← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 242

Sashe 28

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita ma tin zuwanta duniya take shan wahala har ta koma ga Allah, aurenta da bappa kullum cikin ƙunci da kuka take, ya wahalar da ita har Allah yasa ita ma ta haifi Mahnoor.

Ita ma Mahnoor tun farkon zuwanta duniya take shan wahala har zuwan Jaish cikin rayuwarta, ta ɗan samo sassauci kuma ace zata sake komawa cikin wahala? Abin da taɓa zuciya matuƙa.

Sosai hawaye ya wanke fuskar Inna. Tsabar bakinciki da karayar zuciya har ta kusa furta saɓon Allah, saura kaɗan ta ce Allah baya sansu ne yake ta haɗasu da bala'i.

Sai ta yi saurin kame bakinta tana furta istigifari. Allah sarki Allah baya jarabtar wanda baya so, dik wanda ya tsinci kansa cikin jarabawa ya É—aga hannu ya godewa Allah ya kuma roki Allah da ya bashi ikon cin jarabawar, shi ne kawai ya dace da mumini, idan kaga baka shiga kalubalen rayuwa ma to wlh ka binciki imaninka da saura!.

Ganin Inna ta shige ciki yasa bappa ya kama hannun Æ´aÆ´an nasa suka nufi hanyar gida yana jin raÉ—aÉ—i a ransa.

A hanya suka ci karo da Mairo zata shiga gidansu da yake kusa da gidansu ArÉ—on ne.

Har kasa ta tsugunna ta É—aga mashi gaisuwa. Cikin ba daÉ—i ya amsa. Sarai ta kula da babu farinciki a tattare da shi ko miskala zarratin, ga kuma su Mahnoor suna kuka, dan haka sai ta ce dan Allah in ba damuwa tana san yin magana da Mahnoor and Mahreen.

Bai musa mata ba ya sake hannunsu ya ce su je wajenta. Da yake Mahnoor kam ta saba da ita kanwar mahaifiyarta ce sai bata yi gardama ba, tana zuwa ma ta rike hannunta tana cigaba da kuka.

Cikin gida Mairo ta wuce da su, shi kuma bappa ya samu waje a karkashin wata bishiyar kuka ya zauna yana jiransu.

Sun shafi good 30 mins a cikin gidan ka fin su fito, dikkaninsu sun daina kuka, fuska ba yabo ba fallasa, da alama Mairo ta iya kula da yara, tuni ta yi masu dabara sun yi shiru.

Ba karamin daɗi bappa ya ji ba, bawan Allah har da sauke nannauyar ajiyar zuciya, ya ji ya kara samun kwarin gwiwa a kan aurenta, sai ya ji ma bai ga abin ɓata lokaci ba, gobe dole ya kamo shanu ɗaya ya kawowa Arɗo a kai gidansu matsayin sadaki, tin da ta sanya mashi yar marainiyarsa farinciki ai dole ta sanyaya mashi rai.

Dole ayi wanna aure da wuri ko zai samu sassaucin raÉ—aÉ—in da yake ji.

Ita ma ta lura da tabbas ya ji daÉ—i, sosai ta ji ta yi farinciki da Allah yasa ta sanya shi jin daÉ—i, da alama ita ma tana son shi sosai.

Sallama suka yi mata ya riko hannun su Mahnoor suka wuce gida. Ya so su tsaya hira da Mairo ko shi ma zai samu sassaucin zogin da zuciyarsa take yi mashi, amma kash, saboda su Mahnoor da suke a tare da shi yasa ya ce mata sai dare yana zuwa.

Daga haka suka wuce gida.

Nenne na zaune a tsakar gida ta baje tana cin É—inya da addu'a suka iskota, ta yi zaman Æ´an bori a kasa tana wani cika tana batsewa.

Ko ci kanki bappa bai ce mata ba ya wuce zai shiga cikin É—akinsa rike da hannun Æ´aÆ´an nasa.

"Kwairaga magana nike san yi da kai!". Cike da isa da gadara ta yi maganar, yau babu bappan Mahreen da ake cewa, rashin mutuncin ta motso kwairaga kai tsaye aka kira.

Ko a gefen takalmarsa, tamkar bai san da wata halitta a wajen ba ya wuce zai shi ga ɗaki, shi fa namiji kunsan dik in da yake hakan nan dai yake hali baya canzawa, to shi ma fa bappa namiji ne, kun san idan maza zasu kara aure har wani sabon iskanci da waƙalanci ƙwaƙwalensu take karowa, su rinƙa jin kansu a saman iska, sai su ji zasu iya yin komai a kan wanna aure nasu, kamar basu taɓa yi ba, ayi ta rawar kafa ana wani kauɗi kamar angon kare, to yaseen haka suke, a jininsu abin yake.

Idan baki da wayau kika biye masu kika kulasu takaici ya sa zuciyarki ta buga, idan kuma kina da wayo kin san in Allah ya kaddara sai an yi sai ki bawa iska ajiyar É—an albarka, yana kauÉ—insa ki yi kamar baki san da halittarsa a cikin gidan ba, wlh da kansa zai damu sosai, ya yi ta jin kamar ya fasa aure, zai ji kamar ba shi ba, dik wani kauÉ—i zaki ga ta ragu.

Amma in kika nuna ɓacin rai yaseen kara wa zai yi dan ya shaƙa maki takaici. To kun dai ga bappa ya karo sabon walaƙanci, da dik iskancin da Nenne take yi mashi yana daurewa baya kin yi mata magana, amma yanzu ina ai banza yake bawa ajiyarta, bata isheshi ya ɗaura idanunsa a kanta ba, ango na Mairo bada kanka a sare ba............😅

Mu dai ba abin da zai hana mu zuwa wanna biki, ai ko dan mu je a kayar mana da shanu a yanka, mu ci nama mu kora fura da nono mu godewa Allah dole fa mu je.......... Nenne sai dai a mutu idan za'a mutu.

Ganin bai kulata ba yasa ranta ya yi matuƙar ɓaci, kamar wata aljanar ruwa ta miƙe fuuuuuuu kafafu kamar na shamuwa sai cikin ɗakin nasa.

Daidai lokacin ya ciro kayan Jaish dake maƙale a bayan kofa ya miƙawa Mahnoor yana ce mata ta ajiye wannan kaya a ɗakinta na mijinta ne.

Kamar wata walkiya sai ganin Nenne suka yi a tsakaninsu. Sai da Mahnoor ta tsorata ta miƙe zata gudu, baiwar Allah ta saba shan ukubar Nenne, to a tinanina dukanta Nenne ta zo yi shi ne zata gudu.

Wuyar rigar bappa Nemne ta riƙo, ko tsoron Allah babu bare kunya, a gaban ƴaƴansa ta fara jajjaga mashi jajjagen masifa da bala'i kwando kwando kamar wanda ake yi mata wahayinsu daga duniyar shaiɗanu.

Riko hannun Mahreen Mahnoor ta yi tare da É—an cewa. "Zo mu je gidan Inna Rabi". Mahnoor yarinya mai hankali da sanin yakamata!.

Mahreen da faÉ—a a jininta yake ga kuruciya a kai ne ta ce. "Ke ni babu in sa zanje Adda Mahnoor, ki bari in taya bappa faÉ—a mu ci uban Nenne".

Ai daga bappan har Nenne basu san lokacin da suka dawo da kallonsu a kanta ba. Mahnoor da tsabar zaro ido tamkar kwayar idanunta zasu faÉ—o kasa ne da kyar ta ce.

"Mahreen kina da hankali kuwa? Kin san me kike faÉ—a kuwa?".

"Nasani mana, baki ganin Nenne ta kama bappana da faÉ—a ne? Ni zan taya shi mu mata shegen duka, ni kaÉ—ai ma na isheta ba sai bappa yasa hannu ba".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun". Shi ne kawai abin da Mahnoor ta iya sake faÉ—a. Shi kam bappa ya rasa abin faÉ—e, wannan wace iriyar tarbiya Nenne ta bawa Æ´arta? Ko da yake maganinta kenan ai, ba ita ta lallata Mahreen É—in da faÉ—a ba, tun tana yarinya take yi mata huÉ—ubar dik wanda ya daketa ta dage ta rama, ai ga shi yanzu za'a daki bappanta zata rama mashi, harda uban wanda zata dake shi É—in za'a ci wato ArÉ—o kenan.

Sai yanzu Nenne ta gane Mahreen da take kauna take fifitawa fiye da komai ta fi kaunar ubanta a kan ita. Mata kalubale gareku, ku so Æ´aÆ´anku duniya ta kisu, kai har Allah da manzonsa ba zasu yi alfahari da su ba, idan kika daure kika kawar da kai kika danne kika basu tarbiya mai kyau kika kisu sai duniya ta sosu Allah da manzonsa su so su.

Da karfi Mahnoor ta ja hannunta tare da tsawatar mata a kan ta zo su tafi. Tana kwaɓe fuska ta bi yar uwar tata, sai mita take yi a kan ita a kyaleta su kwashi ƴan kallo da Nenne a kan bappanta. Sai kwaɓar bakinta Mahnoor take ya faman yi har suka fita.

Suna fita bappa ya dawo da kallonsa a kan Nenne da ta saki baki tana ganin ikon god, waye ya ce maki Allah wasa ne, hmmmmm kaÉ—an ma kika gani.

"Zaki iya sakeni? Dan ina da abin yi ne!". Ya faÉ—a yana kawar da kallonsa daga kanta, sam yanzu baya san tashin hankali, dan baya san abin da zai mayar da shi ruwa wajen dukan mata kamar a baya kan maman Mahnoor.

Nenne da jikinta ya yi mugun sanyi ta kasa ko motsawa ne ta tsare shi da ido ba tare da ta sake shi É—in ba.

Hannunsa yasa ya kwace wuyar rigar yasa, ba tare da ya sake furta uppan ba ya sa kai ya fice waje ya kyaleta tsaye baki buÉ—e galala.

Nima kai nasa na wuce izuwa kingdom of power na barta baki a sake galala.

=========================🔥

••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••••

Daga ita har Jawad É—in kyakkyawar shiga irin na Æ´aÆ´an manya manyan sarakuna aka yi masu.

Tsadaddun alkyabbars king da kansa ya ɓalle masu a ledarsu, dikka alkyabbar iri guda ne, babu wani bannanci.

Sai dai da amarya da angon dik basa a cikin nutsuwa da kwanciyar hankalinsu a lokacin da ake ƙoƙarin shirya su ɗin.

Ita Chuchu hankalinta gabaɗaya ya tashi tana neman ina Auta take? Dama a bisa ƙaida babbar aminiyarta ce zata tsaya a gefen hannun hagunta, while gefen damanta kuma angonta ne a wajen, shi ma ango a gefen hagunsa babban amininsa ne zai tsaya a wajen.

Sai dai daga shi har ita basu san ina aminan nasu suke ba, shi Jawad ya rasa Jaish a rayuwarsa wanda shi kaÉ—ai ne amininsa kowa yasan da haka.

Ita ma Chuchu sai neman Auta take yi shiru bata ganta ba har lokaci ya kusa. Sai gwada numberta suke yi, wayar tana shiga amma ba'a É—auka.

Hankalinta in ya kai miliyan to a tashe yake, ta shiga damuwa matuƙa, ga shi ba halin ta ce Auntynsu Jawad su dakata da yi mata kwalliya bari ta nemo Auta, ba zasu dakata ba, ga momma bata wajen bare ta nemi alfarmar momma ta dubo mata Autar, ita momma tana can tana fama da nata bakin.
Chapter 28 · 0% Book details