← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 242

Sashe 177

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga wata katanga dake ɗauke da gicciye-gicciyen bayi da aka kashe don tsoratar da mutane birnin su yi biyayya dan dolensu, in ba haka ba su bi sahun waɗan da aka gicciye suma. Ƙofofin fadar guda uku ne kuma gabaɗayansu suna da ƙaho na zinariya, dik wanda baa bashi izinin shiga ba ya keta ƙofar, fatar jikinsa za ta ƙone nan take, tsabar karfin tsafin Queen Zarina.

Gidajen bayi a cikin kingdom ɗin suna a cikin duhu, babu haske, babu kwanciyar hankali, ana ɗaure su da sarƙoƙi, ana azabtar da su idan suka yi ba daidai ba. Ana azabtar da mutanen da suka yi laifi a wurin, wasu ana yanka su, wasu ana narkar da fatarsu da wani abin sihiri nata dan nuna barazana ga ƴan baya tare da tilasta masu dole su yi biyayya ko kuma suma su riski irin wannan tsastsauran hukuncin. Qeen Zarina tana da wani ɗakin sirri da ke ƙasa (underground) wanda ke cike da abubuwan al’ajabi, kamar wurin bautar da jini dan ƙarfafa mulkinta da sauransu.

Suna da ƙasashe da yawa da suka mamaye, ana bautar da mutanen waɗancan ƙasashe a matsayin bayi. Dik wata ƙasa da ta ƙi biyayya, suna kisan jama'arta gabaɗaya ko kuma su tilasta wa yara da matan su zama bayin fadarta masu yi mata hidima. Queen Zarina ita ce uwar zalunci, tana amfani da doka mai tsauri dan riƙe ƙarfinta. Ba wanda zai iya yi mata ƙarya, domin tana da sihirai da sirri mafi ƙarfi da zata iya gano karya suke yi mata, dan haka dole yake tilastawa mutanenta faɗa mata gaskiya koda sun san kashesu zata yi.

Tana da Jagororin mabiyan sihirinta. Wata macece mai suna bokanya Ruhgara, da ke kula da manyan bokaye da matsafa da ke fadar Queen Zarina. Su ke tabbatar da cewa dik wanda aka kama yana tunanin cin amana, sai a hallaka shi kafin ya yi wani abin.

Ana kiran shugaban warriors ɗinsu da black scorpion, wato bakin kunama mai harbi ɗaya sai lahira. Warriors ɗinta ba mutane ne na yau da kullum kamar yadda kuka sani ba, a'a ita ta ƙunshi mayaƙa marasa tausayin da aka horar tun suna yara don su zama na musamman, gabaɗa warriors ɗin renon black scorpion ne.

Mai tsaron dukiyarta. Wanda ke kula da taskar zinariya, azurfa, da kayan sihiri da aka kwace daga ƙasashe da suka mamaye, wani bakin mutum ne, mai hudun launin fata sosai, ga shi shirgege gwanin ban tsoro, mummunar gaske, fuska babu alamar annuri ko ɗigo, in ya yi maka duka ɗaya sai mutuwa, yana da faɗi sosai.
Sannan warriors ɗinta mutane ne da suka haɗa da, mayaƙan Jini wato mutanen da aka yi wa wani sihiri mai karfin gaske, suna jin karfi da lafiya ta yadda suke ganin babu wani bala'i da zai iya shafan su, kuma idan aka sare su, jinsu na iya dawowa su cigaba da yaƙi, wato saboda da tsafi suke amfani ko an saresu suna iya tashi su koma normal yadda suke su cigaba da yaƙi, waɗan nan mayaƙa ne masu haɗari wanda har yanzu tana kan sihircesu ne, bata fara amfani da su ba, sune mayaƙanta na rukunin farko a ɓangaren haɗari. Wlh ba dan kingdom of power masarauta ce ta Allah sun riki addini ba da ba zasu taɓa sha a hannun wannan azzalumar mata ba! Makircinta ya zarce yadda kuke tinani!!.

Akwai masu take masu baya, wato su kuma mutane ne da aka horar tun suna ƙanana dan su zama tamkar dawakai a fagen karfi dik dan su zama masu saurin kashe mutane babu imani babu tausayi. Maza da mata da ke ɓoye suna satar sirrin wasu ƙasashe domin tabbatar da babu wanda zai iya yin juyin mulki, shiyasa kuka ga har cikin kingdom of power suna da ƴan leken asirinsu waɗan da suke binciko masu menene ke wakana a manyan masarautu.

Magana ta gaskiya babu wanda ya isa ya yi masu tawaye. Mutane basu da ƴanci. Dik wanda aka samu da yunkurin yin tawaye, daga shi har danginsa dikka sai an hallaka su. Basa son wata daula ta yi ƙarfi ko kwatansu. Dik wata ƙasa da take kokarin girma ko samun ƴanci, warriors na masarauta suna zuwa su mamayesu su kuma kwace komai. Yadda kuka san Queen Zarina renon BLACK TIGER ce, wlh zalincinsu kusan ɗaya, sai dai Black Tiger ya fita haɗari ne da karfin tsafi.

Sannan tana sihirce mutane. Idan aka samu wani yana tunanin cin amana, mayakan sihiri suna iya hango hakan kafin ma mutum ya furta shi, sai ta sa a sihirce sa, a mayar da shi wani gunki ko kare ko dai wata ƙasƙantacciyar dabba a ajiye shi a kofar gate ɗin farko na shigowa masarautar dan ya zama ya kare a kaskance kuma ya zama izina ga masu tasowa. Wanna ba dalilin yasa ƴan birnin suke yi mata biyayyar dole!.

Masarautar tana da zinariya fiye da kowacce ƙasa except birnin BLACK WORLD. Sannan a tsarin Queen Zarina babu wata ƙasa da za ta iya yin ciniki ko kasuwanci ba tare da izinin ta ba, muna magana a kan kasashen da ta mamaye, kasuwancin dik waɗan da suke kewaye da ita a karkashin sarrafawarta suke yi. Bayin basu da wata ƙima da daraja, a haka kuma wai sun fi talakawar da ake mulka kima, idan ka zama bawa a wannan kingdom ɗin, to ka san rayuwar ka ba taka bace. Wannan kingdom da fadar Sarauniya tana da ƙarfi fiye da sauran ƙasashe. Za su iya mamaye kowace ƙasa, kuma babu mai iya taka masu birki sai KING ZUHAIR, wato KINGDOM OF POWER sune kawai suke zama babbar barazana ga ZARINA! Black Tiger kam bai ma san da wanzuwan Zarina a doran duniya ba!.

Doka mai tsauri, dik wanda yayi gaban kansa ko ya yi magana kan zalunci, ana hukunta shi da azaba mai tsanani. Masu iko sunfi kowa daraja. Dik wanda ba shi da arziki ko gata, rayuwarsa bata da kima. Ana amfani da bayi da kuyangu. Akwai kasuwannin bayi da ake siyar da su kaman dabbobi, kuma manyan gidaje sun cika da kuyangu da ke aiki ba dare ba rana kamar injuna.

Mu leƙa cikin fadar Sarauniya ZARINA mai cigiɓi cigiɓin nau'ikan azaba. Babban gini ne mai girma da ɗan duhu. An gina shi da baƙin dutse na zinariya, yana da hasken fitila ja da launin shunayya. Akwai manyan azurfa da zinariya da aka ƙawata ginin da su. Sarautar ta tara dukiya daga harajin da ake karɓa daga talakawa da ƙasashen da suka mamaye, bayin Allah su sha wahala su yi noma sai su karɓe kaso biyu cikin uku na amfanin gonar su barsu da kaso ɗaya wai haraji, hakan yasa rumbun hatsin QUEEN ZARINA ya cika har yana amai da kayan abinci, girman wannan rumbu kuwa ya kai girman gari guda daga cikin garuruwan kasar. Amma hegiyar matar nan bata sadaka bare kyauta, gara ta bar abincin ya yi ta cike koma lalacewa ne ya yi a kan ta bawa talakawa!!.

Fadar ta cike take da bayin dake hidima. Kowanne yanki na fadar akwai kuyangu da bayi masu bauta mata. Babban zaure mai girma. A nan ne take karɓar baki da shari'a, akwai dogarai masu sanye da rigunan karfe da takubba kamar warriors. Sai ɗakin sirri a cikin fadar, wani ɗaki ne da ba kowa ke da damar shiga ba, anan ne take shiryawa ko boye wasu sirrikan mulkinta.

Bari mu taɓo tahiri a kan Queen Zarina wadda kuka jima kuna jin labarinta ba tare da kun san menene ainahin tsamar dake tsakaninta da Kingdom of power ba, bama ku san wacece ita ba, shin yarinya ce, babba ce, matar aure ce, ko dai bazawara or budurwa, dik baku sani va, to yanzu labari ya juyo ta kanta, bari mu faɗa maku ya take domin yanzu story zai juyota.

Kingdom ɗin nan ba kawai mai arziki bane, yana da cikakken iko a duniya. Nasan ko a iya haka kun fahimci dalilin da yasa a koda yaushe suke cikin takun saƙa da King Zuhair, dan shi baya barin mulkin zalinci ta cigaba da tafiya.

Tabbas kujerar mulkin da Queen Zarina take zama banbancinsa da na King Zuhair kalilan ne, ita ma nata diamond seat ne, sai dai na shi ya fi nata girma sa ƙawatuwa. Ta dake saman kujerar nan tana haɗe cikin alkyabbarta launin gold mai daraja, ba karya kyakkyawar gaske ce, zubin Iceland lady, jajir da ita kamar ka latsa jini ya fita, ga gashin kanta light brow, ka zalika kwayar idanunta light brown, babbar macece ba yarinya ba, ko dai in ce uwa, sai dai yanayin zubin halittarta zaka yi zatan irin ƴan 25 to 30 years ɗin nan ne. Da ka kalli face ɗinta kaga zallar madarar rashin imani, babu annuri kuma babu dariya ko kaɗan, doguwa ce sosai dik da take a zaune, kun san matan Iceland da shegen tsawo sosai Masha Allah.

GabaÉ—aya amintattunta da manya manyan bokayen cikin fadarta suna ciki, daga gefen damarta wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce zaune a saman kujera ta mulki irin wanda Queen take kai, sai dai nata kujerar bai kai na Queen girma, kima da kuma daraja ba. A shekaru yarinyar nan ba zata wuci 17 years ba, ta tsantsara kyau cikin shiga na Æ´aÆ´an manya manyan sarakuna da ake ji da su, ba karya kyakkyawar yarinyar ce irin uwarta sak.

Wani kamshakin dakakken namiji mai kirar lafiya da karfi ne ya danno cikin fadar, cikin tafiyar jarumta da nuna isa, yana cikin shiga irin na manya manyan sarakuna masu karfin iko, da ka gansa babu tambaya kasan basarake ne, jiga jigan warriors huɗu suna take mashi baya har ya ƙariso saman stage da Queen take, yana shigowa gabaɗaya manyan cikin fada suka miƙe tsaye except Queen and her daughter.

A saman kujerar gefen damanta ya zauna, yana zama kowa ya koma ya zauna, yana zama bai fi da minti biyu ba sai ga wani zaƙwaƙurin cikakken namiji mai zubin jarumta shi ma ya shigo, da alama family ake san haɗawa kafin ayi abin da za'ayi, dan wannan matashi ma dai falimy ne, saboda shigar dake jikinsa irin ta Prince.
Chapter 177 · 0% Book details