← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 242

Sashe 130

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mammie ma alkawari ta yi wa kanta a kan lallai ne wannan shi ne mijin Sarina, dama ta ce first born na King yarta zata aura, to ga shi ya bayyana.

Uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka yi gaggawar bin bayan Akka da Dr Raj. Miƙewa Jaish ya yi tare da cewa Smart ya zo su je part ɗinsa ya kwanta ya huta zuwa da safe zasu sake zama, dan case bai kare ba, yanzu ma aka fara.

Jawad da shi ma already ya san da Smart saboda shi ɗin kamar ɗan momma yake, shi ma miƙewa ya yi tare da riko hannun Chuchu yana faɗa mata ta tashi su raka Yah Omerish part ɗin Jaish kafin su dawo su tafi nasu dare ya yi.

Smart rike da hannun guyson and Auta da ta yi shiru ya miƙe tsaye, Jaish ya yi gaba ya rufa mashi baya. Miƙewa Obaid and Omaid suka yi, har zasu wuce su fita Omaid ya juyo da kallansa a kan Sarina, ƙasa ƙasa ya ce. "Aunty Sarina kinga Yah Omerish ɗin yanzu ko? Ko dai har yanzu a mafarki kika san shi?".

Ta fahimci gatse ya yi mata cikin maganar, amma sai ta danne ta ce e ta gansa, a cikin zuciyarta kuma mamakin Omaid take yi, dan lokacin da tambayesu wanene Omerish shi Omaid bai yi magana ba, ya yi ma kamar bai jita ba, ashe ya ji É—an kaniya, rashin kunya yasa ya yi banza da ita.
Wucewa suka yi suka nufi waje abinsu. Mammie ce ya miƙe tana cewa Sarina su tashi su tafi dare ya yi. Miƙewa suka yi suka fita, parlourn ya rage mama, uncle Taheer da kuma Aneesa, mama ta gaza motsawa daga in da take zaune, tamkar ruwa ya cinyeta, ta rasa ganewa kanta, momma ta rusa mata plan, a ranta ta kuduri niyar wlh ba zata hakura ba, ba zata bari ba gaskiya, sai ta ɗauki mataki.

Bedroom dake kusa da nasa Jaish ya kai Smart, cike da kauna ya ce mashi. "Yah Omerish wannan bedroom É—in ya yi maka ko dai na canza maka wani?".

Hannu Smart ya É—aga mashi bayan ya saki hannun guyson, sannan ya ce. "Is okey, Omar ku zauna bari in yi take bath ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sake hannun Auta. Juyo da kallansa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Sorry our baby, daddy sai ya biya wannan marin da ya yi maki, bari Allah ya kaimu wayewan gari kin ji?".
Ya yi maganar yana É—an shafa kumatunta in da shatin hannun King suka fito ruÉ—u ruÉ—u.

Kai ta jinjina mashi tana kara shagwaɓe fuska.
"Hau saman bed ki kwanta ina zuwa". Ya faɗa yana nuna gadan da hannunsa. Ba musu ta haye har lokacin tana ɗan sauke shessheƙar kuka a hankali hankali.

"Yah Omerish ni ma bari in je in yi wanka sai in sa a kawo maka abinci". Cewar Jaish.
Jinjina kai Smart tiger ya yi, kafin ya ce. "No need anything now, ka dai je ka yi wankarka, ba sai kasa an kawo mun komai ba". Ya kai karshen maganar tare da É—an rungumar Jaish É—in kamar yadda suka saba a al'adarsu ta France, sannan ya nufi toilet.

Matsawa kusa bed É—in Jaish ya yi, cike da kauna ya kara rarrashin Auta da guyson kafin ya wuce ya nufi hanyar fita daga bedroom É—in. Yana fita kai tsaye nasa bedroom É—in ya nufa. Wani irin daddaÉ—ar kamshi na daban ne ta dokin hancinsa ba wanda ya saba ji ba, alamar an canza mashi room freshener kenan. Shakar kamshin ya yi haÉ—e da É—an lumshe idanu, alamar kamshin ta ratsa shi sosai, akwai daÉ—i kam.

Mamaki ya yi a kan waye ya canza mashi room freshener kuma?. A bakin bed ya zauna tare da rage kayan jikinsa, short and singlet kawai ya bari a jikinsa, miƙewa ya yi ya nufi toilet yana tinanin wannan cakwakiya na.

Tura kofar toilet É—in ya yi tare da yin addu'ar shiga ya sanya kansa. Tura kofar da ta ji anyi ne yasa ta juyo a miliyan dan taga wenenen? Tana tsaye a gaban jacuzzi wajen shower, ta kunna ruwa ta cika boket tana wanka, dan ita bata san shiga cikin jacuzzi, tafi yarda da ta tara ruwa a boket sai ta yi wankanta.

Ta gama sanya kumfar sabulu a gabaÉ—aya jikinta ta juyo gatesa. ÆŠan zaro mata idanunsa ya yi yana binta da kallo kamar ba shi ne ya ce kada ta bari su sake haÉ—uwa ba, ya ga kaya É—an rainin wayo, dama da guntun jarabarsa ta kwanaki uku da suka wuce da ya sameta tana barci a parlournsa, to bai gama watsakewa daga wancan bama sai ga shi yau ya sake yi babban kallo wanda da wuya ya iya tsallekawa ko kuma ya ce zai kwantar da wannan tarzoma dake shirin tashi

Saboda da alama abar ta motsa. Kasa gaba ya yi ya shigo cikin toilet É—in, ya kuma kasa yin baya ya fita, ya tsare yar mutane da ido, yasata jin kunya in ban da rashin kunya irin na jikokin Akka.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
========🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Love page, yauwa kwana biyu mun sha gwagwarmaya sosai, to yau kam bari mu ɗan yi nishaɗi mu leƙa duniyar masoya kafin mu ɗaura da surprises ɗinmu.

Ita kuwa tana ganinsa ta saki kara tare da juya mashi baya. ÆŠan É—aure fuska ya yi tare da jan siririn tsaki, wai irin shi zai basar kada a rai'na shi É—in nan, sai ya wani tsare gida, cikin dakiya ya ce. "Ke bana ce kada ki bari mu sake haÉ—uwa ba?". Yana maganar kuma yana karewa halittar jikinta kallo dan tabbatar rashin kunya irin na jinin Akka.

Shiru ta yi, ta ƙasa amsa mashi, ji ta yi tamkar ta nitse ƙasa saboda kunya. Wani siririn tsaki ya sake ja kafin ya juya da sauri ya fice yana haɗiyar yawu, wai shi a dole zai basar ya danne.

Saman bed ɗinsa ya haye ya kwanta, janyo wayarsa ya yi domin ya ɗan rage lokaci kafin ta fito. Sai dai kuma yana taɓa wayar tamkar ya kunnawa ƙwaƙwalwarsa tinaninta ne, gabaɗaya ya nemi sukuninsa ya rasa, har wani zufa ne ya fara keto mashi a gefe da gefen face ɗinsa, gabaɗaya a matse yake amma ya nuna zai danne hakan.

A hankali ya jefar da wayar tasa ba tare da ya farga ba, wasa wasa ya ɗan fara juyi a saman bed ɗin ƙwaƙwalwarsa na kara tinano mashi kyan surar jikinta, ga shi sai glowing take yi, hasken fatarta ya ƙara fitowa sosai, har wani yellow yellow ta yi. Haba tini notikan ƙwaƙwalwarsa suka fara kwancewa.

A haka ta fito É—aure da towel É—insa a kirjinta ta same shi, yana jin motsin fitowarta sai ya danne juyin da yake yi, ya kwanta ya kifu tsit kamar wanda ya yi barci, É—an rainin wayo kuma abar tana damunsa sosai, amma wai irin kada ta rainasa É—in nan, sai ya dake.

Ita kuwa baiwar Allah, bata wani kallesa sosai ba, saboda kunyar babu kaya a jikinta, da sauri ta shiga dressing room dan ta shirya.

Yana ganin ta shiga ya yi saurin miƙewa ya nufi toilet wai dan ma kada ta dawo ta same shi a haka har ta gane halin da yake a ciki, sai ya gudu cikin toilet yana matse bananar tasa dan ya samu sauki.

Cikin ɗaya daga cikin kayan da momma tasa mama Haulat ta kawo mata na barci ta shirya. Ta yi wani irin kyau da in dai namiji lafiyaye ne ya ganta to fa ba zai iya hakura ba. Hijabin da take sallah ta ɗauka ta ɗaura a saman kayan, sannan ta fito ta nufi part ɗin momma dan ta ɗauko mashi cappuccinon, Allah sarki sam bata gajiya da kyautata mashi dan tana san kayanta, shi kuma sai sinki sikin iskanci da iyashege cike da ƙwaƙwalwarsa.

Mama Haulat ce kullum take kara karfafa mata gwiwa a kan ta cigaba da matsar da kanta a garesa tabbas watarana zai waiwayeta, shiyasa kuka ga har yanzu take shiga bedroom É—insa bata dai'na ba, ita kuma Chuchu tana kara koya mata yadda zata narka zuciyarsa a soyayyarta, yanzu ta É—auki darasi sosai abinta, jira take yi kawai wani abin ya haÉ—asu yaga zallar madarar soyayya.

Allah sarki momma uwa ta gari, dik da tana cikin damuwa a kan abin da ya faru a tsakaninta da King, hakan bai hanata ta shiryawa Æ´aÆ´anta abin da suke so ba, ta shiryawa Jaish and Omerish cappuccino kamar yadda suka saba sha a kowacce dare kafin su kwanta.

Mahnoor tana zuwa ta ɗauki cappuccinonsa kamar yadda ta saba, a lokacin momma tana cikin toilet tana wanka dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta ta rarrashi kayanta......🤭👀

Bata tsaya jiranta ba ta ɗauki cappuccinonsa ta fito. Har lokacin da ta koma bedroom ɗin yana cikin toilet bai fito ba....... Wai me ya tsayar da Jaish a cikin toilet ne?........👀🥱

Ɗan ƙaniya yana can yana ƙoƙarin controlling na kansa ya haɗiye kwaɗayinsa ya danne abar gadon, sai dai ya gaza iya yin hakan, sai ma kara tashi hankalinsa yake yi ta sanadiyyar tinano mashi surarta da ƙwaƙwalwarsa yake ta yi, dik ya kiɗime, abin tausayi kuma abin dariya.
Saman table ta É—auka cappuccinon, sannan ta É—auko perfume da Chuchu ta bata mai sanyin kamshi ta feshe jikinta da shi. Kamar zata fice waje izuwa bedroom É—inta, sai kuma ta tina da kalaman mama Haulat da kuma Chuchu É—azun in da suke ce mata ta dai'na kwana a wani waje in ba a saman bed É—insa ba, komai zai ce mata kada ta damu ta daure watarana zai wuce kuma zata yi nasara.
Chapter 130 · 0% Book details