Sashe 6
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗan zaro idanu Floris ta yi tana kallon Ronnie, ta ji sabon karatu yau. Shi ma Ronnie zancen Sweetie ya taɓa zuciyarsa, dan haka ta wutsiyar idanu ya kalli Floris while ainahin kallonsa yana a kan Sweetie, tabbas har cikin ransa ya ji yana son sanin wannan Allah da manzonsa da idan ka riƙesu ka bi umarninsu ba zaka taba shi damuwa ba, dik wahalar da Sweetie ta shiga, ga makanta dik, uwa uba aka rabata da ƴar uwarta, ga rashin iyaye, dik bata taɓa shiga damuwa ba dan ta rike Allah da Manzonsa, dik azabar Black Tiger bai ɗaga hankalinta ba saboda ta rike Allah, hakika zai so shi ma ya san ta yadda zaka bi ka rike Allah har ka more haka, sai dai kuma da kamar wuya in dai yana Black world.
"Ya kayi shiru Ronnie?". Cewar Sweetie.
Girgiza kai ya yi ba tare da ya furta uppan ba, amma abin ya bashi matukar mamaki kuma ya ratsa zuciya da gangar jikinsa, sai nanata kalmar idan ka rike Allah da manzonsa, ka yi imani da su ba zaka shiga damuwar komai ba, Allah ba zai bari ka ji kunci ba, sai nanatawa yake yi a cikin ransa yake yi, like wow abin ya ƙayatar da shi ba kaɗan ba.
"Ronnie zaka je wasa ne?". Floris ta jefa mashi wannan tambaya.
Kai ya gyaÉ—a mata ba tare da ya yi magana ba, da alama jikinsa ya yi weak sosai, bawan Allah ya ji É—aya daga cikin karfin ubangijin gaskiya!!.
Idanunsa a kan Sweetie, ita ma tana rike da wayarsa da ta karɓa daga hannun Floris dan ta gani, amma kallonta da nutsuwarta na'a kansa, Allah Ronnie ko baka son ganin kowa in yana waje sai ka ji sha'awar ɗaura idanunka a kansa, saboda kyau, sai ma idan yana murmushi tare da ƴanmatansa.
Ga shi ya karyawa Delisha kafa tana can tana jinya, wato Ronnie ma fa mugune wata sa'an, yanzu haka ta fara samun sauki tana koyan takawa da sanda, amma ta ji a jikinta kam, ta gane annabi Isa ba É—an Allah bane manzon Allah ne Æ´ar banza.
"Ronnie zan bika wajen wasan ka ji?". Cewar Sweetie.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Zo mu je, time ya cika, tun da kuka zo gidan nan ke da Floris kullum nine bayan shiga wajen wasa".
Murya a kasale ya yi maganar.
"Meyasa to?". Sweetie ce ta jefa mashi tambayar.
"Saboda biye maku da nike yi mana, kullum nine karshe".
Floris ce ta karɓi zancen da cewa. "And you're a winner everyday ba".
Kashe mata ido É—aya ya yi alamar haka ne zancenta. "To kuzo mu je".
Ya faɗa yana miƙa masu hannu.
Kusan a tare suka kariso gabansa, wayarsa dake hannun Sweetie ya fara karɓa ya zura a aljihu kafin ya kama hannayensu, suka nufi waje.
Sai daɗi Sweetie take ji yau, hakika tana da karfin tawakkali da imani da Allah Sweetie, ta yadda da kaddara mai kyau ko maras kyau, bata sanyawa kanta damuwa ko kaɗan, idan ta tuna kuncin dake cikin rayuwarta, cikin sauri take tunano girma da niimomin da Allah ya yayi mata, hakan yakesa ta mance ƙuncinta, mu koya daga gareta domin mu ji daɗin gudanar da al'amuranmu cikin nutsuwa, mu kuma kara karfafa imaninmu!!.
Sosai filin wasan skaternsu yau ya cika, matasa sai gwada baiwarsu suke yi, ga Æ´an gasa sun shirya tsaf, tsabar kaunar wasan da Ronnie yake yi, yanzu haka yana kammala karatunsa zai shiga wasannin duniya gabakiÉ—aya bisa yardar Black Tiger, ya yi mashi hakan ne dan ya faranta mashi ransa sosai.
Kowani matashi yana gwada baiwarsa, babu nuna ragonta, dik sun tsaya tsayin daka dan nuna jarumtarsu.
Saman ƙayatattun kujeru na musamman ya zaunar da Floris and Sweetie wanda tun shigowarsu wajen idanun kowa yake a kansu.
Saboda kaunar wasannin Ronnie yasa Black Tiger ya gina masu wannan stadium É—in, dik dan farincikin kanin nasa.
Tin da ya sako kafafunsa cikin wajen jama'a suke ihun sunansa da ɗaukar tafi da hannayensu, ji kake fito ya karaɗe ko'ina, da alama suna murnar zuwansa sosai. Ya saye zuƙatan kowa!.
Sai da ya sumbaci kumatun Sweetie and Floris sannan ya juya ya shiga fili, nan fa tafi da fito ya kara yawaita sosai.
Master Devil ne ya bashi skatersa ya sanya a ƙafafunsa, dik wajen nasa takalmar ce kawai ta fita daban, dan haɗuwa da tsadarta ya wuci tunaninku, dik takalmar wasanninsa da ɗanyar gold Black Tiger yasa aka kyara mashi su, kunga kuwa ai bazama ayi zancen tsada ba, dan akwai kuɗi kam.
Zuba mashi idanu su Sweetie suka yi suna ta kallonsa, shi ma idanunsa yana a kansu. Ƴan wasa gabaɗaya sun tsaya layi kowa jira yake yi su fara, sai fito ake yi.
Wani katon warriors wanda ya ji horo ya ƙoshi ne ya hura masu usir dan a fara wasa. Tafi da karfin sautin fito ne ya kara karaɗa wajen.
Floris ma tafi ta fara yi tana faÉ—in Ronnienta ne winner. Ganin tana tafi yasa Sweetie ma ta fara yi, yanzu dik abin da Floris ta yi ita ma sai ta yi.
Kun san wasan skater kusan yana tafiya ne da zuciyar mutum, kamar gudun doki ne, idan kana a kan doki, to gudunsa ya ta allakane da yanayin bugawa da gwazon zuciyarka, shi ma haka yake.
====================💘🔥
Ko gargada Ronnie bai taɓa yi a wasan skater ba, sai ga shi yau saura kaɗan ya yi wani mummunar faɗuwa Black Tiger ya tare mashi da magic ɗinsa, ba komai ya haifar da hakan ba kuma face Sweetie.
Suna tsaka da tafi ita da Floris suna kallonsu suna nishaɗi, kwatsam sai ta nuna takalmar ƙafarsa da yatsanta tana tambayar Floris amma takalmar Ronnie na gold ne ko?. Dan ta gansa yana kyalli sosai.
Wannan nuna shi da yatsa da ta yi unexpect magic É—inta ya fita, baiwar Allah sam bata ma san yadda zata sarrafa magic É—inta ba, dan bata san da shi a tattare da ita ba, in dai zata nuna abu da hannu to da wuya idan magic É—in bai fita ba, kuma a iya hannun hagunta ne abin.
Wani ɗan siririn haske ne ya fita daga hannun nata kai tsaye sai kan takalmar Ronnie da ta nuna hasken ya nufa, hakan ya haifar mashi da tuntuɓe, da yake Black Tiger yana ganinsu ya ga magic ɗin nata, ya kuma yi sauri ya tare shi, amma dik da haka da yake nata yana da karfi sosai sai da ya sa Ronnien tuntuɓe kamar zai kifa ƙasa, da ya faɗi kuma za'ayi mummunar faɗuwa, saboda ƴan wasa dayawa suna biye da shi a baya, da dik zasu faɗi, wasu su faɗi a kan junansu.
Dayawan mutanen dake wajen sun sha madarar mamakin ganin Ronnie ya yi tuntuɓe, sai dai ba wanda ya ga dalilin hakan, shi kansa ya ɗan yi mamaki, dan dai wajen flat yake babu wani gargada, to me ya sanya shi wannan tuntuɓe? Ya jefawa kansa tambaya.
Yana can yana wannan tunani har wasu Æ´an wasa biyu suka tsere mashi ba tare da ya farga ba, sai da ya ji ihun Floris tana ambatar sunansa ne ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka.
Cikin tafasar jini ya fara gwabza wasan, kafin wani É—an lokaci ya wuce waÆ´an can.
A lokacin da Æ´an wasan can suka wucesa har sai da damuwa da rashin jin daÉ—in hakan ya bayyana a saman face É—in sweetie, Allah sarki bata san ita ce sanadi ba.
Shiru Black Tiger ya yi yana tunanin meyakamata ya yi domin cire magic dake jikin Sweetie? Dan in ba haka ba watarana zata iya zama ajalin Ronnie ba tare da sun sani ba, ko da bai rabata da magic ɗin ba ya zamana shi yake sarrafa magic ɗin nata, dan tsaro, ita bata san da shi a tattare da ita ba, zata yi ɓarna sosai a dalilin hakan.
Can wani zuciya ya ce mashi. "To ai kila saboda magic É—in nata ne yasa aka ce ita ce zata kawo karshenka!".
Tuna hakan yasa ya kara É—aur wanna fuska mai kama da hadarin, dan in kuwa hakan ce da wuya ya iya sarrafa magic É—inta, tunani ya fara yi a kan wacece ita ma tukun nan ? Ina asalinta yake? Wani shafaffe da mai ya bata magic?. WaÉ—an nan sune tunanin dake ransa!.
Ni dai bana tunanin mahaifiyarsu Sweetie ce ta bata magic, domin kuwa mom ɗinsu baiwar Allah ce mai riƙo da addini, ga shi har ta koyar da su karatun addini da har suka koyawa Kamran ga shi yanzu tana karantar da Ronnie girman Allah, kun ga kuwa mom ɗinsu mutuniyar kirkice, da wuya ta koya masu tsafi.
Dik yadda aka yi ko dai mahaifinsu ne ko kuma wannan sadauki mai taimaka masu É—in, akwai dai cakwakiya da sarkakiya mai É—aure kai, to Pretty ma tana da shi ne ko dai iya Sweetie ce kawai?.
Da alama kuma ita ma Sweetie sai da ta haɗu da Black Tiger ne magic ɗinta ya bayyana, dik yadda aka yi magics ɗinsu yana da alaƙa ko dai wani abin makamancin hakan!!.
Lokacin da Ronnie ya matso kusa da su sai da ya kashe masu ido É—aya. Fito mai sauti Floris ta saki, ita kuma Sweetie da bata iya fito ba sai kawai ta sakar mashi murmushi tana cigaba da yi mashi tafi.
A karo na biyu ta sake cewa Floris. "Amma skater kafar Ronnie da gold aka yi ta ko?".
Kai Floris ta gyaÉ—a tare da cewa. "Yeah, da gold yaya yasa aka yi mashi".
Ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin yadda suke facaka da gold, bayan kuma Ronnie ya gaya mata irin tsada da darajar da gold yake da shi, amma a haka suke abin da suka ga dama da shi, bata san arzikinsa Allah ya yi masu ba, a tunaninta saya suke yi, hakan yasa take kara jinjinawa karfin arzikinsu.
Da gudu Floris ta miƙe ta nufi cikin wajen wasa, da idanu Sweetie ta bita tana mamakin ina zata je to?.