Sashe 53
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai bata san time ɗin da ta kurma ihu ba, wayoyin dake hannunta dikka biyu suka faɗi ƙasa, ba komai ya saka ta ihu ba face yadda Bilal ya riko wuyar rigarta kusan hannunsa dikka a saman tudun tula tulanta, shiyasata ihu ba shiri.
Janyota Bilal ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya saketa tare da É—aure fuska sosai, a takaice ya ce. "Meyakawoki nan?".
Kasa tsayuwa a kan kafafunta ta yi, cikin sauri ta durkushe kasa tare da fara ruwan zafafan hawaye, hannu tasa ta fara laluɓar wayoyin da suka faɗi ƙasa, tsikar jikinta dik sai wani mimmikewa tsaye yake yi.
A karo na biyu Bilal ya sake tambayart me ya kawota nan.............. Sai a lokacin ta É—ago da kanta a kansa, cikin sarkewar murya haÉ—e da tashin hankali a tattare da ita ta ce.
"Yah Bilal dama nazo ne in faɗa maku wancan waya wlh bana Leesharh bace, ashe irin namu ne da kasaya mana, wlh tana da gaskiya ba nata bane, kaga namu wayoyin". Ta yi maganar tana ɗagowa, tana kai karshen maganar kuma ta miƙa mashi wayoyinsu dake hannun, sai kerma hannun nata yake yi yaki tsayawa waje guda.
Sai a wannan lokaci Ramish ya juyo, ya ɗaura towel a waist ɗinsa, kallo ɗaya ya yi masu ya wuce ya nufi toilet............ Karɓar wayoyin Bilal ya yi haɗe da furta alhamdulillah da ɗan sauti, da alama shi ma ya ji matuƙar daɗi, bai yi magana ba sai ya nuna mata hanyar fita kawai, a kan ta je.
Cike da tsoro ta ce. "Yah Bilal to Leesharh É—in fa? Zaku dawo mun da ita?".
Kai kawai ya jinjina mata tare da kara nuna mata hanya. Da gudu ta raɓa gefensa ta fice tana toshe bakinta saboda wani iri kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro da ya kubce mata.
Ajiyar zuciya Bilal ya sauke tare da É—aura kallonsa a kan wayoyi, tabbas wannan ne wayoyin da ya saya masu, wancan kenan irin nasu ne kawai? To waye mamallakin wancan wayar? Ya jefa kansa tambayar.
My people's da ni da ku idan baku manta ba mun san ya aka yi wayoyin nan suka fita iri É—aya, in baku manta ba a baya na gaya maku masu nikaf sun canza mata ainahin wayar da suka bata da farko, har na ce maku sun bata wani irin wanda Bilal ya saya mata ita da Sharifat sak ko? To wannan shi ya kawo ruÉ—ani a cikin al'amurran, wayoyin iri É—aya ne, Sharifat guda É—aya tasan Leesharh da shi shi ne wanda Bilal ya basu, bata san da na masu nikaf ba! Wannan shi ne, kunga Sharifat zata wanke Leesharh ba tare da tasan da gaske wancan wayar ma na Leesharh É—in bace. Wai akwai case a gaba gaskiya!!.
Dama kuma tun farko Leesharh ta ce da su Bilal ba wayarta bane, kunga kuwa yanzu da Sharifat ta kawo wannan tsab zasu iya yarda ba nata É—in bane, akwai cakwakiya fa sosai, shin masu nikaf zasu É—auki mataki ko dai shirun banza suka yi? Muje zuwa!.
Karisawa cikin É—akin Bilal ya yi, saman bed ya haye tare da jawo laptop na Ramish ya fara latse latsensa.
•••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥
Tsaye take gaban wannan korama dake aman ruwan, yanayin yadda ruwan yake zuba abin gwanin ban sha'awa, ka korayen ganyayyaki kewaye da wajen, sannan ga ruwa gudu a kasan koramar yana ta gudu mai haske tar, tsabar haskensa har ya É—auki kalar sararin samaniya wato sky blue.
Ta ko'ina kamshin furanni ne yake tashi saboda yawaitansu a wajen, daga gefe can tsuntsaye nau'ika daban daban ne suke dira a kasa bakin ruwan dake gudun suna shan ruwa sai su sake tashi, yanayi mai daÉ—i ga iska na É—an kaÉ—awa a hankali hankali yana kaÉ—a furannin dake wajen kamshinsu yana kara tashi.
Wajen zai yi matukar dacewa da masoyan dake bala'in kaunar junansu. Ta yi shiru kamar mai kallan ruwan dake kwaranya daga koramar, amma kuma ba shi take kallah ba, hakika hankalinta ya luluƙa duniyar tinanin kingdom of power da kuma Hoorain, wannan abin da ya yi mata ya zame mata babban tabo a rayuwarta da ba zai taɓa gogewa ba.
Pretty bata a tare da ita, ta tafi É—auko masu fruits, so ita kaÉ—ai take tsaye a wajen.
Ta yi nisa cikin tinaninsa da take yi ba zato ba tsammani ta ji an rufe mata idanu daga ta bayanta. Hakika ta tsorata matuƙa, dan yanzu abu kaɗan yake razanata yake kuma ɗaga mata hankali.
Ihu ta zunduma tare da fara ƙoƙarin kwatar kanta zata zulle. Saura kaɗan ta afaka cikin wannan ruwan gudu a ƙoƙarinta na zullewa. Da sauri ya riketa da kyau, kamar mai raɗa ya ce mata shi ne fa ta nitsuwa kada ta jewa kanta ciwo.
Dik da ta ji muryarsa bata yarda ba, dan yanzu bata jin zata yarda da wani a rayuwarta, babu wani sauran yarda a zuciyarta, ƙoƙari ta cigaba da yi dan kwatar kanta.
Da yaga haka sai ya zame hannunsa daga idanun nata, dan taga zahiri, sai dai bai saki hannunta da rike dan kada ta faÉ—i ba, sai ya sanya É—ayan hannunsa a saman Waist É—inta.
Cak ta tsaya da ƙoƙarin zillewa da take yi, nan take ta ji mummunar faɗuwar gaba, da sauri ta yi ƙoƙarin jiyowa dan ta tabbatarwa da kanta shi ne ko ba shi bane.
Ganin yadda ta juyo da sauri yasa ya yi saurin saketa tare da ce mata. "Kiyi hakuri"........... Jinjina mashi kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba, sai ta buƙaci matsawa daga kusa da shi.
Bai bari ta yi hakan na shi sai ya É—an matsa baya yana kara ce mata ta yi hakuri. Da okey ta amsa mashi tana mayar da kallonta a wajen koramar.
Wai shin me ya dawo da shi bayan ya ce ya tafi?. E to tinanin Zunaira ya hana shi tafiya, dan haka sai ya samu waje kasan wani bishiya ya zauna yana ƙoƙarin yankewa kanshi shawarar ya dawo ya sake ganinta ne ko kuma ya hakura ya tafi sai gobe?.
Yana tsaka da wannan tinani ya hango gungun mayaka sun dinfarko cikin dajin wanda ko ba'a faɗa mashi ba yasan su Pretty suke nema, tun da ya sha artabo da su a kan hakan. Wannan dalilin yasa ya hau saman bishiyar da yake karkashin ya ɓuya, sai da suka wuce sannan ya sauko ya bi bayansu dan yaga ina suka nufa.
Ganin sun bi wani hanya ba ta in da su Pretty suke bane yasa ya ce to bari ya leƙo su Pretty su ɗan sake ɓata lokaci a tare kafin nan ya wuce, kun ji dalilin dawowarsa. Har zai wuce wajen nasu sai ya hango Zunaira tsaye a bakin koramar nan shi ne ya ƙariso gareta, dama tinaninta ne a ransa.
"Ina Omnish?". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
Kamar ba zata amsa mashi ba, amma ita É—in Æ´ar halak ce, akwai tina alkhari, dan haka sai ta daure ta ce. "Ta je kawo fruits".
"Amma ba nace kada ku fita waje ba?".
Kasa ta yi da kanta tana tinanin amsar da ya kamata ta bashi, a dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta É—auke da fruits a kwando.
Shiru suka yi daga shi har Auta, cike da mamaki Pretty ta ce. "Kai ne ka dawo?". Yadda ta yi maganar sai ku zaci bata yi wani laifi ba.
Binta da kallo ya yi yana mamakin halin Omnish É—in nan nasa, yarinya ce sai ka rasa a wani mataki zaka ajiyeta.
"Omnish wai ba nace kada ku fito waje ba? Ke kika ja Zunaira kuka fito ko?"............ Baki ta turo ba tare da ta bashi amsa ba, saboda ita dai magana ta Allah bata san zaman cikin nan.
Jin ta yi shiru yasa ya sake cewa. "To ku wuce mu tafi". Ya faÉ—a ba tare da wasa ba.............. Ran Pretty bai so ba ta wuce gaba tana tura baki, Auta ta rufa mata baya. Haka suka wuce izuwa ma kwancinsu.
Ko da suka shiga sai da ya jima tsaye a wajen yana satar kallon Auta kamar bakinsa da magana, kamar yana san amayar da ita kuma, sai dai kamar yana tsoro, wato dik zafin kan mutum da izzarsa abu guda ɗaya tana ɗarsa mashi tsoro a cikin zuciyarsa, wannan abin kuma ba komai bane face soyayya, wlh in dai namiji soyayyar gaskiya ce a ransa yana ɗarsa mashi tsoro da ɗarɗar a kan ua faɗa ko kada ya faɗa, yana jin matuƙar tsoron ya furta bai yi nasara ba, tinanin abin da zata je ta dawo da abin da rashin nasararsa zai haifar masa yasa yake dasa mashi tsoro a zuciyarsa.
Haka ya rufesu, ya É—an jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya tafi. A wannan karon ma yana tafiya suka buÉ—e suka fito, wlh ita dai Pretty Allah ya gani ba iya zama a wannan waje take yi ba, burinta ta fito waje, gara ma lokacin da Auta take jinya a cikin wajen, a wannan lokaci kullun tana ciki, saboda tana kula da Auta.
Sadauki ne ya tsinto Auta a cikin ruwa ya kawota wajen Pretty, shi kuma ya yi jinyarta tsawon lokaci, shiyasa kuka ga ta shiga ransa sosai, dan dik wasu magunguna shi yake saka mata a ciwon, Pretty kullum tana manne da ita, ko nan da can bata san matsawa, suna tare, kusan a tare ita da sadauki suka yi kinyarta.
A ranar da Auta ta buÉ—e idanu da Pretty ta fara yin arba, shiyasa take balain jinta a ranta sosai.
Ga dikkan alamu Auta ma bata san zaman cikin ramin nan, saboda da Pretty ta ce tazo su je waje zata ce to, ta bita su tafi, ga shi ita bata gama samun lafiya ba, har yanzu akwai sauran magani a jikinta da ba'a ɓare shi ba.
Kuma ita Auta bata san cewa akwai waɗan da suke farautar rayuwar su Pretty tsawon lokaci ba, bata taɓa kawo hakan a ranta ba, a dik tinaninta fita ne kawai sadauki baya san su yi yasa kullun yake yi masu gargaɗi a kan fita, basu san cewa abin ya wuci haka ba.