← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 242

Sashe 171

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yauwa ina da wata ƴar rokan alfarma a gareku my people's, kunga dai azumi ya zo, Please a taimaka a sakani a addu'a, wlh addu'a in dai ta alkhairi ce a gareni kowacce iriya ce ina so, please my people's, ina kannena da suke gida, ƴan yaran nan da basu wuce 10 ya yi ƙasa ba, please a sanyasu su yi wa princess taku ta amana addu'a, kun san addu'ar yara da karɓuwa yake, to a taimaka a mun wannan alfarma, dik wadda ta je ta hajju ta jefani cikin addu'arta, ina godiya Allah ya bar kauna 💘 🔥 💘 🤍 much love my people's, sai mun haɗe gobe.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

48

Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu kyawawan robbot ne gungu guda da a kallah zasu kai su 8, gabaɗayansu kowanne ɗauke yake da katan tray mai shake da kayan abinci kala kala, ga wasu irin abin rufe abinci wato food cover masu shegen kyau da tsada launin golden suna ɗaukar idanu aka rufe abincin da su, kai tin daga kan masu ɗauko abincin zaka fahimci robbot ne na musamman da zasu kaiwa mutum na musamman abinci, harta tafiyar da suke yi cikin tsari suke yinsa, a tare suke ɗaga kafafu su sauke.

Ai zuba masu idanu Sweetie ta yi tana kallan yadda suke taku gwanin birgewa, kai tsaye suka nufi can wani ɓangare na ɗakin, kun san ɗakin da shegen girma yake, wajen da yake cin abincin zaka yi zatan ba'a ɗakin yake ba saboda girmansa. Sweetie bata kara tsurewa ba har sai da suka yaye white curtains dake wajen, ai wani irin zaro idanu ta yi tana kallan tsaruwar dining room ɗin, kun san a baya Black Tiger baya fita, hakan yasa yake da haɗaɗɗen dining room a cikin bedroom ɗinsa bayan na parlournsa. Sweetie ta sha madarar mamakin ganin set na table ɗin dake ciki, haɗaɗɗun chairs har guda 24 ne a wajen, ko shi da waye yake zaman cin abinci yawan chairs har haka? Ta jefawa kanta tambaya, my people's dining room ɗin nan ya haɗu, ga wasu decorations masu ɗaukar hankali, manya manyan flowers da kayan more rayuwa, sai dai kuma kusan dik da ɗanyan gold aka yi su, yo Black Tiger da WC ɗinsa ma na gold ne me ba zaku gani na gold ba?..... Shi dai wannan sarki wlh sai shirin Allah.

Glass wall ne wajen, haka zalika glass door ne, tura kofar suka yi suka shiga ciki, shi kansa table ɗin abin kallo ne, ya tsaru matiƙa, samansa suka hau shirya mashi abinci kamar yadda suka saba. Suna kammala shirya komai suka kunna ligh launika daban daban dake wajen bayan sun kashe white light ɗin, take wajen ya ɗauki wani irin launi mai ɗaukar hankali, sai ma da suka kunna kenduran dake saman table ɗin, ya ilahi ya lilliahi, haɗuwa iya haɗuwa. Sweetie kam dai sumar zaune ta yi, sai taga tamkar ba a duniya wannan dining room ɗin yake ba.

Fitowa suka yi su 7 sun bar ɗaya a ciki, suka nufi waje ba tare da sun yi komai ƙanƙantar magana ba, da kallo Sweetie ta bisu tana mamakinsu, ita dai yau taga abin da ya goge mata hadda, tambayar kanta ma take yi ashe Black Tiger yana cin abinci? Abin like wow, ya ƙayatar.

Shi kuwa gaban mirror ya wuce, wasu document ya É—auka yasa hannu, takardu ne na katafaren ginin da za'ayi mashi a cikin empeir É—in, tamkar fadar sarki ne shi ma, tsarin ginin ya fi wanda yake ciki komai da komai, sai dai ya ce da zallar gold za'ayi mashi ginin, dan yana san zarce kowani sarki a mulkinsa.

Ni kam na ce mu da mun san tarihin sarkin romawa da su habashawa, a zamanin da manyan sarakunan da suka yi gidan ɗan yar gold a tarihi ma ai suna dayawa, amma yau ina suke? Sun koma ga Allah, to a zamanin nan ma mun samu King Black Tiger, ginin ɗan ƴar gold za'a zuba mashi, my people's yake kuke ayyana wannan gini a ranku? Ɗanyar gold fa? Tab Black Tiger zai tashi hankalin duniya, ai dole ne ma kowani sarki zai so kwace birnin daga hannunsa, ko dan tarin arzikin da Allah ya basu, aww ace fadarsa da komai na gold, dole hankalin duniya ya tashi, ga katafaren filin saukar jirginsa a saman ginin gabaɗaya, ginin dai ya tsaru matuƙa, a zamanin yanzu banda sarakuna da suka shuɗe kafin zuwan manzan Allah (SAW) a zamanin yanzu shi ne mutum na farko da zai yi irin wannan gini, abin dai ba'a cewa komai.

(Ni kuma na ce ya kuke tunani idan ya kammala wannan gini Sweetie ta zama Queen a ciki? Ronnie ya zama Prince? Su dake a fada su ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya suna zartar da hukunci irin na addinin musulunci, ya kuke ganin haɗuwar wannan sabon empire ɗin nasa zata kasance da waɗan nan taurari guda biyun a cikinta?.🤔)

Sai dai har yanzu bai sakawa sabuwar empire É—in suna ba, ya ce dai su fara kaddamar da ginin sai an kammala zai faÉ—i sunanta a rubuta a farkon shiga.... Amma kuna tunanin wani irin suna zai bawa empeir É—in nan?.

Yana kammala sa hannu a kan document ɗin, sai ya sanya hannu a kan wata takardar da ya umarci a biya dik mutanen birnin asarar dukiyar da aka yi masu a sanadin wannan yaki, waɗan da basu bijire mashi ba kuma suka rasa nasu a biyasu diyya na makuɗan kuɗaɗe masu zafi, sannan ya cike wasu takardu na sabbin ma'aikatan da yake san buɗewa na sarrafa abinci da abin sha wanda kowani ma'aikata ɗaya zai iya ɗaukar ma'aikata sama da 500, kunga ya ragewa mata zaman banza, kuma fa shi a ƙaidarsa maza basa aiki sai dai su tafi bakin daga, mata ke yi mashi aiki a dikka ma'aikatunsa domin su samu abin dogaro da kai tun da basu da maza da zasu wani ɗauki nauyinsu........ Yaseen Black Tiger shegen kwaro ne, wai yanzu kun yarda da batun Sweetie da ta ce tana da yakinin akwai abin da ya canza zuciyarsa daga fara zuwa baka? Kun yarda wani lokaci mutumin kirki ne shi, wani lokaci kuma bakin shaiɗani, sai ka rasa gane ina ne takamaiman alkiblarsa wlh, wani lokaci dai ga shi mutum, wani lokaci kuma kai bashi da kyan gani fagen mugunta.

Sai da ya kammala abin da yake yi tsab sannan ya nufi dining room ɗin nasa, da alama ya mance da ita a cikin bedroom ɗin. Wani robbot na tsaye a wajen yana jiran ya kariso ya yi serving ɗinsa. Sai da ta bari ya shiga room ɗin ta miƙe ta bi bayansa tana kara jinjinawa girman arzikin da Allah ya bawa birnin nan. Ba tare da neman izininsa ba ta shiga cikin room ɗin, wannan robbot na ƙoƙarin zuba mashi abinci ta yi gaggawar dakatar da shi tare da cewa. "Zan yi serving ɗinsa kada ka damu".

To kun san abubuwan nasa idan ya rigada ya basu umarni kawai zasu aikata abin da ya ce ne, dan haka wannan robbot ya riga ya karɓi umarnin yin serving ɗinsa, sai ya hanata ya cigaba da yin aikinsa, ba ta isa jayayya da Robbot ba, dan idan ta yi ma ita ce zata sha wahala shi babu ruwansa, dan haka sai ta ja chair dake kusa da shi ta zauna tana kallan face ɗinsa, ya ɗaure fuskar nan tamau yana tinanin gina katafaren football stadium saboda Ronnie, kun san yana sha'awar wasannin.

Kammala zuba mashi abin da ya buƙata wannan robbot ɗin ya yi tare da matsar mashi da plate ɗin gabansa. Chopping stick ya ɗauko guda biyu, zubawa abincin idanu Sweetie ta yi tana mamakin wannan wani irin abinci ne? Bata taɓa gani ba, a hankali ta fara bin sauran cimar da kallo, dik launikan abinci ne da bata san ma da me ake yinsu ba, ga wasu dai kamar nikakkun nama da kwai, wasu kuma kamar damammen shinkafa da yoghurt, abubuwa dai kala kala, baki ta taɓe tana jin ko kasheta za'ayi ba zata iya cin abincin Black Tiger ba, gara ma nasu Ronnie wanda ta sani ne.
Abin da bata sani ba anan shi ne, ta sha cin irin wannan abinci a hannun Kamran, kun san a lokacin bata gani shiyasa bata san irin abincin da yake bata tana ci ba, wlh babu wani banbanci tsakanin cimar mammar Kamran da na Black Tiger, dik irin ɗaya ne, sai dai nata local ne na talakawa, nasa kuma na manyan kai, amma dik iri ɗaya ne, amma har da cewa sun yi mata wani irin ba zata iya ci ba, bayan su ta ci ta girma har ta ƙosa ta yi kumatun da in ta yi murmushi suke birge big bro, eh manaaaaaaaaaaaa.😅

Ɗibar abincin ya yi da chopping stick, abincin wani ball ball haka ash colar, yana ƙoƙarin kaiwa ɗan bakisna cool voice ɗinta ya daki dodan kunnnesa in da take cewa. "Ka yi bismillah kafin ka ci". Ta yi maganar tana kallansa. Tamkar bai jita ba, kamar bai san da halittarta a wajen ba ya cigaba da ƙoƙarin sanya abincin a bakinsa. Cike da tsoro a gaggauce ta kai hannu ta rike hannunsa, kirjinta na bugawa da karfi ta ce. "Please say Bismillah before you eat.........".
Chapter 171 · 0% Book details