← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 242

Sashe 150

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayansa Khadijah ta bi da kallo, take fuskarta ta bayyana alamar damuwa da rashin jin daɗi, gabanta faɗuwa yake yi a dik time da ta kalli uncle Jahiz. Kai tsaye part na momma ya nufa dan duba Zee a wajen. While shi ma Dr Raj yana can bedroom ɗinsa yana fama da juyi da tinaninta. Ita kuwa ta haye bed ɗin mama Haulat ta yi kwanciyarta, har da shigewa cikin bargo. My people's anya gaba ƙwaƙwalwarku zata iya ɗaukar cakwakiyar kingdom of power?......🤔

To kun ji abubuwan da suka faru bayan barin smart kingdom É—in, dan haka mu koma Paris É—inmu.
Auta ta buɗi baki zata wa Hoorain magana sai jin voice ɗin mace ta yi daga bayanta tana faɗin. "Wacece ke kuma?". A miliyan Auta ta juya dan ganin wacece? Ita dai tasan babu wata mace a gidan nan tun da suke zuwa, a nan suke sauƙa idan suka zo, Smart baya kaisu gidansu wajen mom ɗinsa, a nan suke zama, to bata taɓa ganin mace ko ta ji muryar mace ba, kuma wannan ba muryar Pretty bane gaskiya. To ko muryar waye?.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Wata kyakkyawar baturiya ce tsaye a kan kafafunta, tana nan dai cikin irin wannan shiga tasu ta turawa, ta zubo gashinta ta zaman shoulder É—inta ta gaba, ga wani shegen high heel a kafafunta mai tsinin gaske. From up to down Auta ta bita da kallo kafin ta ce. "Ke yakamata in yi wa wannan tambayar".

Tana kai karshen maganar ta cigaba da yin wayar da take yi. Cike da takun ƙasaita ta tako izuwa gaban Auta, hannu tasa ta kwace wayar dake hannunta, cikin zafa Auta tasa hannu zata kwaci wayar. Hatana ta yi tare da binta da wani kallan ƙasƙanci kafin ta ce. "Kin dai ɗan yi kama da baby, dik yadda aka yi kina da wata alaƙa da shi, amma hakan na shi ne zai sa na ɗaga maki kafa ba, ke har kin isa ina magana zaki cigaba da yin waya?".

Auta zata yi magana suka ji alamar an buÉ—e kofar parlour, to jinin sarauta dai ba karya ba, cike da izza ta ce. "Bani da lokacin shashasshu irinku, bani wayata". Kallna banza ta bita da shi, zata yi magana kenan suka ji muryan Smart yana kwala kiran sunan Auta, harara ta dallawa yarinyar kafin tasa kai ta wuce ciki.

A parlour ta iskosa yana zaune saman sofa, kusa da shi ta je ta zauna tana faɗin. "Yah Omerish gani nan". Kamar zata tambayesa wacece a gidan nan kuma dama akwai mace a gidan ne, sai kuma ta yi shiru, ranta a ɓace wancan mata katse mata waya da jaruminta. Hannunta ya riko cikin nasa, a natse ya ce. "Menene yake damunki?".

Wai a ina Smart ya baro mana gawar Pretty ne? Wato ko a jikinsa tun da ba Auta bace ta mutu ko?.

Da farko kamar Auta zata ɓoye mashi abin da yake faruwa, amma da taga bata da wani sauran hanya sai ta sanar da shi game da soyayyarta da Hoorain, da ɓatar da ta yi zuwa forest da taimaka mata da Pretty ta yi da komai dai dik ta sanar da shi, ta kai karshen maganar tana kuka dan ta tina irin soyayyar dake tsakaninsu.

Shiru Smart ya yi ba tare da wani yanayi ya bayyana a tattare da shi ba, kamar dai bai damu ba. Miƙewa ya yi tare da riko hannunta suka haura sama, sai sharar kwallah take yi, dama ga bakincikin an kwace waya an hanata yin magana da shi. Da alama Smart da King halayyarsu iri guda babu banbanci, amma my people's me kuke tunani ne, wai shin ya Smart ya yi da Pretty ne? To mu je dai zuwa, koma dai menene lokaci zai yi mana alkalanci.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Ummie and friend ɗinta hajiya two seater ne zaune a saman sofas a parlourn Ummie, yanzu hajiyar ta zo, daga gani kasan akwai abin da suke shiryawa, sai kuskuskus ƙasa ƙasa suke yi, hajiya two seater dai kusan kullun tana cikin nikaf matar nan, sai idan ta zo keta tsaron gidan Abbie ne securitys suke ce mata sai ta cire nikaf kafin ta wuce, dan su ga wacece, ko da kuwa Ummie ta yi masu waya ta sanar da su bakuwarta na zuwa, to basa barin ta wuce sai sun ga face ɗinta. Nikaf or face mask baya keta gate na farko na gidan Abbie, dole ka ciresa kafin ka wuce.

••••••••••••••••••••🔥

Jakarta ta buɗe ta ciro kwalin STENDRA guda ɗaya ta miƙawa Ummie tare da miƙewa tsaye, ƙasa ƙasa ta ce. "To ni zan wuce dare ya yi, yanzu ma ba dan saboda ke ba ba zan fito ba, ga sakonki nan, kada ki wuce saka mashi guda ɗaya idan ya yi yawa ne biyu dan gudun matsala a iya ganoki, dan yana da karfi fiye da tinaninki". Yadda take maganar tsab zaka fahimci wannan ta yi degree a iya munafurci da makirci.

Jinjina kai Ummie ta yi tare da miƙewa tsaye tana zuba mata godiya, sai uban murmushi take yi burinta zai cika. Gaba hajiya two seater ta yi tana kara jaddada mata kada ta wuce sanyawa Ramish wannan kwaya guda ɗaya kacal, dan yana da karfi sosai, daga karshe ta rufe mata da cewa idan ya sha da minti 15 zata fara yi mashi aiki, dan haka sai ta shirya. Ummie baki har kunne ta amsa da to. Har Hajiya zata fita parlourn Ummie ta yi saurin cewa.
"To ya batun Leesharh fa? Yakamata mu yi gaggawar kawar da yarinyar nan tin kan lokaci ya kure mana, kina ji dai ya faɗa maki Abbie yana tarayya da yarinyar nan a ɓoye, kuma ni ba zan iya jurar hakan ba". Ranta a ɓace ta kai karshen maganar.

Ajiyar zuciya hajiya two seater ta sauke kafin ta ce. "Kada ki damu, ai yanzu yazama wajibi mu ɓatar da Leesharh, idan ba haka ba zata zame mana babban barazana, amma kada ki damu zan dawo gobe dan jin result na maganin nan, a nan zamu tattauna maganar tata in faɗa maki hukuncin da muka yanke, amma kafin nan ki shiryawa Leesharh fita barin cikin gidan nan, kin dai san ba ta yadda za'ayi mu iya ɗaukarta a cikin gidan nan saboda mahaukatan tsawon nan naku masu sanya hantar cikin mutum ta kaɗa da kuke da shi, amma ki nemo wani aika ko wani dalilin da zai sa ta fita daga ita sai driver kawai".
Jinjina kai Ummie ta yi, har zuciyarta ya ayyana mata yadda zata aika Leesharh shopping ita da driver kawai ba tare da Sharifat ko bodyguards ba, tasan ta yadda zata ɓullowa komai.

Sallama suka yi ta raka hajiya zuwa wajen elvator, sannan suka yi bye bye hajiya tana yi mata addu'ar samun nasara a kan dikkanin burikanta.

Ciki Ummie ta koma, dama ita take haɗa mashi abinci dayawa lokuta, Sharifat mai kaiwa ce kawai. Da sauri ta nufi dry kitchen dan shirya mashi cappuccino, dan tasan zai buƙata. Sai dai fa, bata kai ga fara haɗawa bama sai ga Sharifat ta shigo cikin kitchen ɗin tana faɗin. "Ummie na je bedroom ɗinki bakya ciki, Yah Ramish yana san cappuccino"............ Wani irin faɗuwar gaba Ummie ta ji ya dira mata, sai ta ji shakkar saka wannan magani, amma da yake shaiɗan la'ananne ne sai ya fara kara mata confidence a kan ta jajirce zata yi nasara, har da raya mata ya yi cikar buri da biyan buƙata ya fi kwana masallaci, take ta ji kwarin gwiwa, cikin dabara ta ce.

"Okey zan haɗa mashi, amma jeki ɗaki ki jirani ina zuwa". Ta faɗa tana satar kallan cameras dake cikin kitchen ɗin. Da okey Sharifat ta amsa mata tare da juyawa ta komai ciki, tana sanye da jelly dressing. Kamar yadda ta saba haɗa mashi cappuccino haka ta haɗa yau ma, bata zuba maganin a cikin kitchen ɗin ba, saboda Cameras dake ɗaukarta, sai ta ɗauki cup ɗin ta fito waje. Kai tsaye bedroom ɗinta ta nufa, sai dai bata kai ga shiga ciki ba ta tsaya a wani ɗan corridor dake tsakanin parlour da bedroom ɗin, a wajen babu Camera kuma akwai ɗan duhu, a nan ta tsaya ta fito da maganin, a maimakon ta saka mashi guda ɗaya ko biyu kamar yadda aka yi mata kashedi, sai ta ɓallo guda huɗu ta banka mashi a ciki. Tsayawa ta yi har sai da maganin ya narke a ciki, sannan tasa spoon ta gauraya shi sosai, sai ta bar spoon ɗin a cikin cup ɗin.

Kana ganinta kaga maras gaskiya, amma da yake Sharifat yarinya ce sai bata iya fahimtar halin da Ummie take ciki ba, fargaba kamar zai kashe matar nan, amma saboda karfin hali sai dannewa take yi. Ta zo ta miƙawa Sharifat plate and cup ɗin, sannan ta wuce cikin toilet ɗinta tana jin kirjinta tamkar zai fashe saboda fargaba da tsinkewar zuciya. Ita kuwa Sharifat, karɓa kawai ta yi ta wuce abinta, zuciyarta na ta tuna mata Leesharh.

•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Zaune yake a cikin bedroom É—insa yana tinanin yadda aikinsa yake gudana, ga mama ta sako shi a gaba tana saka mashi pressure sosai a kan bayyanar Smart, ta matsa mashi wai sai ya yi mata bincike dan ita bata yarda Smart É—an King bane, wai sai dai momma saboda kwaÉ—ayin mulki ta hayo Smart a matsayin É—a.
Chapter 150 · 0% Book details