Sashe 39
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Uban me kuke tsaya yi mun a tsakar gida kuna wani yi mun koke koke na munafurci zaku hanani shaƙatawa".
Jumma uwar rashin kunya idanunta a tsaitsaye kar ta ce. "Kai dama idan za'ayi wa mutum kishi shakatawa yake yi kenan?".
Zaro idanu Mahnoor ta yi, ai bata san lokacin da ta dakatar da yin kukan nata ba, lallai Jumma bata san bala'i da ake yi a wannan gida a kan wannan kishi da za'ayi ba ne! Da ba zata yi magana ba!.
Fusata Nenne ta yi, ranta ya sosu da jin kalamar Jumma, sai dai ba halin ta yi mata komai, saboda su fa ba ƙaramin aikinsu bane yanzu idan ta daki Jumma mijinta ya zo ya ci uban Nenne ɗin, su mazansu sun iya tarewa matansu faɗa, kai ko yaransu ka daka ba zaman lafiya har sai sun rama.
So Jumma matar aurece a yanzu tana tsoron dukarta bata san ya halin mijinta yake ba, kila mai tsauri ne a kan iyalansa.
Jumma da ta ga Nenne bata kulata ba sai ta ja hannu Mahnoor suka raɓa jefan Faisal suka koma cikin ɗakin.
A saman mattress suka zauna, hannu Jumma tasa tana goge mata hawaye tana cewa ta yi shiru yanzu ai ta zo zasu yi shawara a kan mafita, dan haka ta yi shiru suyi magana.
Ƙoƙarin danne kukan nata ta yi, amma abin ya ci tura, ta kasa dannewa, dan hawayenta cigaba da fasowa suke yi.
Tun Jumma tana goge mata hawayen har ta rabu da su kawai, dan sun ki tsayawa.
Cike da tausayawa ta ce. "Mahnoor yanzu kukan ne kike yi fisabilillah?".
Kifa kanta a saman gwiwonta ta yi, tana jin tamkar an É—aura zuciyarta a saman wuta mai cin bala'i ne, cikin kuka da É—an É—aga murya ta ce.
"Jumma bappa ya ce zai raba aurena da Hamma a aura mun hamma Faisal..........."
Wani irin rushewa da kuka da ta yi ne ya ja ta haÉ—iye sauran maganganun ta kasa amayar da su, saboda ba zata iya karisasu ba, wato yanzu ba kukan rashin Jaish É—in ba ma take yi, kukan raba aurenta da shi take yi, Allah sarki abin ya haÉ—u ya yi mata yawa.
A lokacin kuma Faisal ya wuce ya bar gidan saboda Nenne, yana tsoron bala'inta, sai ya kama kansa kawai ya haƙura, kuma Jumma tazo yasan zata rarrashin mashi Mahnoor ɗinsa.
"Haba mana bappa, ina hakan ba zai yiwu ba, gaskiya kada ki yarda a raba aurenki da hammanki, ina da tabbacin In Sha Allah zai waiwayeki, ai so ba karya bane, tabbas dik in da yake yanzu haka yana tinaninki, ba zai taɓa jefar dake ba komai zai faru"............ Cewar Jumma!.
Wannan magana ta Jumma ta yi dai'dai da lokacin da Jaish ya ke ƙoƙarin kwanciya a saman katafaren bed ɗinsa, ya yi wanka yana sanye da three quter jeans white color and white singlet masu kyau, ya yi matuƙar mamakin ganin yadda gashin kansa ya yi yawa, sai dai bai kawo a ransa ya yi rayuwa a wani waje ne dayasa gashin ta taru sosai saboda rashin datseta ba, ya wanke kansa kawai ya gyarata da mayukansa masu kyau da tsada.
Sai dai fa wlh gashin da ta yi yawa ta yi masifar yi mashi kyau, shi kansa ya shaida ta yi mashi kyau, hakan ce ma yasa bai wani damu da yawan gashin ba, sai ya ji ma kamar zai iya barinsa ya cigaba da kashe mashi kuɗi kawai dan ya yi kyau matuƙa.
Rage gudun Ac ya yi, ya kwanta kenan sai ya fara tunanin ina wayarsa zai kira number Zunaira ya ce ta zo.
Kada ku manta wayar tasa tana hannnun Mahnoor. Miƙewa tsaye ya yi ya fara bincikar ina wayar tasa take?. Ko'ina ya duba bai gani ba.
A bakin bed É—insa ya koma ya zauna, shiru ya yi yana tunanin in da ya jefar da wayar tasa, É—an lumshe idanunsa ya yi ya fara tariyo baya dan ya iya gano ina wayarsa take?.
Dai'dai lokacin King and Momma suka shigo cikin ɗakin, uncle Jahiz yana biye da su a baya, hakan ya dakatar da shi daga tinanin da yake ƙoƙarin yi na a in da ya jefar da wayarsa.
Ita kuwa Jumma cigaba da karfafawa Mahnoor gwiwa ta yi a kan Jaish zai waiwayeta, dan haka dik bala'in da za'ayi kada ta yarda a rabata da aurensa, dan shi kaÉ—ai ne garkuwanta kuma gatanta bayan Allah kenan.
Ta yi na'am da zancen Jumma, dan haka sai ta É—aura É—amarar gayawa bappa ba zata iya rabuwa da Jaish ba, ta kuma ji daÉ—in zuwan Jumma, har ta ji ranta ya É—an sanyaya.
Da kyar ta goge hawayenta ta kuma dakata da yin kukan, har da ajiyar zuciya. Jumma ganin ta yi nasarar dakatar mata da kukan yasa ta fara ƙoƙarin kawo mata hira masu daɗi da zai ɗebe mata kewa.
Cikin hiran nata ne ma ta sanar da ita tana da ciki har na tsawon wata biyu da sati biyu, sosai Mahnoor ta tayata farinciki, ta ji daɗin maganar matuƙa.
Haka suka cigaba da yin hira tana bawa Mahnoor shawarwar haÉ—e da kara mata karfin gwiwa a kan ta dage ta tsayawa aurenta, kada ta yarda a farraka mata shi.
Sosai Jumma ta so jin kwakkwaf a kan ko dai ita ma Mahnoor tana da cikin Jaish ne, ko kuma sun taɓa kwanciya, amma ina Mahnoor taki yarda da faɗa mata komai, da zarar ta kawo zancen Jaish Mahnoor zata doje taki yarda su yi ta.
Daga karshe Jumma ta fahimci Mahnoor fa ba zata faÉ—a mata ba, sai kawai ta hakura, a tinaninta iya kunya ce kawai tasa Mahnoor bazata sanar da ita ba, bata san ba haka bane, Mahnoor tasan wannan sirrin mijinta ne shiyasa taki yarda ta faÉ—a, sai dai su yi hira na iya labarin da ya shafi kauyen, amma Mahnoor bata yarda a shigo da hiran Jaish ba, da Jumma ta sako maganarsa bakin Mahnoor zai fara haila ta ki bata amsa, sai ta yi kamar bata ji me ta ce ba, daga karshe ta kawo wani zancen ta É—aura a kai.
Har sai da mangariba ta kawo kai, sannan Jumma ta tafi ita kuma Mahnoor ta fito ta kama aikin da ta saba.
A tsakar gida ta isko Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi kamar dai É—azun a gona, shi kuma bappa ya wuce masallaci daga nan ya wuce gidan ArÉ—o dan su yi magana a kan Mahnoor É—in.
After some days. Bayan wasu kwanakin.
An É—aura auren bappa da Mairo tamkar yadda aka ce, yanzu saura tarewa, kwana uku kenan yau da É—aura auren, babu wani biki da suka gudanar saboda na faÉ—a maku ita ba budurwa bace, so iya É—aurin aure ne kawai sai kuma wannan al'adar tasu da suke yi nahawa dutse dan a rubuta sunan ma'aurata, wannan dole ce a wajensu, sannan sai al'adar da suke yi na yanka shanu ayi ta gashi, a can gidansu Mairo kuma an yi al'adar da iyaye da makota suke yi wato a tara nono da fura dayawa ayi ta sha, kowasu makota ranar ba zasu sayar da nono da furansu ba, zasu haÉ—osa a kawo gidansu Mairo, shi ne nasu gudumawar.
Dik bakin da zasu zo sai su yi ta sha babu kakkautawa.
So iya abin da aka gudanar a bikin kawai, Mahnoor dai bata je wajen bikin ba, tana wajen Inna kakarta, Mahreen kuwa da bata ga abin da zai hanata zuwa wajen biki ta ci uwar sabada ba ai sai da ta je, ta ci uwar kyalliyar powder gora guda ta zazzage a face É—inta abinta, kamar aljanar asuba, amma saboda bala'inta kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau sosai, kuma karya suke yi ba wani kyan da ta yi, kawai suna tsoron bala'inta ne yasa suke yabata É—in munahikai. Kaki yabata ka shiga uku.
Har da su Jumma sun je bikin, sun kuma yaba kyan Mahreen Æ´ar amarya kenan, dan ita ta gama shaidawa kauye yanzu ita yar Diddi Mairo ce ba Æ´ar Nenne ba, wato a duniya yarinta ma fa duniya ce, ba abin da ya kai shi daÉ—i, ta dai ce ita Æ´ar Mairo ce, ta koma tsagin amarya.
Kwanaki uku ana ta hidima, yau za'a kawo Mairo É—akinta ko in ce zata tare a É—akinta, bappa bai yi mata wani É—aki na daban ba, ya ce a É—akinsa zata zauna, so nan kawai ya gyara mata, yaki yi mata wani bukkar.............. Ni Princess Teema na ce anya bappa ba É—an duniya bane kuwa? Wato so yake bakinciki ya kashe Nenne ko? In ba tsabar minahinci ba ita ma ya yi mata É—akinta daban kamar Nennen mana! Me na wani ta sauka a nasa É—akin?.
My people's kuzo mu yi gulma, anya ba maman Mahnoor bawan Allahn nan yake gani a tattare da Mairo ba kuwa? To mu dai yanzu zamu koma team uwar gida Nenne dan mu taya Nenne faɗa, haba wannan wani irin bala'i ne, yar cikinta ma ta gujeta ta komawa amarya, to mu ba zamu yi lamurje ba.🙄
To izina garemu mata, shi dai bakin hali yana raba ka da kowa, ciki harda Æ´aÆ´an da ka haifa a cikinka, ya rage naku ku kyautata zamanku da kowa, ku zaku ji daÉ—i idan kuka iya zama, kai in fa kuka zauna da kowa lafiya wlh sai kunfi abokan zaman nakuma cin ribar zaman, ina fatan kun É—auki darasi?!!.
Wato akwai dirama a gidan bappa fa, dan kuwa ko da Æ´an uwan Mairo suka kawota basu kwashe ta daÉ—i da Nenne ba, dan kuwa irin wanna nasiha da ake yi ace an kawowa uwar gida amana nan da suka zo zasu bawa Nenne amana ta yi masu wankin babban bargo, har da cewa su dai kaiwa bappa amana tin da shi ya rakitimowa kansa ita kuma yake ganin zai iya, dan haka a kai mashi ba dai ita ba!!!.
Ta ci masu mutunci fes, dik da haka kuma bai isheta ba, da taga basu kulata ba sun nufi cikin É—akin bappa sun kai Mairo suna karisa mata jeren da basu gama na.