Sashe 236
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yanzu kwakkwaran shiri suke shiryawa mai zafin gaske wanda suka ɗaukarwa Queen Zarina alkawarin zasu salwantar da jinin mutum ɗaya daga cikin ƴaƴansu ko ƴan uwa domin ta yi masu bakin sihiri a kan jinin King Zuhair, to dama kun san ZARINA tana kullace da kingdom of power, aikuwa ta yi gaggawar aminta da wannan shiri, ta kuma rattaɓa alkawarin zata yi masu aiki, yanzu Mammie tana cikin zulumi da damuwa matuƙa a kan waye zata sadaukar da jininsa ga Zarina? Ba zata iya bada jinin Sareena ba, saboda sheɗancinsu ɗaya, Sareena tana bin abin da take so, kuma ƴaƴa biyu gareta, yanzu dole ta sadaukar da jinin Fanan muddin tana son cikar burinta!!! Uhm ana tashin hankali ba kaɗan ba a Kingdom ɗin nan.
Sareena kuwa tana can har da zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda uncle Abbas ya faɗa mata cewa ya bada aurenta ga Smart, sai murna take yi, har da wani cewa yanzu lokacin cin uban dik wanda ta gani a part ɗinsa ne, dan shi ɗin mallakinta ne ita kaɗai, sai tsantsara kwalliya take yi zata je wajensa, wai fa ba shi zai zo hira ba, ita zata je wajensa, dik da a tsorace take da shi, amma tana da kwarin gwiwa a kan yakininta, ta yi imanin ba'a jin daɗi sai an sha wahala, kuma ta yi imanin yanzu babu abin da zai yi mata tin da har ya karɓi aurenta hakan na nufin yana sonta, bata san cewa shi bai ma san wainar da ake toyawa ba!!.
Shi kuwa Kamran an kaisa part na baki, commander ya sanya tsaro a kansa sosai, sannan anbashi kulawa a matsayinsa na bakonsu, sun bashi abinci mai rai da lafiya, sun kuma tsaya mashi ya yi wanka ya canza tamkar ba shi ba, ya fito a ainahin yaron mammarsa, babu abin da yake ransa face tinanin Pretty, baya tinanin mammarsa kamar yadda yake tinaninta, saboda yasan mammarsa mace ce da zata iya tsayawa kanta a kowani hali, jaruma ce kuma sadaukiya, so Pretty kuma macece mai rauni da bata san kanta ba bare har ta san me duniya yake ciki, tinanin twins ne kawai a ransa, tsawon waɗan nan shekaru biyun bai taɓa yin minti biyu ba tare da ya tuna amanarsa kuma twin's ɗinsa ba, suna ransa tamkar yadda yake a ran Sweetie, kunga kullum tana tinaninsa, amma Pretty ko maganarsa bata yi, ko da yake ita yarinya ce da ba zaka taɓa iya gane cikinta ba, bata magana bare kasan ina ta dosa, waya sani ko tana tunasa bayyanawa ne kawai bata yi!
My people's, KAMRAN team, ina mai baku hakuri a kan abin da ya faru, kun san bana yin abu haka kawai sai da kwakkwarar dalili, na san kun ji zafin auren Pretty da Smart, amma nasan idan kuka ji dalilina da kanku zaku jinjina mun, tafiyar yanzu ta fara, kada ku manta yanzu muka gota tsakiya kaɗan, ina da dalilina mai karfi na yin hakan, amma kun kusa ji soon!! Ku yi wa KAMRAN fatan samun wacce zata kasance alkhairi a garesa, ba son rai'na bane nike raba masoyan nan, dalili yake sanyawa!! Amma kada ku damu a karshen page ɗin nan zan faranta rayukanku!......🙌💘
*CROWN OF JUSTICE*🔥🔥
Katafaren government house na ƙasar, zaune dattijo MUZAFFAR yake a saman wani dandatsetse kuma lallausan kushin mai bala'in tsada a cikin katafaren parlournsa, yana rike da wani littafin mai suna The Franklin scandal yana karantawa, yana cikin shigar manya-manyan malaman larabawa masu kima da mutumci, fuskarsa sanye da farar glass, ya sha rawani mai bala'in kyau na manyan malamai, farin balarabe ne tas wanda da ka gansa kasan mutumci da kima game da kyau haɗe da dukiya sun yi mubaya'a a wannan waje. Daga bakin kofa wasu zaƙwaƙuran securitys ne ke gadinsa, ya natsa cikin karatun da yake yi sai ji ya yi an yi mashi sallama.
Cikin sanyin murya ya amsa, murya mai cike da dattaku da kima. Wani security ne ya shigo cikin parlourn, with full respect ya ce. "Sir Prince Rishan ne yake neman iso"....... Gyara zamansa cikin natsuwa dattijo ya yi kafin ya ce. "Ka ce ya shigo"....... Sara mashi securityn ya yi alamar girmamawa kafin ya juya ya nufi waje. Yana fita bai fi five seconds ba sai ga Prince Rishan ya shigo cikin shigarsa ta alfarma irin ta Æ´aÆ´an manya manyan sarakuna da ake ji da su. Zuba mashi idanun dattijo ya yi yana kallonsa har ya kariso, a saman kushin da yake zaune ya zauna, amma kafin ya zauna sai da ya duka kasa, dik wata sarauta ya ajiyeta a gefe ya tsugunna a gaban dattijo ya kwashi gaisuwa. Hannu dattijo yasa ya shafi lallusan gashin kansa kafin ya amsa gaisuwar.
Kusa da shi ya zauna, kallo É—aya dattijo ya yi mashi ya gane cike yake da damuwa, dan haka sai ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye a gafe, sannan ya juyo da hankalinsa game da natsuwarsa a kan Prince Rishan. A natse ya ce. "My son akwai wata damuwa ne?".
Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Papa akwai damuwa sosai ma, amma papa please meyasa baka san faÉ—a mun gaskiyar lamari a kan waÉ—an nan mutane biyu?". (Ude and Zarina yake magana) Dogon ajiyar zuciya Papa ya sauke kafin ya ce. "Rishan tono gaskiyar babu abin da zai kareka face bakinciki, koma menene ya rigada ya wuce, ka bar maganar, yanzu ina Rishma?".
Ciki ciki ya amsa da tana gida, da alama ransa bai so amsar Papa ba sam. Wai menene gaskiyar da Rishan yake son sani?. Batu ne a kan mutuwar babansa wanda yake zargin kashe shi aka yi, dan shi bai samu damar ganin gawarsa ba, a lokacin da abin ya faru baya nan, kuma zarginsa gaskiya ya ce, dan familyn Thomas ne suka kashe shi, wato familyn Zarina kenan, ita ta yi poisoning na King Ranveer da hannunta, poison ɗin kuma daga hannun mahaifinta Thomas ya fito, so ita ta kashe sirikin nata, domin kawai Ude ya karɓi mulki ita kuma ta kwace, burinta kuwa ya cika, sai dai ta bar baya da kura, domin kuwa Papa ya san komai, ta so rufe mashi baki amma abin ya ci tura, shi kuma Papa yanzu abin da yasa baya son bayyana gaskiya saboda Rishan shi kaɗai ne, ba zai iya yaki da su ba, zasu cutar da shi ne kawai, dik da suna bala'in shakkarsa da tsoronsa, amma aka ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, Papa yana ganin kamar zasu iya cutar da Rishan and Rishma, shiyasa ya ki faɗa masu gaskiya, har yau Rishan ya gagara samu natsuwa, zuciyarsa tana faɗa mashi lallai dole ya nemo waɗan da suka kashe babansa. Kun san meyasa na baku wannan tarihi? Saboda a gaba kaɗan zaku tsinci kanku a alaƙa da wannan tarihi, bana son ina gaba in dawo baya shiyasa na faɗa maku a nan kawai, dan a gaba ba ɗauko tarihin daga farko za'ayi ba, za'a ɗaura ne daga kan in da Rishan ya tsaya!.
And Papa yana zargin da sa hannun Ude a kashe King Ranveer, saboda bai yarda Zarina kawai ta kaddamar da wannan aikin ba!. Lallaɓa Rishan Papa ya rinƙa yi har ya hakura ya daure ya sake suka sha hira da Papa ya mance da batun su Zarina, sai dai a karshe da ya tashi tafiya ya ce da Papa. "Papa zan kashe Ude tin da yaki komawa musulunci, kuma kasan hukuncin wanda ya yi ridda!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita.
Miƙewa tsaye Papa ya yi, sai da ya gyara alkyabbar jikinsa, sannan ya gyara glass ɗinsa kafin ya ce. "Kada ka yi saurin yanke hukunci Rishan, ka kara mashi lokaci zuwa nan da ko ƴan watanni ne, idan babu haske sai mu san hukuncin da zamu yi mashi, koba komai yayanku ne".
Kun san me my people's, wlh ba dan Rishan baya shiri da su Zarina baya taimaka masu ba, tabbas da babu wanda zai iya cinsu da yaki, saboda shi ɗin namiji ne kuma jarumi ne, tamkar yadda kingdom of power suke da commander Zafar, haka jarumtarsa yake, tsab Rishan zai iya kayar da commander, saboda commander Zafar ya tsufa, shi kuma sabon jini ne, amma Zarina saboda rashin wayo insert of ta kallaɓasa ya zama mai tsaya masu wai take faɗa da shi, ko da yake shi ma ba zai yarda ba, dan ya tsaneta tin kafin Ude ya aureta, tun yana yaro ya tsaneta sosai!.
Jinjina kai ya yi tare da cewa. "A kullum kai kake dakatar da ni Papa, kuma In Sha Allah ba zan taɓa gajiya da bin umarninka ba". Ɗan kara sakin fuska Papa ya yi haɗe da cewa. "ALLAH ya yi maka albarka Rishan, In Sha ALLAH kana cikin kariyar UBANGIJI babu abin da zai sameka, sannan zaka kasance cikin farinciki, na gode kuma na yi murna da har yau baka cireni a matsayin uba da ka ɗaukeni tin King Ranveer yana raye ba, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, ka kula da Rishma sosai, ka tsaya da taka tsantsan".
Amin ya amsa da shi tare da juyawa zai fita, har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo, ya yi mamakin ganin yadda Papa yake yawan kallonsa a kullum idan ya zo zai tafi. "Papa meyasa kake yawan cewa in kula da Rishma da kai'na?". Ya jefa tambayar cike da sa ran zai samu amsar da yake so, dan abin na damunsa ta yadda ko a waya ya kira Papa sai ya ce mashi ya tsananta kula sosai, abin ya fara É—aure mashi kai.
Murmushi irin na manya Papa ya yi dik dan ya kwantar mashi da hankali kafin ya ce. "Babu komai, kawai ina so ne in tabbatar da amanar da King Ranveer ya bani na rike amanar sosai, dan haka ka kula, ba zan gaji da faɗa ba, dan amanace ku a gareni!!". Shiru ya yi tare da juyawa ya cigaba da tafiya, ko kaɗan bai gamsu da amsar Papa ba, ya dai yi shirun ne kawai, kuma hakance, Papa na ɓoye mashi gagarumin gaskiyar da yakamata ace ya sani, amma Papa ya dubi abin ta wata fuska ta daban shiyasa ya ɓoye!.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Bayan wani lokaci.