← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 242

Sashe 51

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turɓune fuska ta yi, tana turo baki ta ce. "Yau ba zan yi magana da kai ba". ........ "But why?"....... Ya yi maganar dai'dai lokacin da yake tsugunnawa a gabansu. Hannu ya kai ya ɗauki lemu mai ɓawo guda ɗaya daga cikin kwandon gabansu. Cikin nitsuwa ya fara ɓare lemun yana satar kallon Auta ta wutsiyar ido.

"Ba kai ne kace ba zaka sake wuce kwana ɗaya baka zo garemu ba, amma yau ka kai kwana biyar baka zo ba". Cewar Pretty sarkin mita da raki. Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Tana kai karshen kuma ta miƙe da sauri ita a dole ta yi fushi zata tafi ta basu waje. Sak dai yadda take yi wa Kamran idan ya ɓata mata rai ta yi fushi.

Cikin zafa ya yi saurin riko hannunta, Pretty tana bashi ciwon kai da shegen shagwaɓa da saurin kukan nan nata, ga shi bata jin lallashi da wuri............. "Haba my baby, to ki yi hakuri ba zan sake ba, kuma nima ai ba dan san raina nike rabuwa da ku ba, idan da dan san raina ne ba zan rabu da ku ba ai, ina san kasancewa daku sosai, amma bani da damar yin hakan, kiyi hakuri kinji rigimammiya kawai"................. Dik maganganun da yake yi idanunsa a kan Auta da take ta binsu da kallo, ita dai Pretty ta shiga ranta sosai, tana burgeta bare ma idan tana yi wa wannan sadauki shagwaɓa, sosai take jin daɗin kallonsu a tare.

Kuka Pretty ta saka mashi wai dan ya ce mata rigimammiya a karshen maganarsa, shikenan ya sake jijjigo wata rigimar............ Dan dolensa ya gyara zama a kasan wannan bishiya, ya É—aura Pretty a saman laps É—insa ya hau rarrashi.

A saman kirjinsa ta kwantar da kanta tana turo baki ita a dole ranta ya ɓaci........ Cigaba da ɓare lemun hannunsa ya yi yana satar kallon Auta, da yake face ɗinsa a rufe sai iya idanunsa ne kawai a buɗe, idan ka gansa zaka yi zaton lemun yake gani, amma Zunaira yake gani, ita kuma tana ta kallon Pretty da ta gama tafiya da imaninta.

Shiru wajen ya ɗan yi na ƴan sakanni da ya kammala ɓare lamun, sai ya rabata kashi huɗu, Pretty dake zaune saman laps ɗinsa ya ɗauki ɗaya ya sanya mata a baki yana dawo da ainahin kallonsa a kan face ɗinta.

Buɗe bakinma Pretty sai ta ja mashi aji sai kuma ta yi shagwaɓa, amma haka ya jirata ta gama shan kamshinta kafin ta ɗan buɗe mashi bakin nata, shi ma kaɗan ta ɗan buɗe.

Tura mata lemun ya yi yana dawo da kallonsa a kan Auta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, wasu zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta, ba komai ya ja hakan ba face abin da yake yi wa Pretty ya tuna mata da ita da guyson, ta yi kewan ƴan uwanta sosai, ba dan sadauki yana kula da ita yana rarrashinta haɗe da kawar mata da damuwar da take ciki ba wlh da bata san ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi ba, bata taɓa rabuwa da ƴan uwanta ko nan da can ba sai a dalilin Hoorain, wannan abin ba zai taɓa gogewa a ranta ba har abada.

Kanta a ƙasa, bai san hawaye take yi ba, sai ya ɗauki lemu guda ɗaya cikin wanda ya raba, bata yi zato ba sai ganin hannunsa ta yi yana ƙoƙarin cusa mata lemun a bakinta. Da sauri ta ɗago kanta, karap suka haɗa ido, ya ɗan yi mamakin ganinta tana kuka, ita kanta Pretty ta yi mamakin hakan.

Tashi ta yi daga saman laps É—inta ta koma kusa da Auta, É—an rungumota ta yi tana faÉ—in............ "Allah sarki meyasa kike kuka kuma Æ´ar uwa?".

Shiru bata amsa masu ba, ita kaÉ—ai tasan me take tinani, ita kaÉ—ai tasan raÉ—aÉ—in da yake cikin ranta.

"Omnish jeki ki kawo mun maganinta kin ji?"............ A faÉ—a a sanyaye. ÆŠan zaro idanu Pretty ta yi, a É—an tsorace ta ce. "Ciwonta ne yake yi mata zafi?".

Kai ya gyaÉ—a mata a alamar e, hawayenta Pretty ta fara share mata, cike da tausayawa ta ce. "Ki yi shiru ki dai'na kuka, In Sha Allah ciwonki zai yi sauki, yanzu zan kawo maki maganinki, amma ki dai'na kuka, bana san ganin kina kuka"......... Oh Pretty sarkin iya tsara zance idan ta yi ra'ayi, in bata yi ba kuma sai ka yi zatan wawuya ce ko kurma.

Jinjina mata kai kawai Auta ta yi ba tare da ta yi magana ba, goge mata hawayen da ƴan hannayenta Pretty ta yi kafin ta miƙe da sauri ta nufi makwancinsu dan ta ɗauko maganin.

Tana tafiya ya matsa kusa da Auta sosai, dama wayo ya yi wa Pretty ta tafi shiyasa ya ce ta je ta É—auko mashi magani, idan ya matso ya ce zai É—aura Zunaira a kan cinyarsa ko wani abin makamancin haka kuka Pretty take yi ta ce ai kafarsa nata ne ita kaÉ—ai shiyasa ya yi mata wayau ta tafi.

Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta, shi kansa sai da ya ji wani irin abu ya tsaya mashi a makoshinsa mai wuyar haɗiyewa. Kallanta ya yi ido cikin ido, gabansa ne ya ji ya fada dum dum haka. Ɗayan hannunsa yasa ya fara goge mata sauran guntun hawayen dake face ɗinta, cikin sanyin murya can ƙasa ƙasa ya ce.

"Kin manta cewa kin mun alkawarin ba zaki sake zub da hawayenki a banza ba ne?".

Shiru bata iya amsa mashi ba, sai ma ji da ta yi kamar ta tashi ta gudu a wajen, dan dai yana da girma da kima a idanunta wanda ba zata iya yi mashi abin da zai ɓata mashi rai ba ne yasa ta danne, ba za kuma ta taɓa manta halaccinsa a gareta ba. Ƴar Halak kenan.

Ganin bata yi magana bane yasa ya sake matsawa kusa da ita sosai, a hankali ya ɗan rungumota da nufin ya yi mata rarrashi irin wanda yake yi wa Pretty. Dik da yake sadauki sai da ya ji wani irin shock a jikinsa, kamar wanda aka jonawa lantarki, har sai da ya ɗan saketa jin abin da bai taɓa ji ba. Amma kuma yana san ta yi shiru kuma ta yi mashi magana, dan haka sai ya daure ya sake rungumota a jikinsa, yana jin wani irin bakon yanayi haka ya daure ya fara rarrashinta tare da tuna mata da alkawarin da ta yi mashi a kan ba zata sake yin kuka ba.

Dan dole ta haÉ—iyi kukan nata, saboda ya iya rarrashi sosai, ko da yake dik wanda zai rarrashi Pretty ta yi shiru lallai ba shakka ya iya rarrashi, dan Pretty sai Allah.

Murya can ƙasa ƙasa haɗe da kuka ta ce.
"Ka yi hakuri ba zan sake ba". Da yake tana kuka sai voice ɗin nata ya yi tamkar a shagwaɓe ta yi maganar, ba ƙaramin ɗarsa wani abin a ransa wannan magana tata ya yi ba.

Ƙasa sake yin magana ya yi, wannan sadauki ya shiga yanayi, abin ku da ba'a saba ba, an saba da datse kan mutane da takoba, ba'a saba shukan fure ba, sai ya zamana kaman wani ɗan fari a gabanta, ya hau aikin binta da ido kawai, daga ta yi mashi shagwaɓa sau ɗaya shikenan ya birkice.

(Anya ba zamu kai sadauki wajen Yah Jawad ya koya mashi karatun shuka flowers ba kuwa my people's?🤔😅🌝)

Jin ya yi shiru bai amsa taba yasa ta yi tinanin ko dai ransa ne ya ɓaci yaki sake kulata, dan haka sai ta kara marairace murya, a wannan karon cikin shagwaɓar gaske ta ce......... "Na yi alkawarin ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri, kaga ma na goge hawayena". Ta kai karshen maganar tana kai hannunta saman fuskarta.

Haba tuni sadaukinmu ya kara shiga yanayi, kamar ba shi ba, sai ya ji kamar an canza shi ne lokaci guda, ya kasa iya yin magana.

Allah sarki ta zaci fushi yake yi, sai ta kai hannunta ta riko nasa hannun, kamar zata saka kuka ta shiga bashi hakuri. Dik sai kara rikita shi take yi, da kyar ya iya samu ya juya hannunta ya koma cikin nasa, a hankali ya furta ta yi shiru dan Allah ta dai'na magana, dan tana kure tinaninsa.

A dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta É—auke da sak irin kwaryar da aka basu magani a lokacin da suke jarirai, ganinta yasa ya yi saurin sake Zunaira ya É—an ja baya kaÉ—an.

Karɓar maganin ya yi Pretty ta zauna kusa da shi, a gefensu ya ajiye ba tare da ya bawa Auta ba, Pretty bata nemi jin meyasa bai bawa Autan ba, sai ta kwanto jikinsa ta fara aikin zuba mashi shagwaɓa da ta saba.

Haka suka kasance cikin farinciki suna hira yana satar kallon Auta na tsawon lokaci, har sun shagala sun mance da zai tafi sannan ya kawo masu batun lokacin tafiyarsa ya yi. Kuka suka saka mashi su biyun dikka, Allah sarki wlh basa san zama su biyu a cikin wannan kungurmin dajin, amma to ya zasu yi? Dole su hakura dan sadauki dai bai san ƙasarsu Gimbiya Zunaira ba, ita ma bata san ta ina take bama bare tasan in da garinsu yake, ba hanyar komawa.

Hakuri ya rinƙa basu yana rarrashinsu har sai da ya samu suka ɗan nitsu, sannan ya rakasu har sabon bakwancin da ya yi masu ya kuma ƙawata masu shi, bai mayar da Pretty ainahi in da suka taso a tare da mom ɗinsu ba, ya canza mata waje, har yau har gobe kuma yana wahalar neman Sweetie, ba dare ba rana, dayawan lokuta idan ya shigo forest ɗin kafin ya je in da su ke sai ya yi ta kewaye a cikin dajin yana neman Sweetie, kun san na gaya maku kungurmin daji ne mai girman gaske, yana da ɓangarori da dama, idan kana wannan ɓangere ba zaka taɓa zatan akwai mutane a wani ɓangare ba saboda nisan dake tsakani.

So kullum a cikin daji yake yawon neman Sweetie, bai taɓa kawowa ransa bata a wannan dajin ba.
Chapter 51 · 0% Book details