Sashe 96
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe takwas yana bugawa dai'dai wani irin daddaÉ—ar kamshin perfume mai kwantar da hankali ya fara dukan kofofin hancin kowa dake cikin parlourn King, turaruka masu tsadar gaske da shegen kamshi momma ta sa aka kawo mata, sai Allah yasan daga ina ta samo waÉ—an nan zafafa turarukan ta feshe sirikarta da shi.
Tin su momma basu kai ga shigowa ba kamshin Mahnoor ya aiko masu sallama. Dikkansu sai da suka shaki kamshin suka ɗan lumshe idanu. Kowa ya fara rarraba idanu a kan hanyar shigowa, suna jiran suka ɓullowarta.
Like wow lokacin da suka sako kafafunsu a cikin parlon, gabaÉ—aya kallo ne ya dawo kansu. Momma na É—an rungume da Mahnoor É—in suka shigo, suna takawa cikin natsuwa.
Like wow tamkar wata tauraruwa haka Mahnoor ta haska, shigar kayan jikinta kawai suke kallah, Sarina alkyabbar kawai take kallah ma tukun nan, bata taɓa kallan irin wannan alkyabbar ba.
Mummyn Chuchu ce ta yi saurin miƙewa ta taro momma, dik da basu san wacece momma ta riko ba, amma suna da haɗin kan taimakawa junansu a irin wannan yanayi. Gefen Mahnoor ta zo ta rungumo suka karisa da ita ciki.
Mammie da tin da suka sako ƙafafunsu take ta faman leƙo fuskar Mahnoor tana san ganinta amma ba dama, dan alkyabbar ya yi mata yawa, hularsa ya fi kanta sosai, kunsan na faɗa maku na momma ce, dik da lokacin bikin momma ita ma da kaɗan ta fisu, amma dai ya yi mata yawa, hakan yasa hular alkyabbar ya sauko mata sosai, kuma ya haɗu da ta sunkuyar da kanta ƙasa, so ba'a iya ganin face ɗinta.
Ita kuwa Sarina bata kai ga batun face É—in amarya ba, tsadaddun kayan jikinta kawai take kallah, ta mutu da san alkyabbar, sai dai ba samu zata yi ba, dan na manyan mata ne wannan.
A gaban King suka kawota, mama sai binsu da kallo take yi, bare Mammie da ta saki baki ta rasa abin faÉ—e kamar wata gaula.
Dama King, uncle Abbas, uncle Jahiz a saman kujerar ɗaya suke zaune mai zaman mutun uku kenan, so a gabansu Mahnoor ta zube gwiwowinta kanta a ƙasa.
King ne ya fara cewa Momma ta kaita wajen Akka tukun nan, su fara gaisawa da Akka. Ƙara ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya da kyau Akka ta yi, Queen mother zata yanke hukunci e mana, Akka tamu ta amana.
Rikota mummyn Chuchu ta yi, ita ta kaita gaban Akka ta durkushe gwiwowinta. Sannan suka koma saman sofas É—insu suka zauna. ÆŠago idanu Akka ta yi ta karewa su Momma kallo kamar na mintu biyu, sannan cike da izza ta ce.
"Ina Zunaira?"........ Dum dum kirjin kowa dake cikin parlon ya buga except Mammie and Sarina, babu wanda ya taɓa expecting Akka zata nemi Auta a yanzu, nan fa parlon ya koma kallon kallo a tsakaninsu, an rasa mai iya bawa Akka amsa, dan sun san dik amsar da zasu bata ba zai taɓa gamsar da ita ba, babbar magana.
Tsit parlourn ya yi tamkar uwar gulma ta yi cikin shega. Can dai uncle Jahiz ya yi ta mazan cewa. "Zunaira bata nan, sun koma school".
Shiru Akka ta yi na Æ´an mintuna da zasu kai uku haka, sannan ta ce. "Amma kun san a bisa al'ada Zunaira ce take da damar buÉ—e fuskar amaryar ko?".......... Jinjina mata kai suka yi alamar tabbas sun sani. Ita dai momma shap ta mance da wannan al'ada, tabbas tasan kanwar miji ce kawai zata buÉ—e fuskar mata, amma ta mance da yake an jima ba'ayi biki ba a kingdom É—in. Kowa kuma yasan yadda bikin Jawad ya kasance cikin ruÉ—ani da tashin hankali, so ba'ayi dik wasu al'adu nasu ba, dan haka ta mance da batun.
Cike da isa Akka ta ce. "To shikenan tun da Zunaira bata nan sai ku mayar da amaryar taku sai lokacin da kuka shirya nuna mana fuskarta Zunaira ta zo ta buɗeta". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe.
Innalilahi, kallon juna suka shiga yi, dikkansu tinanin ta yadda zasu dakatar da Akka ta yi hakuri ta ga Mahnoor suke yi. Uncle Jahiz ya fahimci momma ta shiga damuwa sosai a kan hakan, sai ya yi saurin riko hannun Akka dama suka kusa, cike da kalaman yaudara ya ce.
"Haba Akka na, to menene banbancin Sarina da Zunaira? Ai dikkansu kannen Jaish É—in ne, dan haka ko ba Zunaira Sarina tana nan, sai ta buÉ—e mana amaryar ai".
Komawa Akka ta yi ta zauna, cike da isa ta juyo garesu domin ta sanar da su banbancin Zunaira da Sarina kwatsam idanunta suka sauka a kan uncle Abbas, aka ce idanun iyaye suna da kaifi a wajen da ake ƙoƙarin nunawa ƴaƴansu wani banbanci ko fifikon ko dai cin mutunci, ashe haka ne kuwa, ganin uncle Abbas yasa ta ji bata da kwarin gwiwar iya banbanta ƴaƴansa dana ɗan uwansa bayan kansu a haɗe yake.
Bata san abin da zai kawo masu rabuwar kai, dan haka sai ta ce. "Gaskiya ne babu banbanci, ke Sarina zo ki buÉ—e fuskar matan yayanku"...... Dik wanda ya ji maganar Akka a cikin parlon nan yasan ba daga cikin zuciyarta wannan magana ta fito ba, dik sun fahimci ganin idanun iyayen Sarina a wajen yasa ta danne bata faÉ—i banbancinta da Auta ba.
Wani irin takaici ne ya lulluɓe zuciyar Sarina, yanzu ace ita zata buɗe fuskar makiyarsu kishiyar Fanan? Gaskiya ko a iya haka an cuceta. Ita kuwa mammie ranta ne ya yi muguwar sosuwa, wato kenan ko a ina ƴaƴanta suna da banbanci da na King? Kenan ƴaƴanta ba koman komai bane ko a cikin dangi? Tin ba'a je ko'ina ba ana nuna masu su ba komai bane saboda ba babansu bane a kan mulki?.
A cikin zuciyarta ta furta lallai yazame mata dole ta tsaya tsayin daka domin mulkin kingdom of power ya dawo tsaginsu, ina ba zai taɓa yiwuwa su zama bayin wasu ba, dole suma su ci gashin kansu, ace har kakarsu da ta haifi ubansu da King ɗin tana ƙoƙarin ware ƴaƴan King daban dan shi ne mai rike da mulki, gaskiya ba zata yuwu ba.
Tabbas a nan Akka ta yi kuskure, kuma dayawa mata suna aikata irin wannan kuskure, sai kuga a gida an fi fifita ƴaƴan da ubansu ya fi abin duniya ko yake rike da wani muƙami, wannan babban kuskure ne wanda mun san kuskure ne amma muke aikatawa, Allah bai manta da talaka ba da ya barshi a talauci, haka zalika mai arziki ba wayau ya yi wa Allah ba da yasa ya bashi arzikin ba, dan haka ku daina irin wannan abin da kuke yi, wani ma zaku ga ko ubansu ne karami in dai yana da kuɗi to sai a nuna yafi kowa a gidan, ba'a yin haka wlh, hakan yana ɗarsa gaba da kiyayya a zukata, idan ba'a kiyaye ba sai shaiɗan ya shiga cikin lamurran, a haka ne sai ku ji ana cewa yaya ya kashe ƙaninsa ko ƙani ya kashe ƴaƴansa saboda abin duniya, dik ire iren wannan abin da kuke gani kamar ba matsala bane su suke hasasa waɗan nan abubuwa, dan Allah mu daina irin hakan ba abu bane mai kyau wlh, babu mai arzirtawa sai Allah, shi da yake talaka ai ba yin kansa bane, idan kuwa akwai mai bada arziki bayan Allah sai ku faɗa mun in ji!!!!!.
Shi kansa uncle Abbas ransa ya É—an sosu, amma ya danne ya nuna kamar bai fahimci in da Akka ta nufa ba, shi ma uncle Jahiz ya ji wani irin, amma dik suka danne.
Miƙewa Sarina ta yi tana wani ɓata rai ta nufo Mahnoor. A kule ta sanya hannu ta janye hular alkyabbar baya kamar ma da mugunta ta yi abin. Dan yadda ta ja hular har sai da kan Mahnoor ya ɗan jinjiga.
Mummyn Chuchu ce ta ce. "Sarina menene haka? Haka ake buÉ—e fuska?".
Mammie ce ta tari numfashin mummy da cewa. "An kinsan bata iya bane, kinga ba'a taɓa biki a gidan nan da wayonsu ba sai bikin Jawad wanda shi kuma ba'a nemi kannensa na jini dan gudanar da komai ba, ina ga da yake amaryar yar gata ce kannenta ƴan gata akasa suka yi mata komai".
Wani irin gabaɗaya parlourn suka ji na jin kalaman Mammie, mamaki abin ya bawa King, shi kuma uncle Jahiz ya fahimci kamar abin da Akka ta yi mata ne ya bakanta ranta, momma kam da tasan komai ko kallo basu isheta ba, maman Aneesa dik rashin son zaman lafiyarta da izzarta sai da kalaman mammie suka ɓata mata rai, ga shi dai ba shiri take yi da kishiyoyin nata ba, amma da aka gasawa mummy magana sai ta ji zafi.
Dan haka sai izzar sarautar tata ta motsa. Cike da izza ta ce. "Ke saboda baki da hankali Umaima ɗin kike yi wa martani gatsau haka? Sa'arki ce ita? Shin dake ma ta yi magana ne? Ko kece Sarina? To maza ki bata hakuri kafin ranki ya yi mummunar ɓaci". Mama manya, mama harkar izza ba wasa, bata ɗaukar wargi ko ba a kanta ba.
Momma ta É—an yi mamakin faÉ—ar da mama ta tarewa mummy, dan sun san juna kar tu kar.
ÆŠaura kafa É—aya bisa É—aya Akka ta kara yi, a kadarance ta ce. "Yauwa ku cigaba, ai na faÉ—a maku idan baku yi haka ba ba mata bane ku, ku cigaba da kyau".
Shi dai uncle Jahiz dariya ma abin ya so bashi, wai yau mama ce ta da tare wa kishi faÉ—a, tab abin babba ne.
Harara Mammie ta wurgawa Akka ba tare da kowa ya lura ba, a cikin ranta ta ce shegiyar tsohuwa idan baki yi hankali ba ni ce nan ajalinki. A fili kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa mummy. "Kiyi hakuri".
Wato akwai iyashege a kingdom É—in nan, wlh matan King sun san kan duniya.
Jiki ba kwari Sarina ta bar gaban Akka ta koma mazauninta zuciyarta na tafasa, mammie ta ƙara jin ranta ya ɓaci, ta kara jin lallai dole ta mallaki kujerar kingdom of power ko ta halin yaya ne, da yanzu ita take da mulki a hannunta ai wane kaniyarsu su yi mata abin da suke yi mata ɗin nan.