← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 242

Sashe 178

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen wannan matashiyar budurwa saman kujera ya zauna. GabaÉ—aya ko'ina tsit kake ji tamkar babu halittu a cikin fada. Queen hannunta na rike da wani É—an karamun akwatin lu'ulu'u mai shegen kyau yana kyalli launin gold.

My people's a tinaninku a kingdom of power ake cin amana da munafurci ko? To kun yi kuskuren tinani, bana jin akwai kingdom É—in da ya kai nan cin amana da munafurci dik wannan uban tsaro da kuka gani da izayar da Queen Zarina take yi wa masu tinanin cin amana kafin ma su aiwatar, wlh dik da haka ta ko'ina akwai makarkashiya da suka mamayeta, ku dai mu je zuwa.

ZARTAR, shi ne shugaban bokayen a ɓangaren yanke hukunci a kan abin da ya shafi bayi da sauransu. Gabaɗaya fada ta zuba mata idanu suna jiran jin mezata ce. Ita kuwa shiru ta yi na tsawo a kallah good ten minutes kafin ta ɗan kara dakewa a cikin alkyabbarta zubin Uk, cikin kakkaifar murya ta fara magana kamar haka. "Zartan har yanzu kana nufin baku iya gano in da wannan makulli yake ba? Dik karfin ganinka, dik karfi eagle eyes ɗinka, amma baku iya sanin in da yake ba?".

Kasa gabaɗaya bokayen fada suka yi da kansu, Zartan da ya kasance wani tsohon dattijo mai farar gashi kal, ga shi dogo da shi zubin Uk, idanunsa tamkar na mage gwanin ban tsoro, yana sanye da fararen kaya da wani dogon mayafi dake ja har ƙasa, gashin kansa da kayan jikinsa iri guda ne, yana da wani tabo a goshinsa kamar zanen katan maciji ya fasa kai. Zartan yana ɗaya daga cikin Kim family, Kim family kuma su ne familyn Queen Zarina kenan, kazalika yana da kafa a fada sosai.

Miƙewa tsaye ya yi cikin girmamawa ya ce mata. "Ina kara miƙa hakurina a gareki, dik iya hangen da zamu yi mun hakanga bamu ga wannan makulli ba, amma dai tabbas wannan makulli baya kingdom of power, tabbas yana ta wani wajen ne na daban".......... Tsufa ta fara yawaita a tattare da shi, domin kuwa maganarsa ma bata fita sosai. Mai da kallanta a kan wannan sarki da ya shigo ɗazun ta yi, a natse ta ce. "Baka da abin faɗe ne a kan wanna case ɗin Ude?"...... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "For now dai babu, amma abin da zan ce shi ne zamu yi nasarar mamaye ko'ina, mu cure duniya ya zama abu guda kuma mu mulketa, ko Zuhair yana so ko baya so dole sai ya zube gwiwowinsa a ƙasa ya lashi kasan takalmarmu ya kuma goge mana saman, daga karshe ya zama bawanmu".

Wani irin shu'umin murmushi ta saki saboda Ude ya faranta mata ranta sosai, tana matuƙar yunwar ganin ta cure duniya ya zama abu guda ɗaya, babu wasu kasashe dik a zama ɗaya, sannan ta zama ita ke mulkarsu dikka, ta murza kambunta ta juya kowa, dik wanda yake san sanyaya ranta to ya yi mata kamalai irin wanda Ude ya yi mata a yanzu, koda hukuncin kisa tasa aka yankewa mutum in dai ya yi mata irin kalaman Ude tana iya yafe mashi.

"Amma ya batun Nieelarh da MUZAFFAR FAMILY fa?. Cewar Queen kenan..... Nieelarh ƴar cikin Queen Zarina ce, ita ce kuma wannan kyakkyawar matashiyar yarinya dake gefenta. MUZAFFAR FAMILY wasu jiga jigai ne daga cikin birnin waɗan da su ke da arzikin dik wani abincin da ake ci a cikin birnin, sannan sune politics family dake kasar gabaɗaya, mutane ne masu karfin iko da isa, da ace yau zasu ɗauke wa birnin Justice dik wata tallafi hakika da birnin ta cika da yunwa matuƙa. So head of the familyn wato MUZAFFAR ya kasance mutum mai girma a fada, sannan mutum mai girma a birnin, dik bala'in Zarina tana raga mashi, wasu daga cikin mutanen birnin suna cewa akwai wata alaƙa a tsakaninsu, wasu kuma suna cewa saboda karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafacesa har ma take shakkarsa.

To dik bama wannan ba, haƙiƙa karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafe familyn Muzaffar har ta samu damar sarrafasu san ranta kamar yadda take yi wa sauran jama'a, amma ba hakan ce tasa take shakkar Muzaffar family ba, akwai wani sirri nata da shi dattijo Muzaffar ya sani wanda kuma ga dukkan alamu tana tsoron ya fasa kwai shiyasa take shakkarsa sosai, to a halin da ake ciki yanzu ɗaya daga cikin Muzaffar family ya nuna ra'ayin yana san ƴarta Nieelarh wanda kuma dan dole ta amsa da ta yarda da batun, amma ta ƙarƙashin ƙasa tana neman ta yadda zata yi ta warware wannan batu, saboda ba zata yarda haɗa jini da musulmai ba a cewarta, ta kuduri niyar ko ta halin yaya sai ta ruguje wannan batu, sai dai kuma ba zata iya yin fito na fito da Muzaffar family ba!.

Amma me kuke tinanin zai kasance sirrinta da bata san ya fashe kowa ya sani da har take daurewa ta yi wa Muzaffar family sauki haka?.

Ɗaure fuska sosai Ude ya yi kafin ya amsa da. "Haƙiƙa Nieelarh ba zata shiga Muzaffar family ba, dan hakan ƙasƙanci ne da faɗuwa a garemu". With his full confidence ya yi maganar, haƙiƙa yana da tabbaci a kan maganarsa!. Ɗan Nieelarh fa ƴarsa ce, ba zai bari hakan ya faru ba!.

Jinjina kai ta yi cike da farincikin amsoshin Ude a ranta, sannan ta miƙe tsaye, cike da bada umarni ta ce. "Zartan ku cigaba da binciken ina Spender yake ta maduban dubanku, ku tabbatar kun yi gaggawar binciko shi, Ude ina da magana da kai, ka sameni a ciki main parlour". Tana kai karshen maganar ta yi gaggawar juyawa alkyabbarta na jan ƙasa sosai ta nufi wani katafaren diamond door da zai sadata da cikin katafaren gininsu na alfarma wanda ya kasance shi ne family part ɗinsu.
Gabaɗaya mukarraban fada suka miƙe bisa girmamawa a gareta har sai da ta bar fadar sannan suka koma suka zauna. Tana fita kofar wasu mahaukatan zaƙwaƙuran warriors suka take mata baya zuwa kofar shiga cikin part ɗin nasu!.

Cikin kakkausar murya mai amon bada umarni Ude ya kara jaddadawa bokayen royal palace ɗin abin da Queen ta faɗa, daga haka ya miƙe ya bi bayanta ya bar Nieelarh da Beer wato kanin Zarina ne shi ɗin.

Kai tsaye katafaren parlournsu na alfarma Quren ta shiga, still dai hannunta rike da wannan akwatin. Saman wani luntsumemen sofa mai zaman mutum uku ta ajiye akwaitin, sannan ta fara safa da marwa a tsakiyar parlourn tana É—an bubbuga hannayenta cikin juna, alamar tana cikin damuwa..... A haka Ude ya shigo ya sameta, cike da kula sosai haÉ—e da nuna damuwar ganin halin da take ciki ya ce. "Lafiya kuwa ranki ya tsananta fiye da kowacce rana?".

A gaggauce ta juyo da kallonta a kansa, cikin kakkaifar murya ta amsa mashi da. "Ba zai taɓa kasancewa lafiya ba ka ganni a tsaye, kasan da cewa in dai bamu samu Spender ba tabbas Muzaffar family sai sun ɗauke Nieelarh daga garemu, sannan zata iya shiga wannan addini nasu, dik bama wannan ba, damuwata shi ne Zuhair ya tsugunna ya goge mun takalma, na mayar da shi bawa na dattijo mai goge goge a royal palace ɗina, na mayar da matansa kuyanguna, na mayar da ƴaƴansa masu yi mun hidima, mazan kuma masu ɗeben kewa, na sa ya ɗanɗani ɗacin da ya ɗanɗana mana na kashe mun mahaifi da ya yi ya kuma ruguje Thomas family!!".

"Wannan kuduri naki ba zai taɓa kasancewa ba, na sha faɗa maki ki hakura kawai". Wata murya ce ta furta hakan a yayin da take ketowa izuwa cikin parlourn. Kyakkyawar matashiyar yarinya ce da bazata wuce 23 years ba duniya, fara ce tas kamar madara, kyakkyawar gaske ajin farko, tana shirye cikin alkyabbarta na sarauta na alfarma wanda ya sha kwalliya da duwatsun lu'ulu'u, da ganinta kasan jinin sarauta ce. Kwayar kyawawan idanunta sun kasance hazel eyes ne mai ɗan duhu, hakan yasa ya yi kama da green eyes sosai. Idanun nata basu da girma sosai, amma suna da kyau matuƙa.

Queen Zarina zata yi magana Ude ya rigata da cewa. "Ke Rishma kina da hankali kuwa? Ita kike faÉ—awa magana gatsau haka?". Da wani irin kallo ta bisu, da kaga wannan kallan kasan na takaici ne, sannan ta ce. "Ude idan baka tuba ba, babu shakka zaka mutum a kaskance, zaka mutu mutuwa mafi munin da ko kare sai ya fika daraja a wajen mutuwa........."

Dan dole ta haÉ—iye sauran maganar nata saboda wani irin uban tsawan da ya daka mata, ba shiri ta yi tsit tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi.
"Keeeeee Rishma, ki iya harshenki ko kuwa na datse maki shi a yanzun nan!!!!". Shi ne abin da Ude ya faɗa...... "Ude ba zan iya harshe na ba, ka rigada ka ketare iyakarka, na dai'na jin tsoron dik wanda baya tsoron Allah, tin kan lokaci ya kure maka Ude ka tuba...... ". A miliyan ta haɗiye maganar nata sakamakon nufarta da ya yi gadan gadan tare da cire hannu zai ɗauke mata fuska da mari. Sai dai kuma bai kai ga sauke mata marin ba aka rike hannunsa cak ta baya. Cikin wani irin fusata ya yi zafan juyowa dan yaga wani mai karan kwana ne ya rikesa. Sai wani irin huci mai zafi yake fitarwa, ran maza ya ɓaci. Ita dai Queen tana tsaye tana binsu da kallo.

"Kada ka sake ka É—aura hannunka a jikinta Ude, idan kuma ka yi gangancin yin hakan tabbas hannunka ba zai sake kasancewa naka ba, dan sai na datse maka shi!!". Shi ne abin da wanda ya rike hannun nasa ya faÉ—a. Wani kyakkyawa mutum ne wanda da ka gansa kasan É—an uwan princess Rishma ne, dan suna kama sosai, yana tsaye tsayuwar jarumta, cikakken namijin gaske ne, fari tas da shi, yana sanye da wani irin kaya mai kama da na warriors, sai dai ba su bane, wannan kayan jarumai ne.
Chapter 178 · 0% Book details