King ya zaro mashi tare da zabura ya yaye bargon dake jikinsa. Ai bai san time da ya sauko ƙasa daga saman bed ɗin ba.

Idanunsa a kan momma ya ce. "Da gaske ne abin da Omar ya faÉ—a?".

Kai kawai ta iya jinjina mashi ta kasa yin magana.

"To ina ta je? Kun duba dik part's na cikin gidan nan?".

Guyson ne ya tabbatar mashi da tabbas ya duba ko'ina bata ciki.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da King ya furta kafin ya nufi waje da sauri.

Bayansa suka bi, a parlour ya tsaya tare da harÉ—e hannayensa saman kirjinsa, tunani ya fara yi a kan ina Auta ta tafi? In dai bata cikin kingdom É—in nan to tabbas hanune ya É—auketa, saboda ba ta yadda za'ayi wata halitta ta iya ketare gates É—in nan gabaÉ—aya ta fita ba tare da saninsa ba! To ina take kenan?. Ya jefawa kansa tambayar da bai san amsarta ba. Zuciyarsa ta cika tab da tunani haÉ—e da ruÉ—ani mai tarin yawa.

A nan momma ta isko shi, cike da tashin hankali ta ce. "Yanzu me abin yi?".

Guyson dake tsaye a kusa da momma idanunsa sun ciko da kwallah King ya É—aura idanunsa a kansa. "ÆŠauko mun wayata Omar"........... Ya faÉ—a tamkar wanda yake koyan yin magana, a hankali.

Cikin zafa guyson ya juya ya koma cikin master room É—in. Kallon juna King da momma kawai suke yi babu wanda ya iya furtawa É—an uwansa word.

A haka guyson ya dawo ya samesu, wayar ya miƙawa King, da sauri ya karɓa ya shiga latsawa.

Karata ya yi a kunnensa tare da matsawa gaba kaÉ—an.
Binsa da kallo kawai suke yi momma kamar zata ɗaura hannu bisa kai ta zunduma ihu, wannan bala'i dame ta yi kama? Abin ya yi mata yawa, Jaish ya ɓace shiru shiru tsawon watanni babu shi babu labarinsa, ta danne sai dai ta yi kuka a ɓoye, a fili tana nuna kamar bata damu ba, ta jajirce wajen shanye madarar bakincikin, yanzu kuma ace Auta ta sake ɓacewa basu san ina take ba? Ai gara mata Jaish namiji ne kuma babba ne, Auta fa? Mace kuma yarinyar da ko 14 years bata cika ba, dole hankula su ɗugunzuma su tashi.

"Abbas ka bincika mun Zunaira tana ɓangarenka ne!"........... Cewar King da ya kara waya a kunne.

Da sauri su momma suka kara nitsuwa haÉ—e da kara tsaresa da idanu da kyau.

Uncle Abbas da yake zaune saman dadduma yana gabatar da nafilfilin dare ne ya yi saurin miƙewa tsaye, dama ya idar yana addu'oi ne.

Mammie tana kwance saman bed tana barcin asara, kun san ita fa yanzu ba sallah take yi ba, sai shirka.

Uncle Abbas tin ba'a gaya mashi ta ɓata ba ya shiga tashin hankali, yanzu ai suna nemanta ne, a tinanin kowannensu tana cikin gidan, sai da King ya kira kowannensu har uncle Taheer ya ce su dubata, sai a sannan ne idanunsu ya fara rena fata, dan dik in da suke tinanin tana wajen babu ita, a yanzu kwata kwata basu sa a ransu kasheta ma aka yi ba, tun da ba'a ga gawarta ba, sun fi sawa a ransu saceta aka yi.

Shi King kam ma kai tsaye King Al-Mustapah ya É—aurawa zargin yin hakan, dan in baku manta ba ya kawo masu jiyara yau da rana, kuma shi abokin gaba ne, so dole a zargesa.

King yana zargin shi ya saceta dan su cinwa wani buri nasu a kan kingdom of power.

Shi kuma uncle Abbas yana zargin Queen Zarina ce ta turo mutanenta suka saje da Æ´an biki suka shigo suka É—auke Auta, kowa da abin da yake zargi yake kuma hasashe, sai dai babu wanda ya yi hasashen ta mutu mai gabaÉ—aya ta bar duniya.
Chapter 35 · 0% Book details