← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 242

Sashe 17

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sha madarar mamakin rashin samun Chuchu a É—akin, Aneesa kawai ta samu, ta so tambayarta ina Chuchu and Auta sai kuma ta sami Aneesa tana murzar kuka, shanye tambayar ta yi a ranta tare da hayewa saman bed É—in, cikin sanyin murya ta fara rarrashin Aneesa tana bata baki har da gaya mata wata bata auran mijin wata.

Sam Aneesa taki kulata, dan ita kaÉ—ai tasan me take ji a cikin zuciyar nan tata, tana san Rizwan za'a aura mata Jawad haba dole ta ji zafi.

==========Luv Bird💘🕊️==========

A tsorace ta sake shi tare da komawa jefe ta tsaya haÉ—e da dawo da kallonta a kansa. Dik jikinta kerma yake yi alamar tsoro, a hankali take ta satar kallon su uncle Abbas da suka shigo cikin É—akin.

Allah sarki shi kuwa kasa iya riƙe kansa ya yi, wani irin jiri da ta ɗebesa ne sai da ya yi baya baya ya koma saman mattress ɗinsa ya zauna yana sauke numfashi a hankali hankali mai zafin zazzaɓi, dama saboda ganinta yasa ya samu kwarin gwiwar iya miƙewa.

Dikkansu idanunsu a kan King da yake ta aikin binsu da dara daran idanun gadon nan nasu.

Momma dake tsaye kusa da uncle Taheer ne ta ce.
"Jannat me kike yi a nan kuma? Ya aka yi su Haulat suka barki kika fito daga wancan part É—in?".

Ai tana jin maganar momma tamkar wadda aka kwaÉ—awa guduma a tsakiyar kai, da karfi ta wage murya ta rushe masu da kuka babu kama hannun yaro.

Kasa da kai Jawad ya yi yana tunanin abin da yakamata su yi, dan dai shi wlh ba zai iya hakura da ita ba!.

Uncle Taheer ne ya ce. "Haba momma, wai ni ku meyasa kuke son saka yarana kuka ne? Yanzu dai ga shi kin sakata kuka".

Harararsa ta yi tare da cewa. "Daga tambayarta zata rushe da kuka ka ce na sakata? To me na yi mata?".

Uncle Taheer zai sake yin magana King ya É—aga mashi hannu hakan ya haifar da nutsuwa tsit na gabaÉ—aya familyn dake biye da shi, sannan suka kara gyara tsayuwansu tsit alamar sun bi umarni.

Uncle Abbas ne ya fara takawa ya ƙarisa cikin ɗakin kusa da Chuchu, hannunta ya riƙo a cikin nasa, cikin sigar rarrashi haɗe da zolaya kaɗan ya furta.

"Menene kuma Jannat? Meyasameki kike kuka?".
Kamar bai san kukan me take yi ba!.

Faɗowa jikinsa ta yi tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, irin kukan nan ne wanda zuciyan mutum yana kusa, zaku ji har wani shessheƙa take yi kamar zata haɗiyi zuciyarta.

Cikin kuka haÉ—e da É—aga murya, da kyar ta iya fara faÉ—in.

"Daddy wlh ni Yah Jawad nike so, shi ma ni yake so, dan Allah ka cewa dad kada ya rabamu, ni bana son Yah Rizwan".

Yadda take magana sai ta baka tausayi, har wani shakewa voice É—inta yake yi.

King ne ya amsa mata da cewa. "Amma ba ke kika ce mana Rizwan kike so ba?".

Sautin kukanta ta kara haÉ—e da faÉ—in. "Allah dad ni ban ce ba, ni Yah Jawad nike so".

Momma ce ta murje idanu haÉ—e da shafa toka kamar bata san komai ba ta ce.

"Da bakinki kika ce Rizwan kike so ba Jawad ba, dan haka zo ki wuce ki koma wajen su Haulat su cigaba da shiryaki anjima akwai taron dinner na musamman".

Ƙanƙame uncle Abbas da karfi ta yi tana mai cigaba da kuka tana faɗin.
"Daddy ni nasan zaka yarda da ni, tun da dad da momma basu yarda da ni ba shikenan, nasan kai zaka fahimceni, wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, dan Allah daddy kada ka bari dad ya kai ni wajen Yah Rizwan........"

Bai bari ta ƙarisar da maganar ba ya ɗaura manuniyar yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru, dan yadda take maganar nan tsab zata iya haɗiyar zuciya ta mutu.

"Ya isa haka Jannat, ina nan ai babu wanda zai rabaki da Jawad É—inki, ba wanda zai kai ki wajen Rizwan, ki kwantar da hankalinki".

Cewar uncle Abbas da yake aikin goge mata hawayen, sai dai yana gogesu wasu suna kara zubowa kamar ruwa ya buÉ—ewa kansa hanya.

Cikin zolaya momma ta ce. "A'a fa matar Rizwan ce kada ka kawo mana shubuha a cikin lamura".

Kara ƙanƙame uncle Abbas ta yi tare da cewa. "Wlh ni daddy bana son shi, Yah Jawad nike so".
Yadda ta yi maganar a ruÉ—e ne yasa uncle Abbas ya yi saurin katseta, dan ya lura su momma zasu ruÉ—ar mashi da ita, sai ya yi maza ya ce.

"Babu wanda zai kai ki wajen Rizwan, Jawad shi ne mijinki ba Rizwan ba".

Jawad da tun da suka shigo kansa na'a kasa ne ya É—ago a miliyan yanzu, idanu ya zaro waje sosai, da kyar ya iya cewa.

"Daddy me kake nufi?".

Jinjina kai uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Kwarai kuwa abin da ka ji shi ne gaskiya, kai ne mijin Jannat ba Rizwan ba".

A hanzarce ya miƙe tsaye, lokaci guda ya ji karfi ta zo mashi, ita ma Chuchu bata san lokacin da ta saki uncle Abbas ta dawo da kallonta a kan flowern nata ba.

"Please dad don't play with my heart, ba wai na faÉ—i hakan dan raini bane, a'a, nasan ka saba yi mun wasanni kala kala, please don't make this as a part of joke to me, zan iya mutuwa idan ka yi hakan".

Siririn murmushi uncle Abbas ya saki, a hankali ya kamo hannun Chuchu, ya matso ya riƙo hannun Jawad ɗaya. Ya buɗe tafin hannun Jawad ya ɗaura tafin hannun Chuchu a saman, cike da so da kauna ya fara magana kamar haka.

"I knew that koda yaushe muna cikin wasa da kai, but this isn't a joke, Jannat is ur wife, gata nan kuma na miƙa maka ita amana, don't let her tears to come out dik da nasan ba zaka yi hakan ba".

Ai mutuwar tsaye ya yi, ya kasa iya sake yin magana, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne suka fara wanke fuskarsa, ya kasa fahimtar a wace iriyar duniya yake, gabaÉ—aya ya rasa me zai sake yi.

King ne ya ce. "Eyeee my son ya girma ya yi aure, to me zaka yi mana kuka kuma?".

Uncle Taheer ya karɓa ta cewa. "Ni yaya kada ku takurawa ɗana, ku je bari mu yi sirri da shi".

Yana magana yana nufar Jawad.

Mom ce ta ce. "To mu dai a bamu É—iyarmu mu tafi da ita, sai ku yi ta sirrinku É—in".

Ta yi maganar tana miƙawa Chuchu hannu a kan ta zo. Kara ƙanƙameta Jawad ya yi, da kyar ya iya furta.

"Please Momma ki É—an bar mun ita a nan ko da na 10 mins ne kin ji? Long time bana tare da ita, and...........".

Uncle Abbas ne ya katse shi da cewa. "Babu wanda zai É—auke maka ita, ba 10 mins ba, even one hour take is your time today".

Juyawa momma ta yi ta nufi waje tana faÉ—in. "Kuzo mu je kada Abbas ya koremu".

King ne ya rufa mata baya a in da ya nufi fada dan ya bada umarnin sarkin hatsi ya fito da abinci a girka dayawa a kai gidajen marayu, sannan su tabbatar sun girka abincin da zai kai a ciyar da gidajen prison dake garin gabaÉ—aya, su É—auki tsawon sati guda suna ciyar da gidan prison and gidanjen marayu, su rabawa talakawa buhuhhunan abinci da kuÉ—i makudai dik dan murnar bikin Jawad and Chuchu, sannan su ziyarci asibitoci dan duba waÉ—an da za'ayiwa aiki kuma babu kuÉ—in yi, su biya masu kuÉ—in aikin, wanna hurumin sarkin fada ne, shi zai jagoranci zuwa asibitoci ya tabbatar ya biya kuÉ—in aiki da magungunar marasa karfi.

A wajen É—aurin aure ma ya yi kyauta da kujerun makka sun kai 50, ya kuma yi kyauta da makuÉ—an kuÉ—aÉ—e ta hanyar raba check, anyi abubuwa da dama, King adalin sarki ne mai taimako sosai.

Wai ina maganar waÉ—an da suka karo masu hari? Muje dai zuwa.

Uncle Taheer ma fita waje ya yi ya bar uncle Abbas, Jawad and Chuchu kawai a cikin É—akin.

Zaunar da Jawad a bakin bed uncle Abbas ya yi, sannan ya ja hannun Chuchu suka zauna a tare, yana a tsakiyarsu ya fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya.

Shiru suka yi suna sauraronsa har ya dasa aya, sannan ne Jawad ya ce.
"Daddy please tell me yadda aka yi Jannat ta zama mallakina bayan ka ce mun Yah Rizwan dad ya bamawa?'.

Ajiyar zuciya uncle Abbas ya sauke, nan take yanayin face É—insa ya canza, alamar ya shiga damuwa, hakan yasa zuciyar Jawad ta kara karaya, dan bai san dalilin sauyawar face É—in daddyn nasu ba.

Sun kasa kunne suna jiran jin me zai ce da su, ita kanta Chuchu ta fahimci uncle Abbas ya shiga damuwa a wanna tambaya da Jawad ya yi mashi.

"Rizwan ne ya sami dad É—inku É—azun da safe ya sanar da shi a É—aura aurenka da Jannat ba da shi ba".

Zaro idanunsu a tare suka yi, they will not expect that at all, so they shocked.

"Dama Yah Rizwan yasan ina son Jannat ne ko dai kai ka gaya mashi daddy?". Jawad ya yi tambayar cikin ƙaguwa da san jin an warware masu komai dallah dallah!.

Girgiza kai uncle Abbas ya yi, sannan ya É—aura da cewa.
"Ko É—aya babu wanda ya gayawa Rizwan kana son Jannat, shi da kansa ya san da hakan?".

Sam Jawad bai san lokacin da ya furta. "How and when?". Ba.

"Lokacin da ya sanar da dad É—inku ya sadaukar da soyayyarsa wa kai sai ya wuce room É—insa ya je ya fara haÉ—a kayansa zai koma Dubai, a time É—in dad É—inku ya kirani a waya ya ce dik in da nike na zo yana son ganina".

"Ban ɓata lokaci wajen zuwa in da yake ba, na same shi a room ɗinsa, I was so surprised time da ya gaya mun furucin Rizwan a kanku, ban iya haɗiye abin a raina ba sai da na bi Rizwan ɗakinsa dan na ji meyasa ya yi hakan".
Chapter 17 · 0% Book details