Sashe 115
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani tsawa da ya sake daka mata a kan ta fita mashi daga ɗaki koku ma ya ɓaɓɓallata ne yasa ta yi saurin miƙewa da gudu zata fita. Mama Haulat kuma jin tsawan yasa ta shigo da gudu domin ta duba menene?.
Karo suka yi da Mahnoor a bakin kofa zata fita, da sauri ta yi ƙoƙarin riketa dan ta tambayi ba'asi, sai dai ina, Mahnoor bata bada damar a riketa ba, da gudu sosai ta danna waje tana sakin kuka mai tsuma zuciya.
Dawo da kallonta a kansa mama Haulat ta yi, cikin girmamawa ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya?". Wani irin hararar da ya dallawa mama Haulat ɗin ma har sai da yasa ta ji ƴaƴan hanjinta sun kaɗa. Siririn tsaki ya ja tare da miƙewa ya zo ya wuceta ya nufi waje yana huci kamar ba lafiya ba.
Kai tsaye part na King ya nufa, dan ya fahimci momma a kan Mahnoor bazata wani goya mashi baya sosai ba, King ne kawai zai rarrashesa. Sai dai kuma maganganu suka yi a kan Auta sosai kafin ya sanar da King shi fa baya san Mahnoor, ya tsaneta a kusa da shi, dan haka shi ko a rabata da in da yake, ko kuma shi ya bar gidan ya koma Dubai.
Rarrashinsa sosai King ya yi kafin ya faɗa mashi cewa ya bashi nan da kwana goma zasu tsai da matsaya a kan hakan, amma yanzu dai ya yi hakuri suna tsaka da wani muhimmin aiki ne. (Aikin neman Auta kenan, kun san Jaish bai san ta ɓata ba, kuma an ɓoye mashi, so shiyasa ya ce mashi suna aiki kawai.)
Aminta da zancen King ya yi, dan haka sai ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ransa a ɓace sosai. Kafin ya koma mama Haulat ta goge wajen da cappuccino da Mahnoor ta kai mashi ya zuba, so ta gyara ko'ina tsab.
Yana zuwa ya haye bed ɗinsa ya kwata, yau ba za'a sha cappuccino ba kenan. Amma fa ko da ya kwanta barci ta gagara zuwa, gabaɗaya ya rasa me yake yi mashi daɗi, shi kaɗai sai kunci yake yi har zuwa karfe 2 na dare. Ganin bashi da wata manufa yasa ya miƙe jiki ba kwari ya shiga toilet, alwala ya ɗauro ya zo ya fara gabatar da nafilfili, surorinma dik a daddafe yake karantasu, sai dai kafin ya idar da raka'a biyun farko tuni jikinsa ta wastsake ya koma normal. Qur'ani kenan my people's, dik damuwar da kake ciki kana fara karanta shi cikin ƙanƙanin lokaci zaka ji ka wastsake watsau, Allah dai ya ƙara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya.
Sai da ya yi sallar rakatainil fajir sannan ya bar saman daddumar ya wuce toilet, wanka ya yi ya shirya cikin arabs jallabiya brown color, ya nufi masallaci. Bai tawo ba sai karfe 8 na safe, jiya kwata kwata bai yi barci ba kenan.
Yana dawowa karfe 8 ɗin ma dan kada su haɗu da momma sai ya wuce part ɗin King kai tsaye, dan a tinaninsa Mahnoor ta sanar da momma walaƙancin da ya yi mata daren jiya, shiyasa ya gudu.
Sai dai abin mamakin shi ne ko da ya je part na King baya nan, ya tafi fada, ya sha madarar mamakin jin hakan, me ya fitar da King fada da safe haka? Ya jefawa kansa tambaya. Ganin babu mai bashi amsa yasa ya wuce kai tsaye ya nufi fadan.
Sosai ya kara shan madarar mamakin ganin dik wasu masu muƙami a fada sun hallara, dik wasu manyan fada suna ciki, Aunty MieMie, uncle Abbas, uncle Jahiz, uncle Taheer, harda Guyson dik suna ciki, abin ya yi matuƙar ba shi mamaki.
Dai'dai lokacin da ya sako kansa a cikin fadar sai ji ya yi uncle Abbas ya ce. "Wannan babbar gazawa ce a garemu ace katafaren kingdom kamar wannan wanda babu biyunsa a kasar nan, ga tarin tsaro wanda ba'a taɓa yin biyunsa a duniya ba, dik wasu abubuwa muna da su, amma har a shigo a ɗauki Zunaira a cikin masarautar nan a fita da ita yau tsawon satika shidda, kai gaskiya wannan babbar gazawa ce a garemu, kuma a gaskiya Zafar na rai'na tsaronka, ka bani kunya".
Haba wani irin dum dum Jaish ya ji kirjinsa ta buga, har wani sara mashi ya ji kansa ya yi.
Uncle Jahiz zai yi magana suka farga da Jaish dake tsaye a bakin kofa yana binsu da kallo yama rasa abin faÉ—e, sai yake jin kamar karya kunnuwansa suke yi mashi, kamar kuma mafarki yake yi, kenan dama Auta ba Dubai ta tafi ba? Kenan abokan gaba ne suka É—auketa? Babbar magana lallai yau babu zaman lafiya.
Ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ne yasa gabaÉ—aya suka yi shiru, King ne ya bishi da kallon mamaki, dan bai yi zatan zai zo fada a yanzu ba.
Uncle Abbas ne ya yi karfin halin cewa. "Jaish ka shigo ciki mana, me ya tsayar da kai a bakin kofa kuma?".
Ba musu ya ƙariso ciki, sai dai yana addu'ar Allah yasa karya kunnuwarsa suka jiyo mashi, har zuciyarsa ta fara yi mashi tsananin zafi, dan ba zai iya ɗaukar maganganunsu ba in dai gaskiya ce. A sofar kusa da uncle Abbas ya zauna, kansa a ƙasa cike da fargabar amsa da zai iya samu daga bakin uncles ɗin nasa ya ce. "Uncles ku faɗa mun da gaske abin da na ji kuna faɗa haka ne? Kada ku ɓoye mun kamar yadda daddy ya yi, dan Allah ku faɗa mun, daddy ya ce tana Dubai, and kowa na kira a Dubai kame kame kawai yake yi mun, ga wayarta a kashe baya shiga, please second dad ka faɗa ina Zunaira take? Kasan ni mai iya karɓar kaddara ce a dik yadda ta zo mun, to ka faɗa mun zan yi imani da koma menene ya sameta in kuma hakura".
Dik wanda ya ji zantukan Jaish yasan cikin tsananin damuwa da ɓacin rai yake kalamansa, kuma sun san wlh karya ne ba zai iya ɗaukar wannan kaddara ba, kawai yana san su faɗa mashi ne ya ji wani hali Auta take ciki, idan suka faɗa mashi kuma sun san idan akwai abin da ya fi hauka ma zai yi masu, dan ba karamar yaki za'ayi ba, ba zai saurari kowa ba!.
Shiru fada ya yi suna sauraron kalamansa masu kama da sambatu, dan kamar bai san me yake faɗa sosai ba, dik cikin fadan nan babu wanda bai tausaya mashi ba, saboda kowa yasan yadda yake da Auta, shi fa ya yi renonta, dik wanda ya ga Auta a lokacin yarintarta to tabbas zai ga Jaish a bayanta, a tare suke koda yaushe, shiyasa suka yi sabo sosai, har su commander sun tausaya mashi matuƙa.
Allah sarki commander har ya yi wani irin mummunar rama sosai, saboda tashin hankalin da yake ciki a kan Hoorain, babbar abin da ya É—aga mashi hankali ma shi ne King ya bada umarnin gani da kisa a kan Hoorain, saboda a tinaninsu amanarsu ya ci, kun san ya gudu ne ai, so sai aka saka dokan gani da kisa kai tsaye kawai a kansa.
Tsit fada ya yi, kowa jiran abin da King zai ce suke yi, gabaÉ—aya hankulansu a tashi. King kuwa, sai da ya É—auki a kallah 5 mins yana nazarin abin da zai faÉ—awa Jaish É—in, dan yana fargabar kalar balai'n da Jaish zai tayar masu, shi kansa yasan bafa za'a wanye lafiya ba.
Gyara zamansa ya yi tare da É—an yin gyaran murya, cikin natsuwa ya ce.
"Zan faɗa maka komai, amma ba yanzu ba sai mun haɗu da daddare a ɗaki, yanzu kaga muna wani tattaunawa ne mai matuƙar muhimmanci dan haka ka bari sai mun kammala".
Kirjinsa ne ta amsa da karfi, É—an dafeta ya yi kafin ya ce. "No Please dad, ba zan iya kara koda one minute bane idan har ban ji gaskiyar in da Auta take ba, you know my condition dad, please kada.............."
Hannu kin ya ɗaga mashi alamar ya yi ba sai ya ƙarisa ba. Dakatawa da yin maganar ya yi yana sunkuyar da kansa ƙasa, saboda wani irin bugawa da karfi da kirjinsa take yi.
"Zan faÉ—a maka menene yake faru". King ya faÉ—a.............. Da sauri Jaish ya É—ago kansa zuciyarsa na harbawa da É—an karfi karfi, cike yake da fargabar abin da zai ji, baya san jin zancen da gaske bata nan.
"Lallai ne tabbas Zunaira ta ɓata". Cewan King agin........... Dum dum ya ji kirjinsa ta sake bugawa, take ya ji hankalinsa na neman gushewa, a wani irin zabure ya miƙe tsaye kamar wanda ya rasa control ɗinsa.
Hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙe tsaye, uncle Abbas ne ya yi saurin riko hannunsa yana ƙoƙarin mayar da shi ya zauna, ya ƙasa yin magana, yau tsawon sati shidda babu Auta babu labarinta, gaskiya wanna abin ya girgizata shi. Dole ya koma ya zauna yana tunanin yadda zai yi?.
King ne ya cigaba da bashi labarin yadda komai yawakana. Daga karshe ya rufe mashi da cewa.
"A yanzu dai bayan assistant commander Hoorain babu wanda ya rage muke zargi da sace Zunaira! Dik wanda muke tunanin tana hannunsu ko suna da sa hannu a saceta mun bincika bata nan a hannunsu, Hoorain ne kawai bamu san in da yake ba, kuma muna kyautata zaton shi ya É—auketa!!".
Tashin hankali, wani irin zaro idanu commander Zafar ya yi, kenan dama King yana zargin Hoorain har haka ne? Sam bai taɓa yin wannan tinani ba.
Shi kuwa Jaish zaro idanu ya yi, a miliyan ya sake miƙewa tsaye, zuciyarsa ce take tafasa tamkar an ɗaura dalma a wuta, jikinsa har tsuma yake yi yana tuna idan da zai ga Hoorain a yanzu sai Allah kaɗai yasan me zai faru.
Dik su uncle Abbas kallansu a kansa, sun tausaya mashi matuƙa, sun kuma shiga damuwa dan abin da suke gudu shi ne yake shirin faruwa. Su commander Zafar dik kallansu a kansa, suma sun tausaya mashi matuƙa.
Yana tsaye yana fuskantar King, a take ya fara zuba huci kamar mayinwacin zaki, ya buÉ—e baki cike da É—acin rai zai yi magana unexpect aka turo babbar kofar fadar aka buÉ—eta.