← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 242

Sashe 223

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai su momma suka karɓeta hannu bibbiyu, momma ma ai sai zama yar kallo ta yi a tsakanin Smart da mom ɗinsa, dan kuwa ya tare a wajenta abinsa, kafin ya je wajen momma sau ɗaya ya je wajenta sau uku, kun san zuciya bata da ƙashi, sai momma ta fara danasanin kai mashi su da ta yi, tana ganin kamar ya fi son mom ɗin tasa a kan ita da ta haifesa, bata san ba haka bane, shaƙuwa ce kawai, kada ku manta tun yana jajiriri fa, mom ɗinsa ita ta yi mashi komai, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da ita, momma fa time to time take zuwa wajensa, a shekara sau ɗaya take zuwa idan ta samu damar zuwa Dubai gaisuwar azumi, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da mom ɗinsa, amma batu na so da kauna ai baya haɗa momma da kowa, it kaɗai ce babu ta biyunta!!.

Zaune suke a parlourn momma, da momma da mom É—in nasa suna hira, nan momma take cewa mom ta yi wa É—an nata magana ya yi aure mata. Murmushi mom ta yi kafin ta ce. "Ai baya son yi, ta kyalesa sai time da ya yi ra'ayi, ga shi nan Heleena tana can tana haukar sonsa amma yaki kulata".

Jim momma ta É—an yi, dan tasan Heleena da ake magana a kai, sai bata ce komai ba, dan kada ta ce wani abu mom ta ce bata son familynta.
A can gefe kuma King ya gama sanar da uncle Abbas cewa yana nemanwa Smart auren Sareena, dan sun dace, uncle Abbas kuma ya ce Allah ya basu zaman lafiya, wato ya bashi kenan, uhm yau ake yinta. SAREENA ZAƁIN KING GA SMART, HELEENA ZAƁIN MOM ƊINSA, PRETTY ZAƁIN MOMMA, wa kuke tinani zata zama zaɓin Smart kuma?........

Suna tsaka da hiran sai ga Sareena ta shigo cikin part ɗin, tana san ganin Smart ɗin ne, ta jima tana san ganinsa bata samu dama ba, shi ne ta daure ta zo part ɗin momma ko yana ciki, tana tsoron zuwa room ɗina. Yau dai tana sanye da abaya har ƙasa, sai dai da alama shegen shigar tata ta yi daga ta ciki.

A saman carpet ta zauna tare da ɗagawa su momma gaisuwa kamar wata ta Allah. Fuska ba ya bo ba fallasa momma ta amsa. Shiru ta yi tana tinanin me zata ce ne ta samu bayani a kan Smart, shin yana gidan ne ma ko baya nan, ta ƙosa ta ji. A daidai wannan lokaci mama Haulat ta shigo ɗauke da abincin Smart cikin wani luxury tray na alfarma.

Duba time momma ta yi, karfe 8:30 na dare, kallon mama Haulat ɗin ta yi. "Lokacin cin abincin nasa ma ya yi, bari mutuniyar tasa ta zo ta kai mashi"....... A saman table mama Haulat ta ajiye abincin tare da juyawa ta nufi waje. Jiki na ɓari Sareena ta ce. "Momma abincin Yah Omerish ne?". Kai Momma ta gyaɗa mata alamar e. A hanzarce ta miƙe, jiki na ɓari ta ce. "To bari in kai mashi momma". Oh ta samu dalilin zuwa in da yake!.

"A'a Sareena, Omerish bai aminta da kowa ya kai mashi abinci ba face Pretty, ko su Jaish ya ce baya so, ita kaɗai ya yardanwa, kuma kin san dokace ma ta wannan gidan ba kowa yake kaiwa Prince abinci ba sai wanda ya naɗa da kansa kuma ya amincewa". HAKIKA DOKARSU CE HAKA, BAMA ABINCI BA, BABU WANDA YA ISA ZUWA KUSA DA SMART A MATSAYINSA NA PRINCE MAGAJIN MULKI IDAN BA WANDA SHI DA KANSA YA YARDANWA BA KUMA KO ABINCIN DA ZAI CI SAI AN TANTACETA SOSAI, KO ITA PRETTY DA YA AMINTA TA RINƘA KAI MASHI ABINCI BA TA ISA TA KAI ABINCIN KAI TSAYE BA, DAGA KITCHEN SAI AN TANTACE KOMAI TSAB AN TABBATAR BABU WANI ABIN CUTARWA SANNAN TA WUCE TA KAI MASHI.

Shi da kansa ya ce wa momma bayan Pretty bai yarda da kowa ya taɓa abincinsa da sunan zai kawo mashi ba, yana jin daɗin cin abinci da ita shiyasa ya ce ita zata rinƙa kawo mashi, saboda su ci a tare, kun san Pretty da shiririta da sakalci, idan suna cin abinci tana sanya shi nishaɗi da har ya ci abinci sosai ba tare da ya sani ba, yana mugu mugun son kasancewa a tare da ita, sai ta kai karfe 1 na dare a ɗakinsa, yana aikin bincikensa a kan familynsa, ita kuma tana zuba mashi shirme tana bashi nishaɗi, wani lokaci sai ta yi barci a bedroom ɗin nasa, sai ya kammala abin da yake yi zai mayar da ita nata ɗakin, a tare suke kwana da Mahreen a part na momma, to nan yake kaita idan ya tashi kwanciya barci.

Da momma ta ce to ya auri Pretty É—in mana kawai sai abin ya fi bada armashi, sai cewa ya yi shi bai ce yana sonta ba ai, kawai dai yana jin daÉ—in kasancewa da ita ne, tana É—ebe mashi kewar Zunaira tana kuma saka shi nishaÉ—i.

My people's anya kuwa kun yarda da Smart? Wai tana saka shi nishaÉ—i! Ina team É—in Pretty, kada ku yarda zai lallata maku É—iya, in ba iskanci ba ka aureta É—in mana, zaka wani ce nishaÉ—i take baka!.

Wani irin ɗaure fuska Sareena ta yi, ranta ne ya yi maki, kamar zata sake yin magana sai kuma ta yi shiru, ta zauna tana jin tamkar ta haɗiyi zuciyarta......... Tsabar sakalci irin na Pretty ko sallama bata yi ba ta afko cikin parlourn, tana sanye da sleeping dress white color, riga ne da wando dogo, ta saki gashin nan har baya, Momma ta yi ta yi da ita ta rinƙa ɗaura ɗankwali amma yarinyar nan taki fir. Tana turo baki ta zo ta zauna kusa da momma, sarkin son jiki har da kwantowa a jikinta tana shagwaɓe fuska. Momma tasan halinta sai cewa ta yi. "Yunwa kike ji ko?".

Kamar zata yi kuka ta amsa da e yunwa take ji!. "To ai ga abincin yayan naku, tashi ki je ki kai mashi sai kuci kamar da kuka saba". Cewar momma.. ita dai mom da bata jin larabci sai binsu da ido kawai take yi bata san me aka faɗa ba. Jin momma ta ce ta tashi ya ɗauki abincin Smart ne yasa Sareena ta gane e lallai wannan ita ce Pretty da ake ta magana, binta da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, saboda tsantsar madarar kyau da ta kallah, tasan babu abin da zata gwadawa Pretty sai rashin kunya wanda bata san cewa shi ma Pretty number ɗaya bace, sai dai idan ba'a zo ɓangaren ba!.

Ziciyarta ne ya cigaba da kara ƙawata mata kyan Pretty, tinani ta fara yi a kan me zata yi mata ta rabata da Smart, ya zamana ma ko inuwarsa ba zata sake gani ba, bama ta san wacece Pretty ko yar wacece ba, ita dai tin da ta ganta a part ɗin momma sai ta zaci ko daga cikin ƴan uwan momma na Dubai take!. Tana can tana tinane tinane bata san lokacin da Pretty ta ɗauki abincin Smart ta fita abinta ba, sai waigawa ta yi taga babu abincin kuma babu ita ma Prettyn. Siririn tsaki ta ja wanda ta manta a gaban momma take.

Miƙewa ta yi ta nufi waje, a cikin ranta tana faɗin lallata kyan Pretty kawai zata yi shi ne mafitarta, zata ɓata mata fuska kaca kaca ya yi damage ta yadda kowa zai ji kyamarta. Tana fita ta nufi part ɗinsu Omaid dan su shirya wannan mugunta a tare, dan ta rantse ba zata bar Pretty ba.

Ita kuwa Pretty kai tsaye ta wuce bedroom É—insa, babu ko sallama ta afka ciki abinta, yana zaune a saman bed É—insa sanye da sleeping dress kalar na jikinta sak, dama shi ya saya mata tin a France, so su uku suka yi ankonsu, shi da ita da Auta, yana rike da wayarsa suna chat da Ramish yana jin ya lafiyar Auta a yanzu. Ta wutsiyar ido ya kalleta, tin É—azun tinaninta ne a ransa, yana tina yadda zata kare da azumi gobe, anya zata iya yi kuwa? Bata fa shiri da yunwa, ga shi gaskiya girma ya fara zuwa, kirjinta sun cicciko, period kawai ya rage ta fara yi, dole ma ai ta yi azumi, sai dai za'a sha fama kam, bala'i tab zai fi kowa fama da ita, dan daga shi sai momma take jin maganarsu. Tin É—azun yake ta tinanin mafita a kan azumin.

Ajiye masu abincin ta yi a saman carpet ta nufo shi, a gefen bed É—in ta zauna tana tura baki.
"Bana ce ki rinƙa yin sallama ba? Kuma bana ce idan kin zo ki rinƙa gaishe ni ba?". Ya gefa mata tambayar yana cigaba da katsa wayansa.

Unexpected ta faɗo jikinsa tare da sanya mashi kuka tana faɗin. "Yah Omerish wai mama Haulat ta ce gobe za'a fara azumi babu ni babu cin abinci sai dare?". Tana kukan kuma dan iyashege tana tura hannunta a cikin rigarsa ta kasa, so take ta taɓa cibiyarsa, wai ita da yake yi wa faɗa a kan saka ɗankwali da yin sallama, shi ne ta kwanta a jikinsa take yi mashi wannan sakalci da iyashegen, Pretty sai shirin Allah wlh, dama abin da take ta yi wa kuncin rai kenan, shi ne taki faɗawa momma ta zo tana juyeshi a nan, dan tasan ya fi kowa biye mata a gidan!

My people's me kuke tinani idan Sareena ta zubawa Pretty acid a fuska? Dan dai kun san su Omaid zasu bata goyan baya, uhm

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

58

Tsaye yake cikin arabs jallabiya milk color, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana aikin kai komo a cikin bedroom ɗinsa, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali gane da ciwo, tamkar ba King ɗinmu ba, ya rame matuƙa, ya yi wani irin haske sosai, sai idanu kwala kwala farare tas zaka gani, gabaɗaya a dabaybaye yake da damuwa.
Chapter 223 · 0% Book details