← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 242

Sashe 189

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ruwan nan bashi da niyar tsayawa kuma cigaba da zamanta a wajen nan ba zai haifar mata da ɗa mai ido bane yasa ta miƙe tare da jan echolac ɗinta ta fara tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tin tana iya ganin dai'dai har jiri ya fara ɗibarta, har lokacin ruwan sama bai dakata ba, nisa sosai ta yi daga in da take, a daddafe take tafiya kamar mai gocewar kashin kafa.

After some hours. Almost 6 hours ana zuba ruwan sama, daga bisani ruwan ta rage zuba amma bata ɗauke dikka ba, irin yap yap yap mai ratsa jiki ya sanya mura ɗin nan shi ne yake cigaba da zuba. Tin daga farkon ruwan nan har karshensa a kanta ya kare, a yanzu an kai gaɓar da ba zata iya cigaba da jurewa ba, tafiya cikin duhun kai yasa har ta fita cikin jama'a bata sani ba. A dai'dai wannan gaɓa ta kasa iya cigaba da tafiya, kanta yana yi mata wani irin azabbabben ciwo mai tsanani, sai kakkarwa take yi, hakwaranta sai ba da sauti mai karfi suke yi, gabaɗaya ta takure ilahirin jikinta waje guda, ga wani irin jiri dake fisgarta da karfi karfi. Dai'dai kasan wani dogon karfen sadarwa wato internet, tana ƙoƙarin ɗaga kafafunta dan ta cigaba da tafiya, sai dai ina, ta kasa, tana ɗaga kafa bata san time da jiri ya fisgeta da karfi har ta saki echolac ɗin hannunta ta tafi gabaɗayanta zata kifa ƙasa ba.

Sai dai bata kai kasan ba ya yi gaggawar tarota ta faɗa saman wide chest ɗinsa. Kamar daga sama haka ya faɗo gabanta, yana sanye da waterproof jacket mai girman da ya wuce gwiwansa, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, dik da yana sanye da face mask, hakan ba zai hana ka gane angry face ɗin nan nasa a yau ta fi ta kullum kasancewa a ɗaure ba, harta idanunsa sun yi jajir kamar bashi da lafiya, wasu zaratan maza guda biyu ne tsaye a bayansa dikkansu rike da umbrella, ɗaya ya rike mashi ne ya tare mashi ruwa, ɗayan kuma ya rikewa kansa a in da ya biyo bayansa dan su bashi tsaro. Ransa ya matuƙar ɓaci sosai, with his harsh voice ya bawa matashin dake bayansa umarnin da ya ɗauka mashi echolac ɗinta su tafi. Yana gama bada umarnin ya ɗan duƙa ya cicciɓeta sai saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya juya da ita.

Bata kara sanin in da kanta yake ba sai da ta farka ta ganta a cikin bedroom, ga wani irin ɗumi mai daɗi dake ratsata, tana ƙudundune a cikin duv mai laushin gaske. Lokaci guda ta ware hancinta ta shaki daddaɗa kuma niimanraccen kamshin dake kai komo a cikin ɗakin, slowly ta fara bin ko'ina na cikin ɗakin da kallo, while tana jin kamar jikinta ba mallakinta bane, dik sai ta ji gangar jikinta tamkar baya a tare da ita. Tana ɗago idanu sai kan drip dake ɗaure a hannunta, zaro eyesball ɗinta waje ta yi dan ta kara tabbatarwa da kanta haka ne. Lokaci guda ta ɗan nisa tare da cigaba da jujjuya eyes ɗinta dan ta tantace a in da take. Sai dai kuma, har ta gama iya kallanta bata iya cinkar a ina take ba, ɗan lumshe idanunta ta yi na ƴan mintunan da ba zasu gaza biyu ba. A hankali ta sake waro idanunta. Ai a miliyan ta zarosu waje ganin shi a tsaye a gabanta, blinking eyes ɗin nata ta yi two time kafin ta tsayar da kallanta cak a kansa, ta tabbata ba mafarki ko gizo bane, shi ɗin ne kenan.

Angry face ɗin nan nasa babu alamar wasa kuma babu walwala ko kaɗan, tamkar bai taɓa sanin menene sakin fuska ba, ya sha kunu ya murtuƙe, ko sannu bai ce mata ba, sai dai ya kai hannu ya fara ƙoƙarin cire drip dake manne a hannunta, dan ya kare. Sosai ta sha jinin jikinta, ta tsorata da ganin yanayinsa, muryarta na ɗan kerma ta furta. "Good afternoon Yah Ramish"...... Tamkar mutum mutuminsa ne a wajen ba shi ba, ya yi banza da ita, kamar bai ji ba. Sake shan jinin jikinta ta yi tana zazzare eyesball ɗinta kamar an tare ɓera a tarko. Bata yi yunkurin sake ɗaga mashi gaisuwa ba, saboda tasan confirm ya jita, amsawa ne bai yi niyya ba.

Zare drip ɗin ya yi ya ajiye gefe guda tare da juyawa ya nufi waje. Bayansa ta bi da kallo, daga kan yanayin sleeping dress dake jikinsa ta iya fahimtar yanzu dare ne ba rana ba, ta sha mamaki sosai na ganin cewa dare ya yi, ita da ta sume a tsakanin azahar da la'asar, bata ma san kwana ɗaya ya wuce ba, dan tin jiya ta sume, sai yau ta farfaɗo, dan ma Allah ya taimaketa ta samu kula daga hannun Dr Raj da ya dawo jiya, kuma gobe zai koma kingdom of power, wani dalili ya dawo da shi, ba dan kular da ta samu ba ai da ta ɗanɗana a jikinta. (Ina tantamar anya Leesharh bata da kara mun ciki kuwa? Idan ma ba ciki akwai aljanu a kanta gaskiya 😅 kai nama fi zargin cikin ne yake sakata yin abubuwa off head haka.)

Wasa wasa tsawon kwanaki biyu Ramish baya kulata, baya yi mata magana baya kuma amsa nata maganar, alamar fa ran maza ya ɓaci sosai, tin bata wani damuwa har abin ya fara taɓata, sai take jin tamkar a rami aka haƙa aka sanyata, dik ta fara fita hayyacinta, tinani kala kala ne cike a cikin zuciyarta, wani lokaci ta ce bari ta same shi ta bashi hakuri, sai ɓangare na zuciyarta ya ce mata waye nata ne shi ɗin da har zata ce dan baya yi mata magana kuma baya amsa nata maganar zata damu? Shin sun haɗa dangi ne? Mijinta ne? Ko ubanta ne? Uwarta ne? Ko yayanta ne? Waɗan nan tinane tinanen su suke sanyawa ta ji ba zata iya tinkararsa ta bashi hakuri ba, ga shi kuma zuciyarta ta kasa jurar rashin maganar nasa, tana jin kamar ta fasa ihu. Har jikinta ya warware shi yake cigaba da kula da ita, time na shan magani da ya yi zai zo ya bata, idan ya fita ba zata sake ganinsa ba har sai zai sake bata wani maganin. Ko abinci ba shi yake kawo mata ba, wata dattijuwa ce take kawo mata, kuma idan ta yi wa dattijuwar maga sam bata amsa mata, abin ya dameta sosai, ga shi ba gidansu da ta sani ya dawo da ita ba, wannan gidan kam ma gabaɗaya ta rasa gane kansa, ko ta leƙa ta window ba abin da take gani face pool dake ta baya da basket ball area da gine ginen dake waje, abin ya jefata a ruɗani sosai matiƙa.

Uhm bata san cewa ita ce kawai makaminsu guda ɗaya da suke da shi dan isa ga masu nikaf ba, tsaronta da lafiyarta abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesu, shiyasa ma ya canza masu gida, ya kawota waje mai tsaro sosai, damuwarsa yanzu ta samu lafiya ya samu hujjojin dake hannunta ya fara gabatar da aikinsa.

Yau takama Friday, zaune take a saman dadduma bayan ta yi sallar isha'i, ta yi shiru tana askar, amma tinaninta dik yana a kansa, yau ta kai har kololuwa sosai. Good 30 mins ta ɗauka a zaune a saman daddumar tana addu'ointa kafin nan ta miƙe, jiki dik babu kwari ta nufo bakin bed ɗinta da hijabin a jikinta, yau ko lunch bata yi ba saboda damuwa a kansa. Dik halin da take ciki kuma sarai yana sane, dan ya dasa mata Camera a cikin ɗakin, haƙiƙa ya ji babu daɗin kin yi lunch da ta yi, amma ya danne ya cigaba da harkokinsa.

Tana zama a bakin bed ɗinta sai ga dattijuwan ta kawo mata abincinta kamar yadda ta saba, haɗaɗɗen abinci mai rai da lafiya, sai tashin kamshi yake yi, tsohuwar ce mai girka mata. Sosai ta yi mamakin ganin lunch da ta kawo Leesharh bata ko taɓa shi ba, kamar yadda ta ajiye babu abin da ya motsa shi daga wajen, amma kasancewar Ramish ya ce ko word ɗaya kada ta yarda ya haɗata da Leesharh ɗin yasa bata tambayeta meyasa bata yi lunch ba? Sai kawai ta kwashi kayan abincin ta wuce ta fita bayan ta ajiye mata dinner ɗinta kenan. Dogon tsaki Leesharh ta ja bayan fitar tsohuwar, sannan ta dallawa kayan abincin harara tamkar su suka yi mata laifi. A dai'dai lokacin da take wannan abin sai da ta so sanya Ramish murmushi, saboda yana kallanta, dan dai bai iya murmushin bane da yau sai ya yi. A ransa ya ce ko me dinner ɗin ya yi mata take harararsa kuma? Yarinya sai faɗar bala'i!.

A fili kuwa cigaba ya yi da feshe jikinsa da daddaɗar perfume ɗinsa, yana shirye cikin kayan barci, kwanciya zai yi idan ya je ya bata drugs ɗinta ya dawo. Ita kuwa, gyrawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da tinaninsa, tana jin tamkar ta tashi ya je bedroom ɗinsa ta sanyasa a idanunta ko zata ji sanyi. Amma girman kanta da rike amanar Sharifat yasa ba zata iya ba, a haka ta daure ta lumshe idanunta alamar barci take san yi, ba zata ci dinner ɗin ba kenan. Da kwanciyarta bai fi five minutes ba sai ga shi ya shigo bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. A hanzarce ta miƙe zaune idanunta a kansa, shi kuwa ya ɗaure angry face ɗinsa sosai, yana tafiya cikin natsuwa. Kai tsaye gaban bed ɗin ya nufo, bai ko kalli in da take ba ya hau ɓalle drugs ɗinta yana miƙa mata a kan ta karɓa ta sha.
Chapter 189 · 0% Book details