← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 242

Sashe 212

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya ɗan yi har sai da ta kai bakin door zata fita, gentle ya ce. "I need 10 mins from your time". Ya yi maganar tare da juyo da kallonsa a kanta. Juyowa ita ma ta yi, ɗan tsuke face ta yi. "Yah Ramish small chop zan je in ci fa, am feeling hungry............". A karshen maganar tata da shagwaɓa ta ƙarisa. Sai dai bata iya kai karshen maganar gabaɗaya ba ta zubawa kayan jikinsa idanu, kai Ramish duniya ne, karshe ne guy ɗin wajen iya dressing, haƙiƙa sleeping dress suna mubaya'a a jikinsa yadda yakamata, kamar ba shi ba, ya yi masifar kyau cikin kayan, wando ce zuwa gwiwarsa da rigar da bata da botira sai siririn maɗauri a gaban rigar wanda idan ya daure ma faffaɗar kirjinsa zata kasance a buɗe, siffar bathrobe, to amma shi bai ma ɗaure igiyar ba, ya ji daɗi buɗe wide chest ɗin nasa da kyau, abin dake tafiya da imaninta kenan. Shima kuma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin dirin da Allah ya yi mata, sai ya ja dogon numfashi kafin ya ce.

"Shin an hanaki ci a nan ne?". Kai ta girgiza kamar wata yarinya ƙanƙanuwa. Kallan gefen ido ya wurga mata kafin ya ce. "Zo ki ajiye shi in yi maki wasu tambayoyi, idan na kammala sai ki je ki ci ɗin"..... Jinjina mashi kai alamar to ta yi kafin ta dawo cikin bedroom ɗin. A saman bedside drawer ta zauna bayan ta ajiye small chop ɗinta a kusa da cappuccinonsa.

"Zo ki zauna a nan". Ya faɗa yana nuna mata kusa da shi. Kamar ba zata je wajen ba, sai kuma ta ga ai bincike yake yi, kila wani abin zai nuna mata, a gefensa ta zauna, wani irin shakar kamshin perfume ɗin jikinsa ta yi ta ɗan lumshe idanu, shi ma dai shaƙar nata ƙamshin ya yi ya lumshe idanu.

"Aesh shin kin san ɗaya daga cikin waɗan nan mutanen?". Ya yi maganar tare da nuna mata hotunan dake kan screen na laptop ɗin gabansa. Kai kallonta a kansu ta yi, shiru ta zuba masu idanu tana kallonsu, tabbas ta taɓa kallonsu dikkansu, sai dai ta manta a ina ne, ɗaya na tsakiyar nan tabbas akwai ranar da ta ga idanunsa kurkusa da ita, to amma a ina ne? Shiru ta nausa cikin tinaninta ko Allah zai sa ta iya tina in da ta taɓa ganinsu, sai dai kuma ina ta gagara tinawa. Jin ta yi shiru ne yasa ya juyo da kallansa a kanta. "Ko dai har yanzu baki dawo dai'dai bane? Har yanzu akwai tsoro a ranki ko?". Ya jefa mata tambaya.
Ɗago da kallonta a kansa ta yi, suna haɗa ido bata san time da murmushi ya kubce mata ba, haka kawai ta tsinci kanta a cikin farinciki da kwarin gwiwar jin zata iya yin komai a kansa........YAU BA BATUN AMANAR SHARIFAT KENAN, WAI ZATA IYA YIN KOMAI A KANSA KAI LEESHARH DUNIYA.😅

Zubawa smile ɗin nata idanu ya yi yana kallanta, hannu tasa ta rufe fuska tana cigaba da murmusawa.......... Matsar da face ɗinsa dab da ita ya yi, ƙasa ƙasa ya ce. "Murmushi yana yi maki kyau, amma yanzu dai murmushin me kike yi daga tambaya?". Kai ta girgiza mashi alamar babu komai. "To faɗa mun shin kin sansu ne?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta sansu.
Ajiyar zuciya ya sauke. "To faɗa mun a in da kika sansu". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya riƙo hannayenta, ya zamesu daga face ɗinta. Dakatawa da yin murmushi ta yi tare da kura masu idanu, take wannan dattijuwa ta faɗo mata a cikin ranta, ɗan limshe idanunta ta yi tana tina abubuwan da ta gani a jikin wannan dattijuwa. Nan take ƙwaƙwalwarta ya tuna mata wani irin zanen tattoo na harafin B a wuyarta wanda kuma irinsa ne a wuyar Bilal kuma irinsa ne a wuyar dik mutanen dake jikin wannan hoto, hakan na nufin dik team nasu ɗaya kenan.

Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali. "Yah Ramish ba zan iya ce maka ga in da na sansu ba, amma dai ka sani koma a ina ne to a gidan Abbie ne, dan dai kaga bana fita, tin da na karɓi wannan contract ɗin na shiga gidanku to ai kaga bama fita, dik yadda aka yi dik suna gidan Abbie, ka bincika cikin dayawan masu aikin dake gidan, har hawa na sama da kasa dik ka bincika suna ciki, kai har cikin securitys ɗin nan ma dikka". Tin da ta fara magana yake bin ɗan bakinta da kallo, babu abin da yake tsaye a ransa irin kissing ɗinta da ya yi ɗazun.

"Zaki iya bani wata alama da zan iya ganesu da shi?". Ya yi maganar kamar ba shi ya yi ta ba. Shiru ta ɗan yi kamar mai nazari, sai kuma ta ce. "Zanen wannan B dake wuyarsu, dik ƴan cikin team ɗin suna da wannan zane..........". Bata karisar ba ta yi shiru sakamakon ta tuna taga wani zanen scorpion a waist na tsohuwar can ta baya sama da mazaunanta kenan, dan fighter wears dake jikinta bai rufe mata ƙugu ba. Shiru ya zuba mata idanu a lokacin da ta dakata tana tinani.

"Yah Ramish ba iya zanen B a wuya ba, suna da wani tambari na kunama a waist ɗinsu, tabbas na gani a wajen........" Kasa ƙarisa a wajen waye ta gani, take ta ji ta shiga ruɗani, zazzare eyesball ɗinta ta yi tana kallansa.

Dik abin da suke tattaunawa a kunnen wannan dattijuwa suke yinsa, saboda ta sanya masu abin jin magana a ɗakin kasan bed ɗin Ramish ba tare da Ramish ɗin ya sani ba, dan haka dik maganganunsu tana daga kwance bisa bed ɗinta, ta maƙala bluetooth a kunne tana jinsu, hannunta rike da wayarta tana rubutawa masu nikaf sako da cewa su yi saurin ɓoye dik wasu zanika dake jikinsu, dan Ramish ya san da zanen kuma zai iya zuwa a kowani lokaci dan ya yi bincike, dan haka su nemi plaster mai irin fatarsu maza maza su rufe zanen!.

"Aesh har yanzu akwai abin da baki san in sani ko?"........ Cikin gaggawa ta girgiza mashi kai tare da cewa. "A'a ina san ka san komai, dan haka zan faɗa maka komai, amma ina tsoron irin labarin da zan ji a kan babana ne! Wannan yasa zuciyata take rawa a kan in yarda da kai ko kada na yarda". Allah sarki uba, wato har yanzu ta gagara iya ciresa a ranta ta danne ta yi abin da ya dace, tana san babanta sosai, kuma mun san cewa abu ne mai matuƙar wahala ta iya daurewa a kansa.

Hannunsa yasa ya riko nata, cikin sigar tausasawa ya fara sanar da ita kada ta damu, babu wani abin da zai sami babanta, ta faɗa mashi komai a yanzu. Hawaye ne suka ciko idanunta sosai, muryarta na rawa ta ce. "Zan faɗa maka, na yi alkawarin ko zan rasa rai'na zan faɗa". Jinjina mata kai ya yi. "Ba zaki mutu ba, muna nan tare dake In Sha Allah har sai kin......" Fasa ƙarisa maganar ya yi, dama zai ce har sai ta haifa mashi babynsa, sai ya tina idan ya yi wannan magana kuma zai ja ne su canza topic na magana, a halin yanzu kuma yana cikin matsuwa da san jin abin da yake da buƙatar ji.

"Suna dayawa a gidan Abbie, nasan zaka san wata mata mai kiba dake zuwa wajen Ummie, to ita ce nan wadda ta kawoni gidanku bayan masu nikaf sun damƙa mata ni, bayan ita akwai wata mai aiki a hawa na biyu, tana nan fara tas kamar baturiya, to haƙiƙa ba farar fata bace, shiri aka shirya aka sauya mata jiki ta hanyar make up, baya ga wannan akwai ɗaya daga cikin securitys ɗinku wanda ina zargin shi, dan akwai ranar da muka ci karo da shi a harabar gida, na juya zan ce mashi sorry sai na kalli zanen B a wuyarsa, na sha mamaki sosai, amma haka na wuce ina ta kallansa dan in gane face ɗinsa, amma yana sake da face mask, tabbas suna da yawa a gidan Abbie". Ta kai karshen maganar hawaye na bin kuncinta.

Abin like some how haka Ramish ya jisa, babu abin da ya fi bashi mamaki ma shi ne har da kawar Ummie a ciki, kenan har da sa hannun Ummie? To me suke nema da shi ne? Ya samu bayani sai dai babu hujja. Shessheƙar kukanta ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, janyota jikinsa ya yi ya rungume yana kara karfafa mata gwiwa a kan kada ta damu, babu abin da zai samu babanta dan ta fallasasu.

A can kuwa wannan dattijuwa ta ji komai, dan haka sai ta bada sanarwa a team nasu da ayi gaggawar kashe Hajiya two seater yanzu, dan Leesharh tasan face ɗinta har ta fallasata ga Ramish, su kasheta kawai, saura kam su kyalesu tin da Leesharh bata san ainahin face ɗinsu ba, amma wancan bakar fata da suka sanyawa farin fata na roba dan ɓadda kama ita ma su kasheta da sauri. BABBAR MAGANA, RAMISH YANA AIKI WANNAN MATA TANA WARWARE MASHI, DIK WASU HUJOJI DA LEESHARH TA BASHI DAN ISA GARESU SAI LALATAWA WANNAN DATTIJUWA TAKE YI BA TARE DA YA SANI BA, ALLAH SARKI, YANA ZATAN YANA DA HUJOJI BAI SAN DIK BABU KOMAI BA.

Tsoro yasa Leesharh ta gagara sanar da shi wannan dattijuwa ma ba tsohuwa bace ba, yarinya ce wacce kuma ƴar team ɗin su masu nikaf ce. My people's me kuke tinanin zai faru? Uhm INTERMISSION muke, yanzu wasan zai ɗauki zafi, bari mu ga karfin ƙwaƙwalwar Ramish, shin zai iya kamasu dik da matar can ta lallata makaman da ya samu ne? Shin zai iya gane wannan dattijuwa yarinya ce? Shin zai iya rigasu isa ga hajiya two seater ne, ya wasan zai kaya, mu je zuwa, hojojin Leesharh basu kare ba, bata bashi recoding da ta yi ba da sauran maganganunta da su, amma zamu ga ya wasan zai kaya!!.

🔥🔥🔥🔥BABYN BABY🔥🔥🔥🔥
Chapter 212 · 0% Book details