← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 242

Sashe 18

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A lokacin da na shiga É—akin nasa ya gama shirya echolac É—insa domin tafiya, ni na dakatar da shi na kuma umarcesa da ya zauna mu yi magana. Bai yi mun musu ba, ya zauna.
Da kallo É—aya na yi mashi na fahimci ya sha kuka sosai, dan ga idanunsa har sun kumbura, ban nuna mashi kamar na gane yana cikin damuwa or ya sha kuka ba, na yi amfani da fifikon dake tsakaninmu na tambaye shi cikin hikima".

========================💔😥

"Rizwan meyasa kace ka barwa É—an uwanka Jannat ya aura?".

"Babu komai daddy, naga hakan shi ne yafi dacewa da ni ne!".
Ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, baya san su haɗa ido da uncle Abbas, dan baya san ya gane yana cikin tashin hankalin da ba zai iya ɗauka ba a dalilin sadaukar da soyayyar tasa da ya yi.

"Ko zaka ɓoyewa kowa Rizwan bai kamata ni ka ɓoye mun na, shin ka manta nine daddynku ne?".

Girgi kai ya yi alamar a'a bai manta ba.

"To ka gaya mun meyasa ka sadaukar da soyayyarka ga Jawad? Shin ya ce maka yana son Jannat ne?".

Girgiza kai ya sake yi a karo na biyu, kamar zai rushe da kuka ya ce.
"Babu wanda ya gaya mun Jawad yana san Jannat a baya, da idanuna naga hakan, sannan kuma Auta ta tabbatar mun da hakan, har ɗakin nan ta zo ta gaya mun cewa Jawad yana san Jannat tun tana ƙarama, ta nuna mun video da hotunansu a wayarta a lokacin da suke soyayya, na kuma kara bincikawa na tabbatar da hakan ne, a binciken nawa ne ma na gane rashin lafiyan ɗan uwana nine sila, nine na yi mashi shamaki da abar kaunarsa yasa ya faɗi ciwo........."

Yaushe Auta ta gayawa Rizwan soyayyar dake tsakanin Jawad and Chuchu baiwar Allah? Allah sarki kila tin kafin ta mutu ta gina masu soyayyarsu dan su cigaba da kasakcewa da juna, ita kuma nata soyayyan shi ne ya zama ajalinta!!.

Cikin in ina ya idasa maganar sakamakon sarkewa da muryarsa take yi, ga wasu zafafan hawayen da suka cika mashi idanu, Allah sarki har wani zazzaɓi mai karfi yake ji tana ƙoƙarin kayar da shi. Dik taurin zuciya namiji soyayya tana sanya shi ladab, to ga dai Rizwan da ruwan hawaye saboda rasa Jannat da ya yi!.

Tun da ya fara magana tsananin tausayinsa ya kara dabaibaye zuciyar uncle Abbas, yau da yana da yadda zai yi ya raba Jannat gida biyu ya bawa Æ´aÆ´an nasa da ya yi.

Matsowa ya yi ya rungumi Rizwan, zuciyarsa tana yi mashi zafi ya hau rarrashinsa a kan ya jure In Sha Allah zai samu wadda ta fi Jannat.

Murya a sarkafe ya amsa da. "Ba dai wadda ta di Jannat ba daddy, nasan ba zan samu madadinta bama bare wadda ta fita, Jannat ta dabance a zuciyata daddy, ka tayani da addu'ar Allah ya sassauta mun sonta a rai'na".

Tamkar ƙaramin yaro yake kuka yana magana. Hakika uncle Abbas ya fahimci irin tsananin sonta da Rizwan yake yi, abin ya wuci tunaninku, yanzu tsoronsa ɗaya shi ne kada wani abin ya samu first love ɗin nasa, dan a gaskiya soyayyar da Rizwan yake yi mata hakura da ita zai iya cutar da shi matuƙa.

"Babu abin da ya fi karfin Allah Rizwan, In Sha Allah zaka samu fiye da Jannat, ina tayaka addu'a a kan hakan, Allah Ubangiji ya yi maka albarka da sauyi na alkhari".

Sam soyayya ta rufe mashi ido, yaki yarda zai iya samun wadda ta fi Chuchu, gani yake yi ita ce karshe, daga karshe dai uncle Abbas shiru ya yi ya rabu da shi a mazaunin ba zai taɓa samun madadinta ba!.

Sosai Rizwan ya sha kukan da bai taɓa yin irinsa ba tun bayan rasuwar mahaifiyarsu, yau ya kara ɗanɗanar ɗaci a karo na biyu a rayuwansa, da kyar ya iya sarrafa hawayensa suka dakata da zuba, sosai zuciyar uncle Abbas ta karaya, yana ganin kamar tabbas wani abin zai faru da Rizwan, dan irin wanna kuka kai akwai tsorata mutum.

Sun ɗauki lokaci a wannan ɗaki, daga karshe uncle Abbas ya buƙaci da ya tsaya ayi ɗaurin aure da shi kafin ya tafi. Da farko yaki yarda, ya ce.

"Daddy zuciyata ba zata iya É—aukar ganin auren Jannat da É—an uwana ba, Please ka barni in tafi kawai ko zan samu sauki cikin rai'na, burina kawai in bar kasar nan".

"A'a Rizwan, babu wani abin da zai sami zuciyarka, Allah yana tare da kai, please ka tsaya ayi wannan É—aurin aure da kai".

Baya iya yi wa daddyn nasa musu, dan haka ya hakura ya tsaya É—aurin auren, shiyasa a wajen É—aurin auren kowa ya gansa a wani sake sukuku haka kamar dai wanda baya cikin hayyacinsa, dayawan mutane suna tunanin saboda rashin lafiyan É—an uwansa ne.

A lokacin da uncle Abbas ya kammala gaya masu yadda aka yi suka mallaki juna, gabaɗayansu hawaye ya gama wanke fuskokinsu, jikinsu ya yi matuƙar sanyi, sun ji sun karaya sosai, tsananin tausayin Rizwan ya mamaye duƙatansu!.

Da kyar Jawad ya iya cewa. "Daddy ina Yah Rizwan É—in yake yanzu?".

Miƙewa tsaye uncle Abbas ya yi yana faɗin. "Rizwan ya wuce Dubai tun bayan barinsa wajen ɗaurin aure, ina zargin da zazzaɓi a jikinsa ma ya tafi".

A ɗan razane Chuchu ta ce. "Zazzaɓi kuma daddy?".

Kai ya gyaÉ—a masu tare da nufar hanyar fita dan ya basu waje su ga juna a matsayin ma'aurata yanzu.

Da ido suka bishi har ya fice, kamar abin haÉ—in baki suka dawo da kallonsu a kan juna a tare, dikkansu fuska jaga jaga da hawaye.

Hawayen farinciki, na tausayin Rizwan da kuma na ƙoƙarin rabasu da akayi.

"Jannat kin ji sadaukarwar da Yah Rizwan ya yi mana ko? Kin ji ƙoƙarin da Auta ta yi a kanmu dan kada a rabamu ko? Ashe ita ta je ta gayawa Yah Rizwan muna san juma?"?

Jinjina mashi kai ta yi tana cigaba da hawaye.

"Miƙo mun wayata bari in kira Yah Rizwan ɗin, in mun gama waya sai ki kira mun Autaa cikin gida".

Allah sarki anata shagalin biki babu wanda ya lura da auta bata a gidan, baki sun yi yawa kowa zai zaci tana ɓangaren ɗan uwansa ne, sai dai kuma, kowa yasan bata rabuwa da Chuchu, so idan aka yi wa Chuchu kallon farko basa tare, aka sake ganinta na biyu basa a tare, a karo na uku dole a tambaya ina take?.

Miƙewa ta yi a hanzarce ta zagaya ta ɗayan gefen bed ɗin ta ɗauko mashi wayar tasa.

Zuwa ta yi gabansa ta miƙa mashi tana faɗin. "Ga shi nan".

A maimakon ya karɓi wayar sai ya janyo hannunta ta faɗa jikinsa. A tare suka sauke sanyayyar ajiyar zuciya. Hannunta dake rike da wayar ya riko, kamar mai raɗa ya ce.

"Wannan flowers É—in sun yi kyau sosai, wadda ta zana maki ta iya sosai".

A ɗan shagwaɓe ta amsa da. "Ai saboda kai aka yi".

Ɗan karkata kansa kaɗan ya yi tare da ɗan leƙo face ɗinta. "Anya kuwa? Dan Yah Rizwan dai aka yi, kuma nasan sai da aka kai ruwa rana dake kafin ki aminta ayi shi ko?".

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e.

"Da baki bari anyi maki ba da kin yi mun asarar kyau kenan, kin ga yadda kika yi kyau kuwa?".

Ɗaga kai ta yi suna kallon juna, hawayen fuskarta har ya fara bushewa, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Da gaske na yi kyau?".

Kai ya gyaÉ—a mata alamar e, yana yi mata wani irin mayen kallo mai wuyar fassaruwa.

"To shikenan yanzu kam tin da kai ne mijina bari in je mama Haulat ta kara gyara mun jikina".

Bai san sadda ya É—an saki murmushi ba a lokacin da ta yi wannan magana. Ya ji sanyi a ransa har da ajiyar zuciya.

Kamar mai raÉ—a ya ce. "Da gaske nine mijinki yanzu? Ke mallakina ce kenan?".

Kai ta gyaɗa idanunta sarƙafe cikin nasa babu ko kyaftawa, ko kunyarsa bata ji ba.

Shi ma babu ko kunya ya matso dab da ita kamar zai sumbaci lips ɗinta, har ta zaro mashi idanu tana kallonsa, sai kuma ya karɓi wayarsa dake hannunta ya ɗan ja baya yana kallonta.

Number Rizwan ya shigar dan ya kira, ta kafe da kallonsa kamar nace zan kwace mata shi.

Na'urar ce ta sanar masu da cewa number wayar Rizwan a kashe, sosai ya ji babu daɗi, sai ya ji ya kara karaya, nan take ya kara jin ya shiga damuwa matuƙa.

Ganin ya shiga damuwa yasa ta kai hannu ta É—an shafa kumatunsa. "Yah Jawad ka yi hakuri nasan yana hanya ne, idan ya sauka zai kunna wayarsa".

Dawo da kallonsa sosai a kanta ya yi, tin da ta fara magana yake kallon lips É—inta har ta kai aya.

ÆŠan rankwafo kanta kaÉ—an ya yi. "Jannat ina kaunar Yah Rizwan, ba zan iya jure ganinsa a cikin damuwa ba, ban san ya zan yi da rai'na ba".
Cikin tsananin damuwa ya yi maganar.

Hannunsa ta É—an riko a cikin nata, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce...........

Idan kunga tsayin page ɗinku yana raguwa to rashin comment ɗinku ne sila.🥱

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Hannunsa ya É—an riko a cikin nasa, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce. "A'a Jannat, na tabbata damuwa ba zata bari ya kunna wayarsa ba, lallai ina san tafiya Dubai a yau".

Zaro idanunta waje sosai ta yi, kamar zata yi kuka ta ce.
"Dan Allah Yah Jawad ka yi hakuri, babu abin da zai same shi, kuma In Sha Allah anjima yana sauka daga jirgi zamu samu wayarsa a buÉ—e".

Tana magana tana share mashi hawayen dake bin ƙuncinsa, ya shiga damuwa sosai na jin halin da ɗan uwansa yake a ciki.
Chapter 18 · 0% Book details