← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 242

Sashe 107

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mota ya zo ya buÉ—ewa yaran super market É—in suka jibge mashi niki nikin kayan da ya saya, sannan ya dawo ya shiga gidan gaba. Kunna motar ya yi da gudun gaske suka nufi school, dan ta yi latti. Dik bayan minti sai ya juyo ya kalleta, tabbas ya fahimci fushi take yi da shi, amma bai kulata ba saboda saurin da suke yi.

Bai dakata a ko'ina ba sai a cikin katafaren parking space na school ɗinsu, yana yin parking ya sanya hannu a gidan baya ya ɗauki ƙaramin lada daga cikin shopping da ya yi ya miƙa mata. Kin karɓa ta yi a in da ta sanya hannu zata buɗe kofar motar ta fita, ita dai ta yi fushi da shi.

Zuba mata ido ya yi yana kallanta har ta buÉ—e kofar ta fita, bai hanata ba kuma bai yi magana ba, cikin nitsuwa ta fara takawa ta nufi barin parking space É—in, ko kyafta idanu daga kanta ta gagara yi, kallanta kawai yake yi.

Sai da ta ɗan yi nisa, sai kuma ta dakata cak da tafiyar tata, da sauri ta juyo garesa, ganin ita yake kallo yasa ta yi saurin dawowa garesa. Yana dai kallanta bai motsa ba, ta side ɗin da yake ta zo ta buɗe kofar motar tana huci irin na shagwaɓa.

A saman laps ɗinsa ta zauna, hannu tasa ta ja dogon hancinsa da karfi har sai da ya furta wash, ƙara ja ta yi tana faɗin. "Shi ne ba zaka rarrasheni ba, kuma kasan na yi fushi, amma shi ne kake kallona zan tafi baka rarrasheni ba ko? To ba kai ka ɓata mun rai bane?".

Daga ganin idanunsa zaka fahimci yana cikin yanayi, dik jikinsa a mace, idanunsa sun sauya sun yi ja, sai faman lumshe su yake yi, da kyar ya iya riko hannunta da take ta faman jan dogon hancinsa da shi, can ƙasan maƙoshinsa ya furta.

"Ba zaki iya yin fushi da babynki ba ai, shiyasa na zuba maki idanu ina kallanki, na san zaki dawo ai rigimamma kawai". Ya kai karshen maganar yana janyota ta faÉ—a saman kirjinsa.

"To yanzu na bada hakuri kuma na yi rarrashi, baby ya bada hakuri ko?". Ya sake faɗa ƙasa ƙasa yana kallan face ɗinta. "Ni wannan hakurin ya mun kaɗan, sam ban yarda ba, sosai zaka rarrasheni". A shagwaɓe ta yi maganar.

Kamar mai raɗa ya ce. "To na yarda rarrashin ya yi kaɗan, kuma zan yi mai yawa, amma sai kin dawo daga school, anjuma da daddare zanzo sai na yi rarrashi mai yawa kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa bayanta. Ɗago kanta daga saman kirjin nasa ta yi. "Promise me first!". Ta yi maganar tana miƙo mashi tafin hannunta.

ÆŠaura nasa tafin hannun a saman tata ya yi, sannan ya ce. "I promised you that zan zo da daddare in yi rarrashi mai kyau".

Siririn murmushi ta saki tare da matsawa kusa da shi ta manna mashi sumbata a lallausan kumatunsa, ƙasa ƙasa ta ce mashi take care, sannan ta yunkura zata fice daga cikin motar. Rikota ya yi jikinsa dik a mace, a hankali ya ɗan matseta a jikinsa kafin ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Sumbata ya bata a kumatu shi ma yana mai faɗa mata ta kula da kanta sosai. Daga haka ya ɗauki ledar chocolate ɗinta na ɗazun da taƙi karɓa ya miƙa mata yana kallanta.

Karɓa ta yi da sauri ta fito daga cikin motar, da kallo ya bita tana tafiya har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da dawo da kallonsa ga makunnin motar. Da kyar ya iya tasarta ya nufi gida wajen Ammo da shopping ɗin da ya yi.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

GabaÉ—aya hall É—in tsit suka nitsu saboda tsoron bomb É—in, gabaÉ—aya yawan jami'an dake wajen sun tsaya cak, kowannensu idanunsa a kan Ramish dake kasa ya kasa É—ago kansa, saboda wani irin É—aci da ransa ya yi mashi.

Bilal yana tsaye a kusa da Abbie, saboda ya razana shi ma ya miƙe tsaye kafin mutanen can su yi barazana da bomb ɗin.

Wani irin tsawa mutanen suka daka a kan wai Ramish ya miƙe tsaye, har da cewa shi kaɗai suke da buƙata a taron nan, su basu zo nan da nufin su cutar da kowa ba, shi suke san ɗauka, in yana san cetan ran jama'arsa to dole ya tashi ya bisu. Ajiyar zuciya Ramish ya sauke kafin ya yunkura ya miƙe tsaye.

Yana miƙewa suka sake daka mashi tsawa a kan ya sauko kasan stage ɗin ya ƙariso gabansu ya zube gwiwowinsa a ƙasa..... Babban magana!!.

Ko kaÉ—an bai damu da abin da suke faÉ—e ba, hankalinsa bai tashi ba. Slowly ya kai kallansa a kan Leesharh dake kwance jininta na zuba tamkar an buÉ—e hanyar ruwa. Ta wutsiyar idanunsa ya kai kallansa a kan Bilal wanda shi ma shi yake kallo.

Blinking eyes ɗinsa Ramish ya yi sau biyu, da alama magana ce tasu ta jami'ai, dan kunsan suna karɓar irin wannan horo ta magana da gaɓɓan jikinsu saboda shiga matsala irin wannan sai su yi magana ba tare da sanin kowa ba su fahimci junansu.

Jinjina kansa Bilal ya yi tare da dunkule hannunsa sai ya sake warewa. Yana warewa Ramish yasa hannu cikin zafa a aljihun Suit É—in jikinsa kafin kowa ya ankara ya zaro pistol gun, a tare suka zaro shi da Bilal.

Mutanen suna ganin haka sai suka yi ƙoƙarin danna bomb ɗin su kunna, sai dai kafin su yi motsi Bilal da Ramish suka harbesu a tare lokaci guda, Ramish ya harbi ɗaya Bilal ma ya harbi ɗaya a goshinsu. Tare suka zube ƙasa, ashe kallan da Ramish ya yi wa Bilal maganar da suka yi kenan, abin da yasa suka yi haka kuma shi ne idan Ramish shi kaɗai ya ce zai harbesu kafin ya harbi ɗaya ya sake harbin ɗayan to ɗayan zai kunna bomb ɗin, dole a tare za'a harbesu idan ana san kowa ya tsira.

Suna harbinsu gabaÉ—aya jami'an dake wajen suka yi kansu da gudu dan su duba bomb É—in a kunne yake ko a kashe yake. Mayar da gun É—insa cikin aljihunsa Ramish ya yi, juyawa ya yi ya da nufin ya isa ga Leesharh kamar walkiya haka Bilal ya rigasa isa gareta. Bata numfashi kamar rai ya yi halinsa ne.

Cak Bilal ya É—auketa jami'ai uku suka rufa mashi baya izuwa wajen motocinsu, shi kuma Ramish ya haÉ—a kan family sannan ya bawa jami'an su umarni da su wuce mashi da waÉ—an nan mutane h-q zai bi ta kansu amma ba yanzu ba, bari ya gama da case dake gabansa na Leesharh tukun nan, zuwa anjuma idan ya tabbatar da Leesharh bata mutu ta dalilinsa ba zai zo ya binciki mutanen.

Hankalinsa ya tashi sosai, ya kuma yi mamakin yadda aka yi Leesharh tasan za'a harbesa har ta sadaukar da nata ran a kansa! Dik yadda aka yi tasan wani abin, dan haka in dai bata mutu ba zai tsaya ta samu lafiya ko dan ya samu wasu amsoshi daga bakinta.

Kunsan dik taurin zuciyar mutum in dai aka yi mashi irin sadaukarwar da Leesharh ta yi mashi wlh dole zuciyarsa ta raunata ta kuma sassauta, to shi ma hakan ne, sai da ya ji wani iri a ransa, tambaya É—aya yake yi wa kansa shi ne meyasa Leesharh ta bada ranta ta ceci shi?. Wannan ne babban damuwarsa.

HaÉ—a kan family ya yi suka nufi gida. Da gudun gaske motocinsu suka danna cikin gida, sai kuka Sharifat take yi kamar ranta zai fita, ta shiga damuwa da tashin hankali sosai. Ummie kuwa addu'a kawai take yi Allah yasa Leesharh ta mutu.

Suna shiga gida tun motocin basu gama yin parking ba Bilal ya fito da gudu ya buÉ—e gidan baya ya É—auko Leesharh a saman shoulder É—insa, cikin zafa Ramish da Dr Raj suka rufa mashi baya, dan su dubata. Da sauri shima Abbie and Sharifat suka fito suka rufa masu baya.

Kai tsaye a&e É—insu suka nufa da Leesharh. Hankalin Bilal idan ua kai miliyan a tashe yake a zahiri, amma bamu san me yake a cikin ransa ba, shin tashin hankalin me ma yake yi, yana damuwa Leesharh ta mutu ne ko kuma yana damuwar ta bada ranta ta ceci Ramish? To wannan dai dik bamu sani ba.

A tare Dr Raj da Ramish suka shigo cikin room ɗin. Bilal yana ƙoƙarin sanya karfi ya yage rigar jikin Leesharh Ramish ya dakatar da shi. Da mamaki suka dawo da kallonsu a kan Ramish ɗin. Dr Raj ya yi mamakin ganin yadda Bilal ya tashi hankalinsa sosai har ya rasa control saboda Leesharh, sai kace wata tasa ta jini ko da akwai wata alaƙa a tsakaninsu! Abin da mamaki, tabbas yasan Bilal mutum ne mai tausayi, amma ya nuna san Leesharh sosai wanda sun san ba halinsu bane.

Cikin nitsuwa Ramish ya tako ya kariso bakin bed É—in da Bilal ya kwantar da ita, in a cool voice ya ce. "Rai'na ta ceta ta shiga haÉ—ari, dan haka da kai'na nima zan cetota daga haÉ—ari". Yana kai karshen maganar ya buÉ—e drawer dake kusa da bed É—in, cikin zafa ya kwaso kayan aikin cire bullet irin su. Irrigation Syringe, Retractors, Suction, Machine Forceps, Scalpel, Local Anesthesia, X-ray Machine, Sutures, Sterile Gauze Pads, Antiseptic Solution.

A gaban bed É—in ya zo ya zubesu saman wata tables dake ta gefe dai'dai in da kanta yake.

Su Abbie da suka shigo yanzu ne suka tsaya cirko cirko suna kallansa yana aiki cikin zafa da kulawa.
Almakashi ya fara É—aukowa, rigar jikinta ya yanke tin daga farko har karshe, ya tsaga rigar biyu kenan, wani farar vest wadda ta ji jaga jaga da jini ne ta bayyana a ciki. Saman breast É—inta kaÉ—an bullet É—in ya sameta, hakan yasa ya yanke iya hannun vest É—in kawai. A saman table É—in ya mayar da almakashin ya ajiye.
Chapter 107 · 0% Book details