← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 204 OF 242

Sashe 204

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kaɗan bata yi ƙoƙarin taka mashi birki ba, sai ma hannunta ɗaya da ta ɗaura a saman faffaɗar kirjinsa, ta ɗaura ɗayan kuma a saman bayansa. Hot kiss ya shiga bata cikin salon da bai san ta ya aka yi ya iya bama, ita ma mayar mashi da martani ta shiga yi cikin salon soyaya mai kara narka zuciya, ai bai san lokacin da ya janyo waist ɗinta ta tafi gabaɗaya ta faɗa saman kirjin nasa ba, macewa suka yi da kissing na juna babu kakkautawa. Woooooo yau Hoonaira ta bawa heronta abin da ba zai taɓa mantawa ba, gabaɗaya ya fita a hayyacinsa, ya ƙanƙameta sosai sai juya tongue ɗinsa a cikin bakinta yake yi, abin mamaki, ko waye ya koya mashi kiss cikin salo har haka kuma? Shi da yake so silent bai san komai ba!.
Sai da ya sha lips ɗinta son ransa, ya gama yin musayan yawun bakinsu, sannan ya saketa yana wani irin numfashin da kana ji kasan yana a cikin tsananin buƙata, ƙasa iya yi mata magana ya yi, idanunsa a ƙasa ya yi mata nuni da kofar shiga cikin gida, alamar ta tafi da sauri tin kan shaiɗan ya cigalaba mai gabaɗaya a kansu wajen sanya shi ya aikata fiye da abin da ya yi. Ita kanta gabaɗaya jikinta tamkar an zare mata laka, bata da karfi ko kaɗan, da kyar ya iya jan kafafunta ta nufi cikin gida, ko sau ɗaya bata waiwayosa ba, shi kuwa, tana tafiya ya ɗago idanunsa ya tsareta da kallo har ta shiga ciki, lokacin da ta turo kofar nan sai ya ji tamkar kofar zuciyarsa ta datse, gabaɗaya sai ya ji tamkar an jefasa cikin kunci da matsi, da kyar ya juya ya nufi bedroom ɗinsa. Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinsa ya fara juyi dan samawa kansa sassaucin abin da yake ji.

Ita kuwa kai tsaye bedroom na Momma ta nufa, sai dai ko da ta je babu kowa, hakan yasa ta fito ya nufi wajen King, har zata shiga sai kuma ta fasa ta koma bedroom ɗinta. A lokacin Pretty ta jima da yin barci abinta. Saman bed ta haye tare da ɗauko wayarta, lokaci guda ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, gabaɗaya abin da ya faru a tsakaninta da shi ne ya dawo mata cikin kwakwalwarta, lumshe idanunta ta yi tana tariyo yadda ta ji tausasan lips ɗinsa wanda ta san babu wata mace da ta taɓa ɗanɗanawa sai ita, dama kuma mallakinta ne, shi da ko face ɗinsa ba a gani yaushe wata zata samu damar ɗanɗanar lips ɗinsa? Ai ba wannan magana, ita ce first and last in ji zuciyarta. Lokaci guda ta saki cool murmushi, bargon sanyin ne ya lulluɓe zuciyarta. Wayarta ta janyo tare da danna mashi kira. A daidai lokacin da kiran ya shigo yana juyi a saman bed ɗinsa, dik yagama birkicewa ya fita a hayyacinsa.

Wayar ta yi kara har ta katse bai ɗaga ba, sake kira ta yi, a karo na biyu ma bai iya yin picking ba, sai a karo na uku ne ya miƙa hannunsa da kyar ya ɗauki wayar, ba tare da duba mai kiran ba kawai ya yi picking, manna wayar a kunnesan ya yi ya ƙasa iya yin magana. Daga can ɓangare ta saka mashi shagwaɓa tana faɗin. "My Hero shi ne kaki picking da wuri?". Wani irin zoki bananarsa ta kara yi mashi ma jin sautin muryarta, da kyar ya iya amsa mata da. "Am sorry my Hoonaira".

Zare eyeballs É—inta ta yi kafin ta ce. "Ya naji voice É—inka a haka? Ko dai ka fara barci ne?". ÆŠan datse idanunsa ya yi tare da girgiza kai irin wanda yake cikin tsananin azabar nan, ya É—an datse lips É—insa na kasa da hakwaransa, bai iya ce da ita komai ba. Jin shiru yasa ta sake maimaita tambayar tata, a zatanta barci yake yi.

Da kyar ya iya sake lips É—insa ya amsa mata da e barci ya fara yi. "To mu bar wayar sai da safe ko?". Ta jefa mashi tambayar, ko kaÉ—an bai iya sanin amsar da bakinsa ya bata ba, daga haka ya saki wayar ta cigaba da juyinsa dan nemawa kansa sassauci. Ita ma cire wayar ta yi daga kunnenta tare da katse kiran, dan yadda ta ji ya ce sai da safen ya yi mata kama da wanda barci ta rigada ta ci karfinsa, so bata tsaya neman kiss na good night ba, gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike da tinanin kiss da ya bata. Saboda gajiyar hanya yasa tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Tana yin barci bai fi da minti biyu ba sai ga guyson ya shigo cikin bedroom É—in ya zo nemanta...... Ganin tana barci ya sa ya matsa dab da ita, addu'oi ya tofa mata kafin ya fice abinsa.

A ɓangaren Smart kuwa, yana barin bedroom na King ya wuce nasa, a gurguje ya yi wanka ya yi shirin kwanciya, rufe kofarsa da key ya yi ma saboda kada su zo su damesa, dan ya san Jaish zai zo, kuma yana kan tsini za'a iya samun matsala. Kuwa hasashensa gaskiya ce, dan kuwa Jaish ya zo nemansa, sai dai da ya ji kofar a rufe sai ya juya ya koma bedroom ɗinsa cike da damuwar menene yake damun ɗan uwan nasa. A daren wannan rana dai kusan rabin family ba barcin daɗi suka yi ba, cike da kunci da bakinciki wasu daga cikinsu suka kwana, har shi kansa King zuciyarsa tamkar zata fashe haka ya kwana. Momma ma dai hakan ce, Jaish cike da damuwa da tinanin san sanin abin da yake faruwa ya kwana, haka shi ma Jawad, abin dai sai shiru.

Washegari da safe, misalin karfe bakwai na safe, kiran gaggawa King ya aikawa da kowani members na family da ya hallara a cikin main parlournsa, aikuwa basu ɓata lokaci ba wajen hallara gabaɗayansu except Smart da kwata kwata ya ce ba zai sake taka kafafunsa a in da daddynsa yake ba har sai ya canza magana, kada ku manta kuma momma ta yi zazzafar magana a kan kada ya sake saka baki a kan bikin Auta, shiyasa ya yi banza da kiran daddyn nasa, ya ga massage ɗin kuma, yana kwance saman bed ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarsa yana ta tinanin Pretty, dan da safe war haka a France tana ɗakinsa ne tana damunsa da zata sha tea ya je ya bata, yau dik sai ya ji babu daɗi da bata zo ta damesa ba, a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa kuwa, bakinciki ne tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu!!.

Gabaɗaya family sun haɗe a main parlour, har da su Mammie, kowa ya natsu tsit yana jiran fara maganar King, Sarina burinta kawai taga Smart ya shigo cikin parlourn, dan a yunwace take da san kallansa. Fanan sai satar kallan Jaish da ya yi ƙasa da kansa yana tinanin zuwa ya duba Smart take yi, Khadijah and Zee suna part na Aunty MieMie. While ita kuma Aunty MieMie ɗin tana nan a wajen meeting da za'ayi. Gyaran murya King ya ɗan yi wanda ya janyo hankalin gabaɗayansu a kansa, natsuwa suka yi tsit dan sauraran abin da zai faɗa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kalli Jawad da Jaish ya fara magana a natse cikin bada umarni.
"Bakin Dubai sun sauka, ku shirya motocin zuwa tarbarsu a airport cikin ƙanƙanin lokaci". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan Auta dake zaune kusa da Chuchu ta kwanto jininta, dama ba komai yasa ya tattara ƴaƴan nasa dikka ba face yana san ne ya nuna masu cewa lallai ya isa da kowannensu, da alama kalaman Smart na cewa watarana zasu bijirewa maganarsa ta tsaya mashi a rai, shiyasa yake san kara nuna masu shi mai iko ne da su.
"Zunaira!". Ya ambaci sunanta. Da sauri ta É—ago daga jikin Chuchu, cike da respect ta amsa da na'am dad. "Anjuma by 2 za'a É—aura aurenki da yayanki Abdussalam, shi ne taran jama'ar da kika gani a gidan nan, abin ya zo cikin gaggawa ne, dan haka ki shirya". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan su Momma. Da farko ya ce ba za'a faÉ—awa Auta É—in ba sai an É—aura auren, amma da Smart ya yi mashi waÉ—an can kalaman sai ya ce bari ya sanar da ita ya gwada masu shi ke da iko da su, kun gane irin abin ai?!!.

Wani irin zaro ido da Auta ta yi, tsabar rikicewa da shiga tashin hankali bata san lokacin da ta zamo daga saman sofa ta zube gwiwowinta a kasa ba, a kiÉ—ime ta fara faÉ—in. "Dad Hoorain fa? Shi fa nike so dad, wlh Yah Abdussalam yayana ne kawai, Momma ki faÉ—awa dad, Akka please ki faÉ—awa dad cewa Yah Abdussalam yayana ne kawai, small dad ka faÉ—awa dad ina san Hoorain ka ji?". Cike da tashin hankali take sambatun, ba komai ya girgizata har yasa ta fita hayyacinta ba face tasan King magana É—aya yake yi, yanzu ya rigada ya yi kenan, wannan abin yasa ta kusa zaucewa, surutu kawai take yi ba tare da tasan me yake faÉ—e ba!.

Wani irin tsawa da King ya daka mata a kan ta natsun masa ne yasa bata san lokacin da ta zabura ta miƙe ta faɗa jikin guyson tare da kankame shi gam ba. Cikin kakkausar murya King ya ce. "Na rigada na gama magana, ƴan awanni kaɗan suka yi saura!!".

Dik cikin parlourn nan babu wanda bai razana da ganin yadda King ya ɗauki zafi sosai ba! Dayawa daga cikinsu sun tausayawa Auta, mussamman ma Chuchu da tini hawaye sun gama jiƙe mata fuska, ita ma Fanan hawaye ya jiƙe eyelashes ɗinta sharkaf saura su zubo, Aneesa ma dai idanunta sun yi jajir alamar ta tausayawa sister tata.
Chapter 204 · 0% Book details