← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 242

Sashe 30

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dik wani bawa da yake jin kamar wata musifa tana tinkaro shi, yana yawan jin faÉ—uwar gaba to ga addu'ar da zai yi wanda zai sa Ubangijinmu ya juya wannan abin zuwa alkhari, in ma kaddararsa ce ta zo a haka to Allah zai saukaka mashi abin ya zo mashi da sauki, zan rubutu maku addu'ar da hausa dan ina samun korafi a kan rubuta shi da larabci da nike yi, wasu basu iya karatun larabci ba, so addu'a addu'a ce koma da wace yare ka yi ta Allah zai jika, gata kamar haka haÉ—e da fasararta dik na haÉ—a na rubuta maku da Hausa dan ku fi fahimta da kyau, Allah yasa mu dace.

"Hasbiyallahu laa ilaaha illa Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Azeem."
Fassara. Allah Ya ishe ni, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, a gare Shi na dogara, kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma, shi kaÉ—ai zai iya kareni daga dik wata sharri.

Sai cikin Alqur'ani mai girma, Suratul Baqarah Surah ta 2 bayan Fatiha kenan, aya ta 286. Wannan ita ce aya ta ƙarshe a cikin Suratul Baqarah, kuma tana ɗaya daga cikin mafi girman addu'o'in Al-Qur'ani don neman gafara, rahama, da taimako daga Allah, wannan addu'a idan kika yi ta bata da shamaki da isa ga Ubangiji, kika yi ta da tawali'u ki kaddara addu'aki ta karɓu kawai, dan bata da shamaki kai tsaye take wuce zuwa ga rabbil izzati, ita ce addu'a kamar haka.

"Rabbanaa laa tu’aakhidhnaa in nasinaa aw akhṭa’naa. Rabbanaa wa laa taḥmil ‘alainaa iṣran kamaa ḥamaltahu ‘ala-l-ladheena min qablinaa. Rabbanaa wa laa tuḥammilnaa maa laa ṭaaqata lanaa bihi wa’fu ‘annaa waghfir lanaa warḥamnaa anta Mawlaanaa fanṣurnaa ‘ala-l-qawmi-l-kaafireen."
Fassara. Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu idan mun manta ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana nauyi kamar yadda Ka dora wa waɗanda suka gabace mu. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana abin da ba za mu iya ɗauka ba. Ka yafe mana, Ka gafarta mana, Ka jiƙanmu. Kai ne Majiɓincinmu, Ka taimake mu kan mutanen da suka kafirta suke binmu da sharri.

Addu'a ta uku a kan Allah ya kareki daga dik wata masifa da kike jin kamar tana tinkaro ki shi ne.
"A‘oozu bikalimaatillahi-ttammaati min sharri ma khalaq."
Fassara. Ina neman tsari da kalmomin Allah masu cike da kamala daga sharrin duk abin da Ya halitta.

Manzon Allah (SAW) ya koyar da wannan addu'ar don neman kariya daga kowanne irin sharri, so addu'a ce mai karfin gaske, idan kika riketa wlh wane mutum sai dai ubangijin mutum!!!.

Addu'a ta huɗu kuma mafi tsada, wannan addu'a idan kika yi ta da safe kafa uku, Manzon Allah ya yi rantsuwa a kan babu wata sharri da zata sameki, safe da yamma ake yi, in kika yi ta uku da safe wlh a wannan wunin ranarkam babu wani sharri da ya isa ya kusantoki, dik balai'n mutum nan zai ganki kuma yarbi, Allah zai saukar da Mala'iku daga sama domin baki kariya wunin wannan rana har zuwa yamma, in kika sake yin kafa uku da yamma to fa har zuwa washegari da asuba kina cikin kariyar Ubangiji. Sai dai ki sani addu'a babu cikakkiyar Tauhidi fa Allah baya karɓarta, sirrin addu'a ita ce idan zaki roƙa ki sanya a ranki cewa Allah ya gama biya maki buƙatar ma kawai, ki sa a ranki dama babu wanda zai biya maki sai shi!!.

Ga addu'ar kamar haka.

"Bismillahil-ladhi la yadurru ma’asmihi shai’un fil-ardi wa la fis-sama’i wa Huwa-s-Sami‘ul-‘Alim."
Fassara. Da sunan Allah wanda ba zai yiwu wani abu ya cutar da mai ambatonsa ba a sama ko a ƙasa, kuma Shi ne Mai ji, mai sani a kan komai.

A karanta sau uku safe da yamma, domin samun tsari daga sharrin duniya gabaÉ—aya!. Allah ya cigaba da karemu daga dik wata sharri!.

WaÉ—an nan addu'oi Momma take ta karantawa dan ta samu saukin abin da take ji, hakan ne ma yasa mutuwar Zunaira bai yi mata wani tsananin tasiri ba, Allah ya dafa mata zuciyarta ya É—an sanyaya dalilin wannan adduoi.

Guyson na shigowa ya haye saman gadon, kusa da ita ya matso, tana kwance idanunta a sama, jin motsinsa yasa ta É—an yi kasa da kallonta izuwa kansa.

"Lafiya Omar?". Ta yi maganar da kyar.

"Momma jikina ne dik yake mani some how na kasa ganewa, and kaina yana É—an sara mun, kamar bani da lafiya".
Tin da ya fara magana idanunsa suka cicciko da kwallah, dama kun san halinsa mai kukan ciwo ne, da zarar ya fara ciwo zai fara kuka. Allah sarki babu juriya!.

Yana kai karshen maganar kuma ya kwantar da kansa a saman laps É—inta yana shirin fara yin kuka mai gabaÉ—aya.

Miƙewa ta yi zaune a tsakiyar bed ɗin, hakan ya bashi damar kara gyara kwanciyarsa a saman laps ɗin nata.

Daidai lokacin King ya fito sanye da jallabiya ruwan hoda a jikinsa, sai tashin kamshi yake yi.

Ganin Guyson nasa a saman bed É—in ga kuma hawaye a face É—insa yasa ya kariso da sauri yana tambayar ba'asin meyake faruwa?.

Yana ganin King ya kara rushewa da kuka mai ɗan sauti, kukan shagwaɓa har da shessheƙa.

Hankalin King ne ya kara tashi, dama shi bai wani san halinsa sosai ba, dan in baku manta ba girman Dubai ne shi, Momma ce tasan kayanta tsab, dan haka bata wani rikice sosai ba, dan tasan a kan ɗan buge hannu a jikin bangoma guyson kuka yake yi bare azo ga ciwon kai ko ciki, ai sai ya wuni yana kuka!. Sakalene.........😅

A hanzarce King ya haye saman bed É—in yana kara tambayarsa me yake faruwa?. Ya yi maganar tare da kai hannu yana É—an É—agosa daga jikin momma.

Ai tin bai gama kai hannu jikinsa ba ya miƙe ya faɗo jikin daddyn nasa yana kara tsara kukan shagwaɓar tasa da kyau, har da hawayen iyashege!.

Kallon momma da bata wani damu sosai ba King ya yi. "Rahilarh lafiya? Me kika yi mashi?". A rikice ya yi tambayar.

"Wai jikinsa ne yake yi mashi ciwo shi ne yake kuka".............. Ta bada amsa tana kai hannu zata taɓa gaban goshinsa.

Zaro idanu King ya yi, ya kara shiga damuwa. Muryarsa har tana É—an sarkewa saboda saurin wajen furta magana ya ce. "Miko mun wayata bari in kira Dr ya zo".

Ganin yadda ya rikice ya tashi hankalinsa haka abin ya ɗan bawa momma mamaki, dan ita tasan halin kayanta, a ganinta yanzu haka idan aka bincika ba wani ƙwaƙƙwaran ciwon da yake damunsa.

"A'a dare ya yi, ka bari sai zuwa da safe se mu kai shi hos........"
Wani irin cin burki ta yi a maganar tata bata karisar ba, ba komai ya ja hakan ba kuma face zaro mata idanu da King É—in ya yi.

Cike da mamaki ya ce. "Rahilarh kin san me kike faÉ—a kuwa? Mu bari sai da safe fa kika ce?".

Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa da yes hakan ta ce.

"Amma lallai Rahilarh baki san me bakinki yake faÉ—e ba, kinfa san Omar tun yana karamin yake fama da ciwon ciki, kuma kin san yanayin tsananin azabar da yake sha idan ciwon nan ta tashi, ba godiya zaki yi wa Allah ba da yasa yau ciwon ta tashi har yake iya yin magana? Ai hamdala zaki yi ki kuma yi gaggauwar taimakawa wajen kiran Dr dan sauki ya fara samuwa, amma sai ki ce mu barshi sai da safe, Omar É—in nawa?".

Momma dai bata wani damu ba, ta miƙa hannunta ta ɗauko wayarsa dake saman bedside drawer ta miƙo mashi tana ce mashi.

"Allah ya huci zuciyarka ranka ya daÉ—e, ga wayar".

Karɓa ya yi da sauri, yana rarrashin guyson, number Dr ya shigar dan ya kirasa ya zo ya duba mashi ɗan lelensa.

Sai binsu da kallo Momma take yi, guyson yana kara narkewa haɗe da kukan shagwaɓa.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Babban Dr na hospital É—insa King ya kira, cike da bada umarni ya ce dik abin da yake yi ya bari ya yi maza ya zo gida Omar É—insa bashi da lafiya.

Cikin girmamawa Dr ya amsa da In Sha Allah ga shi nan zuwa yanzu.

Katse kira King ya yi ya hau rarrashin guyson babu kama hannun yaro, kun san irin wannan yanayi da zasu ga mutum ya yi kasa gane me yake yi mashi daÉ—i irin hakan sam babu daÉ—i, sai ka ji a takure kake a duniya.

Momma jiki dik a mace sosai, komawa ta yi ta kwanta tana tunanin meyake faruwa da ita ne haka?.

A haka Dr ya zo part na King ya samesu, da yake kowa ya san Drn King ne sai babu wanda ya tare mashi hanya, suka bashi dama ya shiga har tsakiyar parlon, sallama ya yi haÉ—e da dakatawa a wajen.

Kallon guyson da kyau King ya yi. "Tashi mu je Dr yana parlour ya duba mun kai".

Kai ya fara girgizawa, yana kuka ya ce. "Ni daddy bana san Dr ya dubani, ya tafi kawai".

"Meyasa to?". King ya jefa mashi tambayar.

"Bana san ya yi mun allura, ni dai gaskiya ya tafi zan ji sauki". Yana magana yana kara tsananta kukansa.

Lumshe idanunta Momma ta yi kamar mai jin barci, dama ita tasan idan ba Dr Raj ba babu mai iyawa guyson, Dr Raj ma sai in su Ramish suna nan ne zaku ga ya yarda ayi mashi allura, nan ma yana kwance jikin É—aya daga cikinsu suna É—auke mashi hankali sannan ake yi.

"Dr ba zai yi maka allura ba, i promised you that".
Chapter 30 · 0% Book details