← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 242

Sashe 155

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro idanu waje ta yi, cike da ƙaguwa na san jin abin da zai yi masu ta ce. "Me zaka yi masu da har zai sa su koyi darasi?". Hannu yasa yana share hawayenta ya amsa mata da. "Kada ki damu, ke dai keep praying for me". Ya kai karshen maganar yana duba wayarsa dake ruri alamar shigowar kira. Number momma ce again, kuma yasan dad ne, dan haka sai bai yi picking ba, saboda yana san ya ɗan yi tinani a kan irin lesson da yakamata ya koyar da familyn nan nasu, su san cewa mutum ɗan adam ba abin rainawa bane, da talaka da mai kuɗi dik Allah ne ya yi su..

Jama'a na ce mu jinjinawa momma, lallai ba shakka jinin momma ce yake gudana a jikin Smart, a gabaÉ—aya kingdom of power momma ce kawai bata kyama ko kyarar talaka, ita ce kawai ta É—auki kowa dik É—aya suke, ita ce uwar marayu irinsu Mahnoor, Zee, Khadijah and Mahreen, lallai ba shakka momma baiwar Allah ce kuma jininta ya fi karfi a jinin SMART!! Dan kunga shi ma baya gudun talaka bawan Allah!.

Pretty ce ta katse masu hiransu ta hanyar miƙewa zaune a saman kujerar da take kwance, kwata kwata Auta bata lura da ita ba tun shigowarta, dama a saman kujerar ya kwantar da ita, sannan ya wajen ya yi mata allurar da ya ceto rayuwarta. Sai dai kuma ya yi matuƙar mamakin ganin ta yi saurin farfaɗowa, yasan dai zata iya kai kwana biyu a sume kam, sai kuma ga shi ko awa biyu bata yi ba ta farfaɗo, abin da bai sani ba shi ne ita fa Pretty ko da bai yi mata wannan allura ba zata farfaɗo, saboda poison dake cikin chemical ɗin bai yi mata lahani ba dan ita ma akwai irin abin dake jikin Sweetie a jikinta, kuma ita ma hannunta yana iya yin magic, sau da dama tana ɓarin abu ta hanyar magic ɗin, amma rashin sani yake sakawa ta yi zatan kawai ɓari ta yi, bata san da shi a hannunta ba.

Da kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa a ransa yana mamakin tashinta a yanzu. Cike da kula da so da kauna Auta ta ce. "Pretty ina kika shiga ina ta nemanki". Tana aikin turo baki bata yi magana ba, miƙewa daga jikin Smart Auta ta yi ta koma wajenta dan ta ji menene yake damunta. Shi kuma Smart miƙewa ya yi yana faɗawa Auta zai je gidansu wajen mom sai kiransa take yi, yanzu ba jimawa zai dawo, daga karshe ya ce mata kada ta sare kuma kada ta bar Hoorain cikin kewa ta rinƙa kiransa a waya In Sha Allah kukanta zai tsaya. Da okey ta amsa mashi tana murna, har da sakin murmushi. Kai yasa ya nufi waje a ransa yana tina ta yadda zai yi ya yi maganin King, lallai ba zasu koma kingdom of power a yanzu ba, dole su dakatar da auren Abdussalam, sai after one month zasu koma, dole ya yi magana da momma dan su shirya komai a tare ta yadda ba zasu rasa King ba.

My people's kuna ganin shirin nan zai shiryu kuwa?. Auta zata mallaki Hoorain kuwa a yadda King ya datse dik wata alaƙarsun nan?. Muje dai zuwa, zamu ga shin Smart ne zai yi nasara ko King!.

🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

44

🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

Tafiya take yi tana waige waige ta fito daga part ɗin mama ta nufi part ɗin momma domin ta duba Zee, har yanzu uncle Jahiz bai dawo mata da babynta ba, yana can ɓangaren Aunty MieMie suna hira, Aunty MieMie ta rike baby gam, ta ce sai dai uwarsa ta biyo shi part ɗinta, ma'ana sai dai Khadijah ta dawo part ɗinta da zama, dan ita ta samu yaro, dama bata da shi, uncle Jahiz ya ɗauka wasa take yi, aikuwa ta nuna mashi da gaske take yi, dan fa ta dage Allah ba zata bada babyn nan ba, uwarsa kawai ta dawo part ɗin da zama dan yaron ya shiga ranta.

Sai waige waige take yi dan bata gama sanin hanya ba, hanyoyin akwai sarƙakiya, idan ba ka san cikin family part sosai ba zaka iya ɓacewa, shiyasa take ta waige waige, taga hanyar shiga part ɗin King and Akkas part, sai ta ruɗe ta rasa ina zata bi.

Unexpect suka ci karo da mutum, ya fito daga bedroom É—in King, King ne ya kirasa a yazo a kan batun Spender, so shi ne dalilin zuwansa. Karo suka yi ta É—an yi baya tana goge goshinta da ta buge da kirjinsa, da yake ita ta fi Zee ladabi da kuma hankali sai ta durkusa kasa tare da É—aga mashi gaisuwa.

Ido uncle Abbas ya zuba mata yana mamakin ganinta, dan shi bai san ta a kingdom É—in ba. Jin bai amsa mata bane yasa ta ce. "Kayi hakuri ban ganka bane shiyasa"...... Jin kalamanta yasa ya yi saurin ce mata. "Babu komai tashi ki je abinki".

Miƙewa ta yi tana yi mashi godiya tare da satar kallansa ta ƙasa ido, gaba ta yi ba tare da tasan ina ta dosa ba, dan bata gane hanyar part ɗin momma ba. Da kallo uncle Abbas ya bita baya san kawar da kallansa daga kanta. Har ta ɗan yi nisa ta tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Zo ina da tambaya"........ Juyowa ta yi ta dawo gabansa, tana ƙoƙarin tsugunnawa ya yi saurin cewa. "A'a ba sai kin durkusa ba, magana zamu yi a tsayen ma is okey".

Ƙasa ta yi da kanta tana amsa mashi da okey cikin harshen turanci. "Zan iya sanin wacece ke?". Ya jefa mata tambayar yana ɗan sunkuyo da kansa ya kalli face ɗinta. Lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi, sai ta ji wani irin fargaba mai razanarwa, tsoronta ɗaya kada yasa a hukuntata dan bata da wata alaƙa da masarautar, kada ya ce waye ya kawosu? To waye zata ce mashi tun da ita ko sunan uncle Jahiz bata sani ba bare ta faɗa mashi sunan wanda ya kawosu.

Ganin ta yi shiru ta rasa abin faɗe yasa ya ce. "Zaki iya tafiya". Dan ya lura tambayarsa ya saka ta a cikin damuwa, lokaci guda hakan ya bayyana a face ɗinta. Ai yana cewa ta tafi ta yi gaggawar juyawa har kamar zata yi tuntuɓe, da kallo ya bita yana jin kamar wani abin a ransa, mamakinsa ɗaya shi ne a ina aka samo waɗan nan black beautys ɗin?.... Ni kam na ce to dama mu Nigerians ai shegen shiga rai ne da mu ato, dik in da muka je sai mun ratsa zuciyar mutane, bare ma mu arewacin Najeriya ai daban muke.

Har sai da ta kurewa ganinsa sannan ya ja dogon numfashi tare da wucewa ya nufi elvator domin ya yi ƙasa ya koma part ɗinsa, mammie na can tana jiransa ya dawo ta zazzage mashi jajjagen masifar da ta jajjaga ta ajiye mashi. Shi kuwa yana nan zuciyarsa ta shiga wani yanayi. Babbar magana, muje zuwa my people's, ba'a fara komai ba, RAWANIN ZALINCI zai baku mamaki gaba kaɗan, fatana dai Allah ya ara mana lokaci!!.

Sai da Khadijah ta shiga almost part uku a cikin amma bata iya gane part ɗin momma ba, daga karshe ta lallaɓa ta koma part na mama ta yi kwanciyarta zuciyarta cike da tunanin ina Zee? Bata damu da tunanin ina babynta kamar yadda ta damu da tunanin ina Zee ba?. Dan ta san halin yar uwar tata da shegen zuciya bata ɗaukar raini.

A ɓangaren guda kuwa, mammie dai ta yi jigilar aikin gasawa Sarina jiki, Sarina anji jiki, dan ma Allah ya taimaketa a ba kan tsini ta isko Smart ba, ai da bata rage ba, amma dik da haka ta jibgu ba karya, jiki dik ya yi ruɗu ruɗu ya kumbura, ta sha ruwan zafi kam ba karya.

Idan muka waiwaya gefe guda kuma, a can hospital ɗin Kingdom ɗin, a lokacin da King ya saki Hoorain, kwance yake a saman bed na hospital ɗin, sai da ya yi good two days kafin ya dawo cikin hankalinsa, amma fa har lokacin baya iya tafiya, tin da yake a rayuwarsa ba'a taɓa yi mashi irin wannan horo mai bala'in tsananin ba, wannan ɗakin duhu wlh karshen azaba ne, amma kuma da yake ba bawa yake sanyawa kansa so ba, dik wannan wahala da suka bashi wlh soyayyar Auta ninkuwa ya yi a ransa, sai ya ji ma tamkar buɗe kirjinsa suka yi suka zuba mashi santa na wannan azaba da suka yi mashi.

A ranar da ya farfaɗo ma da sunanta ya farfaɗo a bakinsa, sai dai yana buɗe idanunsa da Abbonsa ya fara yin tozali, ya ji matuƙar daɗin ganin mahaifin nasa, sai dai kuma da buɗar bakinsa ya ce. "Abbo Hoonaira bata sake zuwa wajena ba ne?". (Yana tinanin tin da ta je wajensa a ɗakin duhu kenan bata sake zuwa ba, dan tun wannan rana da ta je wajen nasa King ya zo ya ɗauketa, zafin ɗaukarta da aka yi yasa zuciyarsa ta tsananta ciwo, dalilin suman da ya yi kenan sai yau ya farfaɗo.)

Ɗan girgiza kai Abbo ya yi irin alamar tausayawa ɗan nasa, shi ma ya rame sosai, dama ga tsufa, ga ciwo, ya sha wahala dattijon arziki, zuciyarsa ta rauta a kan Hoorain da Auta sosai, sai yake jin kamar ba zai iya sanya karfi wajen rabasu ba, ga shi kuma ya yi wa King alkawarin zai rabasu, dama a tinaninsa karfi zai sakawa Hoorain ɗin, zai ce mashi ya zaɓa ko shi ko Auta, kowa dai yasan dole Abbonsa zai zaɓa ko da hakan zai yi sanadiyar rayuwarsa tun da iyaye dai ba'a haɗasu da komai, to commander ya ji jikinsa ya mutu a kan wannan mataki da yake san ɗauka.
Chapter 155 · 0% Book details