← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 242

Sashe 185

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cauting from one to ten ya yi kafin ya lallaɓa ya gudu bayan Black Tiger ya ɓuya, sannan ya ce mata let's go. Lalluɓarsa ta fara yi tana tafiya a hankali. Shi ma a hankali hankali ya baro bayan Black Tiger ya matsa ya dawo ta bayanta, ya zamana tana tafiya yana biye da ita a baya, sam bata jisa ba, gabaɗaya hankalinsa a kan Black Tiger, ya tsare yayan nasa da kallo kamar mai nazarin wani abin. Sai nemansa Sweetie take yi tana zagaye cikin ruwan, ga shi ruwan ya fi karfinta, dan har wuya ya kai mata, dan dai ba ruwan gudu bane, da ba zata tsira ba. Ta sha kewaye a wajen bata ji alamarsa ba, dab kusa da Black Tiger ta tsaya, suna fuskantar juna ba tare da ta sani ba, Ronnie na bayansu, a shagwaɓe sosai ta saka kuka tana faɗin. "Ni lovely bro ka zo ka kwance mun wannan abin, ka ɓuya nakasa ganinka..........." Bata kai karshen maganar ba Ronnie ya tureta da karfi ta tafi sai saman lion chest na Black Tiger.

Murmushi ya saki kafin ya ce. "Dama a manne da juna na sameku, ni na rabaku, yanzu kuma da zan tafi shi ne na mayar daku yadda na ganku". Yana kai karshen maganar ya yi zafan fita daga cikin ruwan wai dan ma kada Black Tiger ya kama shi, abin gwanin ban dariya kuma gwanin birgewa. Yana fita bai dakata ba ya yi gaggawar barin wajen ya koma cikin bedroom ɗin Black Tiger. Ita kuwa Sweetie ƙoƙari kwace abin dake idanunta ta yi dan ta samu gani, sai dai ta ƙasa, saboda yadda kuka san padlock aka sanya aka datse hanki ɗin, yaki kwancuwa ko kaɗan.

(Anya ba Black Tiger ya rike shi ya hana shi kuncuwa ba kuwa? Ɗan duniya ba! Ka gansa kaman wani salihi, ɗan rainin wayo.😅🥱)

"Big bro please remove this thing for me". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Kamar babu Black Tiger a wajen, ya yi banza da ita idanunsa a kan face ɗinta, kaman mai nazarin wani abin. Laluɓe ta fara yi tana ɗan tattaɓa jikinsa dan ta tabbatar da yana wajen ne ko dai baya nan, ta yi magana without reply, shi ne take zaton ko dai baya wajen ne.

Lokaci guda ya yi wani danko hannunta ɗaya cikin zafa, ba komai yasa hakan ba kuma face a garin laluɓenta take ƙoƙarin sake capke mashi hero kamar dai ta ranar..... Ajiyar zuciya ta sauke jin ya damki hannunta, hakan yasa ta fahimci yana wajen kenan. Can ƙasa ta tsinkayo lion voice ɗinsa yana faɗin. "Na yarjewa yarjejeniyarki, amma kada ki wuce gona da iri".

Yarjejeniyar me kuke tinanin ta ce su yi? Sweetie akwai wayo sosai wlh, da alam tarko ta É—ana mashi. "To shikenan na yarda, amma yanzu dai kwance mun wannan abin". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

"Hakan baya cikin yarjejeniyarmu, and ai bani na ɗaura maki ba". Ya faɗa a sanyayye sosai................ Ɗan rainin wayo, so yake ya yi ta kalle mata fuska kada ta san ya kalla, shiyasa ya ce ba zai kwance mata ba, saboda ba kara mun kyau ta yi ba a yadda ruwa ya jiƙata, gashin kanta ya kwanto har face ɗinta, lip's ɗinta sun kara kyau matuƙa saboda ruwa da ya taɓasu, gashin gaban goshinta sun kara kwanciya luff, ko makiyinta ya ganta yasan ta yi kyau over, kuma sai ya shagala da kallonta bare kuma shi Black Tiger da ba kiyayya suke yi ba, bashi da wata matsala da ita, hasalima yanzu yana san ta kasance da su dan ya lura kaso 60 cikin ɗari na farincikin Ronnie yana tattare da ita, so bashi da wata matsala da ita yanzu...... Ni kuwa nace ba dole ta zama farincikin Ronnie ba tun da ta bashi kalmar shahada, ta janyo shi cikin haske, dole ya yi farinciki idan yana tare da ita.

"Please mana our big bro, nasan baya cikin yarjejeniyarmu, amma kuma ai akwai batun kada ka bari wani abin cutarwa ya zo kusa da mu ko?". Ta faɗa tana ƙoƙarin kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. "Wannan ai ba abin cutarwa bane, da na cutarwa ne Ronnie ba zai ɗaura maki ba". Ya yi maganar tare da sakinta. Yana saketa tamkar wadda aka turo haka ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa again...... "Allah abin cutarwa ne shi ma". Cikin muryar kuka ta yi maganar.

Banza da ita ya yi, bai da niyar kwance mata, ɗan rainin wayo dan bai gaji da kallan madarar kyan da Allah ya yi mata ba, sai ya fake da cewa ai ba shi ya ɗaura mata ba, dan haka ta nemo Ronnie ya kwance mata, har da dagewarsa irin da gaske yake yi shi fa. Kamar zata yi kuka ta bar jikinsa ta fara laluɓar hanyar fita. Allah ya bata nasara ta samu ta fito, idanunsa a kanta bai hanata ba, haka ta fara laluɓe har ta isa wajen stair case, ga ruwan dake zuba a jikinta, bata san ta isa wajen ba, tana ɗaga kafa ta sauke sai ta tafi gabaɗaya ta yi ƙasa, tin daga kan step na farko ta yo kasa har karshe, dik kuma yana ganinta bai taimaka mata ba, bai kuma yi amfani da magic wajen tsayar da ita ba, ya barta ta isa ƙasa dik ta bubbuge jikinta, har ta dan ji ciwo a hannu. Azaban da ta ji ne yasa ta saki ihu mai sautin da ya ja hankalin Ronnie dake zaune saman sofa yana shan tea mai zafi sosai.

Da gudu ya ajiye cup ɗin a saman table dake gabansa ya nufota yana tambayarta lafiya kuwa. Kuka ta saka mashi kawai ba tare da ta yi magana ba, duƙawa ya yi ya ɗauketa cak ya yi waje da ita, har ya canza kayansa izuwa na sport, sarkin san wasanni ba. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma da ita, a nan ya kwance hanki ɗin ya yi ta rarrashinta har ta yi shiru, sannan ya ce ta je ta yi wanka ta canza kaya, ba musu ta bi umarninsa. Yau da ta yi wanka irin shigar mutanen birnin ta yi, wato umbrella gown mai maɗauri a tsakiya, ta yi kyau sosai, gashin kanta saboda samun kwanciyar hankali ya kara tsawo sosai, har ya kusa zarce mazaunanta, ya kuma kara tura kala sosai. Kwace saman bed ta iskosa yana kallan chandelier ɗin ɗakin nasa, a gefensa ta zauna, cike da nuna kauna ta ce. "Lovely bro ina san zuwa church ɗinku".

Zaro idanu ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. "Mezaki je ki yi?". Ya yi maganar tare da miƙewa zaune suna fuskantar juna. "Babu kawai ina san zuwa ne in gani". Shiru ya ɗanyi kafin ya ce. "To gobe idan kika dawo daga school zamu je a tare by 4:00 ko 4:30 haka". Sosai ta ji daɗin amincewarsa, cike da murna ta matsa ta sumbacesa a kumatunsa, siririn murmushi ya saki kafin ya ce. "Kin san wani abu sister?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba. Tana ta sakin ƙayataccen murmushi.
Kashe murya sosai ya yi kafin ya ce. "Ina san ganinki a tare da big bro, kuna kyau sosai, dan Allah ki rinƙa kasancewa a tare da shi, kinga yanzu kin fara canza mana shi ko?". Shiru ta ɗan yi alamar kamar bata ji daɗin maganar ba, sai kuma ta saki siririn murmushi kafin ta bashi amsa da. "Ina fatan ya sauya, ya canza ya zama musulmi, ina yi mashi kwaɗayin rahamar Allah sosai". Ɗan zaro idanu Ronnie ya yi. "Kina nufin ba kya san yayana? Dik abin da kike yi mashi kawai kina yi ne dan ya musulunta?". Jinjina mashi kai ta yi alamar ba shakka haka ne, sannan ta ɗaura da cewa. "Ko kaɗan babu soyayyarsa a rai'na, soyayar Kamran ce kawai a raina, and na fi jin sonka a rai'na ma sama da yayanka, ina jin yayanka tamkar ɗan uwana ne na jini wanda ina ga hakan ce tasa bana jin sonsa na soyayya a rai'na, kasan wani abu?".

Kasa bata amsa ya yi ko ya motsa daga in da yake, ya kafeta da ido mamaki kamar ta kashe shi, shi dik tinaninsa tana san yayansa shiyasa yake tayata yakin neman soyayyarsa, bai san ita wanda take so ma daban ba ne...............Dik da bai amsa mata ba hakan bai hanata cigaba da yin maganar da take da niyya ba. "Yayanka ya haÉ—a dik abin da kowacce mace zata so a duniya, nasan kasan da cewa komai isar mace idan ta gansa sai ta faÉ—a mashi, amma ni kaunarsa nike a matsayin É—an uwa na jini haka, soyayyar Kamran ne kawai a rai'na".

Shiru ya yi na almost 3 mins kafin ya nisa, sannan ya saki ƙayatattcen murmushi. "Sister a labarin da kika bani kin ce mun Kamran ma ba musulmi bane ko?"............. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To meyasa baki taɓa tsayawa ki jajirce a kansa lallai sai ya musulunta ba? Ko shi baki yi mashi kwaɗayin rahamar Allah ne?"....... Shiru ta yi kamar mai tinanin abin faɗe, da alama ya ɗaureta da magana.

"Baki da amsa ko? Dama ai ba zaki iya bani amsa ba, amma ni zan baki amsa, dalilin da yasa kika tsayawa big bro kika zage kina san ganinsa a cikin ni'ima ta Ubangiji ba komai bane face so, shi ne wanda kike yi wa so na gaskiya, dik wanda zaki so to a bayansa ne........." A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "No Ronnie, ko ɗaya ban taɓa san yayanka ba, in dai kaunarsa". Jinjina kai ya ɗan yi. "Kin san soyayya ne ma da zaki iya banbanta wanda kike kauna da wanda kike so?". Ya tambaya kamar shi ma ya san me so ɗin, da dalilin ɓacewar Floris daga garesa ne fa ya fara fahimtar me soyayya, amma har ya fara zaƙewa zai nuna shi ya sani.
Chapter 185 · 0% Book details