← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 242

Sashe 187

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bedroom ɗinsa ya fara leƙawa, bata a ciki, da sauri ya wuce bedroom na yayansa, yana ɗaure fuska a kan yau ba zai kyaleta ba. Sai dai ko da ya shiga bedroom na yayan nasa ma bata a ciki, babu ma kowa, ya ɗan yi mamakin ganin ba kowa. Har toilet ya leƙa bai ga kowa ba, da sauri ya fita ya haura sama izuwa gym area nasu ko ta maƙale a can. Sai dai bata a can ma, yawon nemanta ya hauyi, ton yana nemanta cike da burin ya ganta ya ɗauki fansa, har ya fara nemanta cike da damuwar ina ta shiga?. Wasa wasa har tsawon good 20 mins yana nemanta bai ganta ba. Da sauri ya sauko ƙasa dan ya duba harabar empeir ɗin, hankalinsa ya tashi sosai a yanzu kam, dan yasan empeir ɗin yana da wajaje daban daban, akwai wurare masu haɗari, akwai kuma wuraren da idan ta shiga tabbas ba zata iya fita ba, zama ta iya rasa ranta idan ta shiga, hankali tashe ya bazama nemanta.

A dai'dai wannan lokacin ita kuwa tana wata duniya ta daban, dan a lokacin da ta gudu ta haura sama, bedroom na Black Tiger ta nufa, saboda ta haɗa da sallama dik ta yi mashi na zata wuce school. Sai dai da ta shiga bata samu kowa a cikin bedroom ɗin ba, sai ta gudu balconynsa dan ta ɓuya a can, nan dai ta ga kamar a nan ma zai iya ganinta, hakan yasa ta dawo ta shiga dressing room, kun san nan akwai drawers da sauransu, so zata samu wajen laɓewa ba zai ganta ba. Sai dai kash, tana shiga suka ci karo da Black Tiger yana sanya kaya, yana tsaye a ta kusa da kofa wajen shoe set ɗinsa dake shirye cikin wasu mahaukatan glasses masu tsadar gaske, wani irin white light ne a cikin glases ɗin nan masu masifar haske da suka haskaka zafafan shoes ɗin nasa, yana san ya yi selecting na wanda zai sa ne, daga shi sai B- short wanda ko haɗaɗɗun cinyoyinsa bai gama kaiwa ba a jikinsa, tamkar dan iya penis ɗinsa aka yi short ɗin, Lion check ɗin nan nasa a buɗe, ya ɗaura wani small white towel a kansa, da alamar yana tsane ruwan dake gashin sa ne.

Aikuwa tana shigowa ta sauke kallanta a kansa, while shi ma ya juyo da kallonsa a kanta slowly, ya ji motsi ne yasa ya É—ago. Ai sumar tsaye ta yi, a zahiri kamar shi take kallo, amma kuma ina hankalinta ya yi nisa, kamar wadda aka daskarar!. Shi kuwa kallonta ya fara yi tin daga kan santala santalan cinyoyinta da suke tamkar madara har izuwa saman kirjinta da yanzu suka fara cika pam sosai, yanzu girma ya fara zuwa, matasan tula tulanta sun fara ciccikowa sosai. Ga yanayin uniform É—in nasu sai dai shiru, kun san ba addini ne da birnin ba, mini skirt É—in nata ko gwiwa bai rufe ba, a dai'dai tsakiyar tsala tsakan laps É—inta ya tsaya, daga sama rigar ma dai sai shiru, dan ya kamata sosai, har kana iya ganin shatin tula tulan, sai dai ita tana sanya jacket na school É—in dan suturta kayanta, amma yanzu dai bata sanya ba, saboda basu kai ga tafiya ba, dama idan zasu tafi ne take sakawa. Jacket É—in yana parlor tare da school bag É—inta!.

Wlh yau dai sai da ƙwaƙwalwarsa ta amsa, barema yadda yana skin ɗinta wajen cinyarta, tamkar ka latsa jini ya fita, tin ainahi dama babu abin da yake mugu mugun tafiya da shi sama da golden white hair ɗinta da idan ya sha gyara yake wani irin kyalli na musamman, sai ga shi yau ta sake shi ma bata ɗaure ba, dan bata kammala shirin tafiya ba, sai zata tafi school zata ɗauresa.

Me kuke tinanin zai faru da dikkansu suka bushe da kallan juna? Waye zai fara dawowa cikin hayyacinsa?.

🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥

Kiran farko na asuba ta farkar da shi daga ɗaddaɗar barcin da yake yi. A hankali ya waro fox-s eyes ɗinsa da suke jajir alamar barci bai ishe shi ba. Yunƙurawa ya yi ya miƙe zaune, jikinsa dik ciwo yake yi mashi tamkar ba lafiya ba, slowly ya waigo da kallansa ta side da take kwance. Ga mamakinsa sai ya ga babu kowa a wajen, wayam, ina ta yi to? Ya gefawa kansa tambaya, sai ya ji tamkar a mafarki ne dama ya kawota bedroom ɗinsa ba a zahiri ba. Miƙewa ya yi jiki ba kwari ya nufi toilet.

Jim kaÉ—an ya fito É—aure da white towel a kugunsa. D-room ya wuce domin shiri. Sanye da white arabs jallabiya mai bala'in kyau ya fito, sai ya kara fita a ainahin arabs guy É—in nasa, ya yi kyau sosai, sai tashin kamshi yake yi, yau dai kamar yana ji da mutumci, dan da ya gabatar da sallar rakatainil fajir sai ya É—auko alkyabba mai shige da na sarauta ya sanya a saman jallabiyar tasa, alkyabba ce ta manyan malamai ba ta sarauta ba, yau kuma ya koma gefensu Abu Abdussalam, wato ya yi shigar manyan malamai, har da rawani ya yi a kansa, ga dikkan alamu daga masallaci zai wuce wani wajen.

Bai je ya dubata ba, ya wuce ya fita bayan ya ɗauki wayarsa da car key. Ita kuwa, tsakiyar dare ta farka sai ta ganta a gado guda da shi, shi ne ta lallaɓa ta gudu bedroom nata zuciyarta cike da zargin ko ya yi mata wani abin ne, har da kara duba jikinta da kyau dan ta tabbatar, dik da bata ga wata alama ba, amma tabbas tana zargi dole ya yi mata wani abin, hakan yasa ta ji ta kara jin haushinsa sosai, ta tsanesa, dan tana ganin kamar halinsa ne neman mata kenan, amma fa ba har kasar zuciyarta ta yarda da cewa yana neman matan ba, kawai dai kokari take yi ta tirsasa zuciyar tata wajen ganin ta ɗaura mashi tuhuma dole dole.

Ko da ta koma bedroom ɗinta bata iya rintsawa ba, ta kwana cikin tinani da zilimin abin da yake faruwa, zuciyarta ya rinƙa ingizata a kan meyasa zata yarda ta zauna a gidan da daga ita sai namijin da ba muharraminta ba? Kuma ga abin da ya taɓa shiga tsakaninsu! Ai wannan ita da kanta ta kawo kanta, dan haka koma me yake yi mata ita ma da nata laifin, dan haka kawai ta gudu ta bar gidan nan shi ne mafita a gareta, idan ba haka ba za'a samu matsala, zata tabka danasani fiye da a baya, dan ita wlh babu batun yarda da aurensa a ranta, ba zata taɓa yarda ta auresa ba, Sharifat take yi wa kwaɗayin samunsa!.

Da wannan tinani da zulumi ta kwana har asuba, da kyar ta iya tashi ta yi sallah, sannan ta koma ta kwanta, tsawon kwanaki biyu tana ƙoƙarin shirya yadda za'ayi ta samawa kanta mafita ba tare da saninsa ba, dik iya binciken da take yi ta rasa samun mafita, idan ya fita baya nan har bedroom nashi take shiga ta yi ta yi mashi bincike, amma dik ta rasa samun mafita. A ɓangarensa kuwa, yana mamakin wanenne yake yi mashi bincike a ɗaki, dan bai taɓa kawowa ransa zata shiga bedroom ɗinsa bama bare har ta yi mashi bincike, ga shi kuma su biyu ne kawai a gidan, abin da ɗaure kai sosai, bai kawo komai a ransa ba, kuma bai tuhumeta ba, sannan kwana biyun nan yana ɗan busyn da baya samun wuni a gida, kazalika baya samun haɗuwa da ita sosai, wani lokaci kafin ya dawo ta yi barci, kuma yanzu garƙame door ɗinta with key take yi abinta, kun san zuciya da iya sake sake, tini ta saka mata wai idan ta yi barci yana zuwa ya yi amfani da ita, shiyasa ta dai'na yarda ta ci abincin idan ya sayo mata, sai dai ta girka a gidan, dan zuciya ya raya mata ai kila yana sanya mata maganin barci ta sha ya yi amfani da ita, ta dai kasa yarda da shi gabaɗaya!.

Yau garin an tashi da hadari sosai, iska mai daÉ—in gaske ne yake kaÉ—awa, hadarin ya yi bakinkirin, zaune take a bakin bed É—inta ta kurawa tvn dake fuskantar balconynta idanu, wata kyakkyawar balarabiya yar jarida ce take ta magana a cikin tvn, da alama akwai abin da yake faruwa, dan news dake fita daga bakinta gabaÉ—aya maganace a kan rashin zaman lafiya da suka tashi da shi a yau, ta natsu tsit tana sauraron matar. Sanye take da riga da wando arabs dress wanda zaku ga rigar ya kai mata har gwiwa, while wando kuma dogo ne wanda kasansa yake da faÉ—i. Ta É—aura silky headband milk color kalar kayan nata kenan a kanta. Ta yi masifar kyau sosai da sosai, fuskarta fayaw, kamar bata da lafiya, mood na face É—inta looks some how haka.

Lokaci guda ta ji kamar a takure take, tamkar dai akwai wanda yake kallanta, hakan yasa dik ta ji babu daÉ—i, ta jita a tsarge, cike da fargaba gabanta na faÉ—uwa ta juyo da kallanta a kan kofar shiwowa cikin bedroom É—in. Tsaye yake ya harÉ—e hannayensa a saman wide chest É—insa tare da É—an É—aure angry face É—insa, kamar dai shi ma his mood for today isn't good.

Bin sexy sleeping dress É—in jikinsa da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faÉ—i, gudun kada ya ganota yasa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa, tasan kwararrun jami'ai suna amfani ne da motsi da kuma idanun mutum wajen gano mai laifi ko mai gaskiya, dan haka sai ta yi juriyar zare kallanta a kansa, ba wai dan bata sha'awar ta yi ta kallansa ba, saboda kowa ya gansa sai ya sake kallah. Dan kawai ta kare kanta kuma ta tabbatar da shirinta. TO ME TAKE SHIRYAWA KENAN? HAR DA WANI TA TABBATAR DA SHIRINTA!.
Chapter 187 · 0% Book details