← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 242

Sashe 225

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hanzarce momma ta rikota tare da cewa. "Ba sai kin faÉ—awa kowa ba kin ji my baby? Kada ki faÉ—awa ko Zunaira É—in ce ma, ki bari iya ke da ni zan rama maki abin da ya yi maki!". Girgiza kai ta yi. "Ni Momma ki bari in faÉ—awa Zunaira, ai ita ma ta faÉ—a mun da Hoorain É—inta ya sha bakinta"....... Ai momma bata san lokacin da ta zaro idanu waje ba, bala'in can, yaushe Zunaira ta iya dikka wannan abin? Yaushe aka yi hakan? Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Gaskiya King ya yi kuskure da ya hanasu mallakar juna, abin har ya kai haka?.

Tana can tana tinani Pretty zata gudu, kuma fa wajen Smart É—in zata koma dan yarinta, shi ne kawai zai kira mata Auta a waya ta kuma faÉ—a mata ya sha mata baki, kai kuruci dangin hauka.
"Zo mana my baby, baki san shi Yah Omerish É—in mijinki bane? Shi zai aureki ai! Kada ki faÉ—awa kowa abin da ya yi maki, ki rufe sirrinku". Momma ta faÉ—a mata hakan ne dan ta samu ta yi mata wayo kada ta faÉ—awa kowa, sai dai ina, taki fir, ta ce babu wannan magana, ita wlh sai ta sanarwa da Zunaira abin da yake faruwa.

Cigaba da lallaɓata momma ta yi, dan ta samu ta yi shiru, tasan idan ta ce zata yi abu to wlh sai ta yi ne, idan kuma ta ce ba zata yi abu ba ko me zaka yi mata ba fa zata yi ba, ai abin da kunya ta faɗawa Auta ga babban yayansu ya yi mata kiss, haba zata zubawar da Smart mutunci................😅

To shi ɗan air me ya kai shi dama, ko da yake ba laifinsa bane, laifin Prettyn ce, ƴar rainin wayo sai ta rinƙa yi mashi abubuwa, ta godewa Allah ma da abin ya tsaya a iya kiss, badan yana da dauriya ba yadda suke da gadan abar ai wani canza ake ba wannan ba, in ba iskanci irin nata ba ina ruwanta da cibiyarsa? Dan ta saba yi wa Kamran haka, shi Kamran a lokacin da take yi mashi ai kunga bai ma san me feeling ba, time da ya fara jin feeling ya sanar da mammarsa kuma ai kunga kashe mashi sha'awar ta yi da magunguna, ko kun manta lokacin? Saboda ma kada ya shiga haɗari ya yi ciwo tasan babu mata a forest ɗin shiyasa take bashi magungunar kashe sha'awa, wannan yasa dik abin da Pretty take yi mashi baya jin komai bawan Allah, amma Smart fa? Ai kunga da banbanci, dole idan ta yi mashi ya yi mata...........🥱😅

Da kyar momma ta shawo kanta ta hanyar yi mata alkawarin cartoon na kayan zaƙi, sannan ne ita ma ta yi alkawarin ba zata faɗawa kowa ba, ajiyar zuciya momma ta sauke kafin ta miƙe haɗe da riko hannun Pretty ɗin ta ce da mom tana zuwa bari ta duba Smart. Da okey mom ta amsa, bata jin larabci bata ji me suka tattauna da Pretty ba.

Bedroom na Smart momma ta nufa da ita, a parlourn ta ce mata ta zauna bari ta zo, da okey ta amsa tare da zama saman sofa tana turo baki ita kaÉ—ai kamar wadda aka yi wa wani abin. Ciki momma ta wuce, yadda Pretty ta bar shi haka momma ta shigo ta samesa, idanunsa a lumshe, da alama tashi jarabar ta fi ta kowa, har sallama momma ta yi mashi amma bai jita ba, hankalinsa ya yi nisa sosai.

A saman bedside drawer ta zauna tare da kai hannu ta É—an shafi lallusan gashin kansa. Nisawa ya É—an yi ba tare da ya yi magana ba, sai dai ya waro idanunsa da suka kaÉ—a suka yi jajir kamar wuta. "Omerish". Momma ta ambaci sunansa cikin sanyin murya, bai iya amsa mata ba, sai dai ya É—an juyo da kallonsa a kanta, sai a lokacin ya farga da Pretty bata a cikin É—akin, a hanzarce ya yunkura ya gyara zamansa yana É—an wawwaigawa nemanta!.

"Bata nan ta fita". Momma ta bashi amsa, dawo da kallonsa a kan mommar ya yi, da yake shi ba kunya ne da shi ba, renon masu jajyen kunnuwa sai ya ce. "Momma ta je ta faÉ—a maki na yi kissed É—inta ko?"....... Jinjina mashi kai momma ta yi alamar e, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To ina take ta zo muci abinci". Ya faÉ—a yana kawar da kallonsa daga kanta.

"Tana parlour, amma yanzu dai ba wannan ba, idan kun kammala cin abincin sai ka É—auketa ku je ka siya mata cartoon na kayan zakin da na yi alkawari, sannan ina da magana da kai". Juyowa gareta ya yi. "Kayan zaki kuma a daren nan?". Kai ta jinjina mashi alamar e kafin ta É—aura da cewa. "Sai da na yi mata alkawarin kayan zaki sannan ta yarda ba zata sanar da kowa abin da ka yi mata ba".

Da mamaki ya ja É—an siririn tsaki haÉ—e da cewa. "To me a ciki momma dan ta sanar da na yi kissing É—inta?"......... Momma bata yi mamakin jin hakan ba, dan tasa daga ina ya fito, ba ruwansa da wani kunya. Kawar da zance ta yi da cewa. "To ni dai ina san kuje ka saya mata kayan zaki". Ita dai momma tasan kunya, kuma tasan wannan ba magana ce da za'a fitar da shi ba, yana matsayin Prince ace Pretty ta fitar da wannan magana ai sam bai yi ba!
"Momma zakin nan fa cuta ce a gareta, baikamata take sha ba". Yana É—an É—aure fuska ya yi maganar. "For today dai ka saya mata". Shiru ya yi yana tinanin yadda zai yi ya rabata da zakin nan ya huta. "Omerish ". Ta ambaci sunansa tana kallansa.

Dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Na'am Momma".
Tattara natsuwarta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Omerish kana son Pretty, meyasa ba zaka yarda ka aureta ba kawai tin da ire-iren waÉ—an nan abubuwa sun fara shiga tsakaninku?".......... "Momma saboda na yi kissed É—inta ba shi ne zai nuna ina santa ba, kiss daban soyayya daban that's all!".

Shiru momma ta É—an yi, yana neman goge mata hadda, wato kiss ba wani abin bane, e lallai ma Smart, wato zai gaji babansa kenan!!.

"Na yarda kiss daban soyayya daban, amma kuma ai kasan haramun ne ka yi mata hakan ko?". Shiru ya yi bai bada amsa ba, babu kuma alamar zai yarda da zancen momma É—in ma.

"Please ka yarda ka aureta ga ji my son? Ina san yarinyar sosai, na tabbata zaka ji daɗin zama da ita, kuma nasan kana sonta kai ma......." Saurin katseta ya yi da cewa. "Ni bana sonta momma, ki dai'na faɗa mun haka".... Murmushi irin nasu na manya ta saki kafin ta ɗan girgiza kai, a ranta ta ce ta yaro kyau take bata ƙargo, a fili kuma sai ta ce. "Na yarda baka sonta, amma nikuma ai ina sonta ko?".

Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can kuma sai ya ce. "Momma please ki bari in yi dinner, am feeling hungry, ta ya za'ayi ki fara cewa in auri wannan ƴar yarinyar da na kai in haifeta". (Ku ji iskanci, wai ya kai ya haifeta amma a haka ya sha mata baki.🤔)

"Amma kuma ai dik da ka kai ka haifeta É—in zaka iya kissing É—inta ko?"........ Wani irin kallo ya wurga mata haÉ—e da cewa. "Mommaaaaaaa, zaki fara ko? Shiyasa jiya naki zuwa wajenki, saboda kada ki cigaba da kawo mun zancenta, ga mom ta dameni da zancen Heleena, so kuke yi in daina zuwa wajenku ko?.........." "Mom É—inka ai bata san ka rabu da ita ne shiyasa take son ka auri Heleena, kaga zaku kasance a tare, nima bana son ka rabu da ni shiyasa nike son ka da Pretty, please ka duba mu mana my son". Cikin tausasawa ta faÉ—a.

"Momma mata mayaudara ne, please ku kyaleni haka, ni bana da sha'awar wata mace ta shiga rayuwata a yanzu, Please kada ku katsa mun farincikina". Ya kai karshen maganar yana saukowa kasan bed É—in. Riko hannunsa ta yi da sauri, hakan yasa ya dakata a bakin bed É—in ba tare da ya karisa sauka ba. "My son meyasa yanzu baka son farincikina sosai ne?".
"Mommaaaaaaa, zaki fara ko?". "Gaskiya na faÉ—a ai". Kai ya girgiza. "Kenan kin san ina sanki kuma ina san farincikinki, kawai so kuke ku wahalar dani"....... "Haba my aboy".... "Mommaaaaaaa wai ba zaki manta da wannan suna ba?". Ya faÉ—a yana binta da kallon kauna.

"Sai ranar da matarka ta haifa mun jika zan daina ce maka sunan in mayar kansa, idan kana son na dai'na faɗa to ka yi aure ka haifa mun jika". Ta kai karshen maganar tana shafa kansa. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so kin san shi nike yi mommata, kuma farincikina, this time ki ɗan bani lokaci zan yi tinani, zan yanke hukunci"........... Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Okey tom amma ka yanke hukunci mai kyau, sannan ka rinƙa kulawa a zamantakewar da Pretty, kada ka zurfafa abubuwa"...... Ya gane nufinta, wato kada ya rinƙa taɓa Pretty har a kai ga kiss, ya gane in da ta dosa, sai ya miƙe kawai ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi wajen abincin nasa. Miƙewa momma ta yi ta nufi waje tana sanya mashi albarka.

Tana fita ta turo mashi Pretty, babu ko sallama ta afka mashi cikin ɗaki, alamarta ya gani ta wutsiyar idanunsa, bai ce mata ko uppan ba, a kusa da shi ta zauna tana kallan abincin. Tana zama ya kai hannu ya capki shoulder ɗinta haɗe da cewa. "Saboda na yi kissed ɗinki shi ne zaki kai karata wajen momma?". Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Saboda me zaka saka mun yawunka da babu zaƙi kuma babu daɗi? Kuma na goge bakinka da ya taɓa nawa tas, na tufar da yawun naka ma".
Chapter 225 · 0% Book details