← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 242

Sashe 65

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

With her full confidence sweetie ta ce. "Ronnie kada ka damu, kwantar da hankalinka ka dai'na yin zufa, Big bro kana ɗagawa Ronniena hankalifa, kuma ni bana san hakan, ka dai'na kada rai'na ya ɓaci". Yadda ta yi maganar yadda kuka san uwar Ronnien ce take magana.

Ronnien da ya kusa sakin fitsari a wando saboda tsorata ne ya kara zaro idanu waje tare da juyowa gareta da kyau ya kuma saki hannunta da ya rike.

Sai dai kafin ya kai ga juyowa gareta da kyau Black Tiger ya juyo magic eyes ɗinsa a inda tamkar walkiya haka ya fisgota ta ƙariso gabansa. Cikin zafa rai a matuƙar ɓace ya sanya hannunsa ya yi mata wani irin mahaukacin damka a wuya mai razanarwa wanda sai da ta ji kamshi kamshin mutuwa.

Ta ɗauka wasa yake yi, bata san baya ɗaukar wargi ba, a tinaninta idan tana tsokanarsa ta wannan hanya zata iya samun damar shiga jikinsa har su fara aiwatar da plan ɗinsu a kansa, bata san shi ɗin tamkar dutse yake wanda huda jikinsa a shiga ba ƙaramin abu kamar yadda ta zata bane, in ta yi kokarin shiga jikinsa ya zo mata da karar kwana ma ai sai ta mutu ba damuwarsa bane.

Wani abin da baku sani bama, da farko wlh Ronnie ya so ya yi amfani da shiga addininta dan su samu Spender ne, dan ya lura tana san addininta sosai, shi ne kuma rauninta, amma da yake Allah ba'ayi mashi wayo kuma ya so shi da rahma, sai ya dasa mashi kaunar addinin a ransa na gaskiya wanda zai ma iya sadaukar da ransa a kan addinin ba tare da ya ji komai ba!!.

Da gudu cikin tashin hankali Ronnie ya nufi Black Tiger domin ya bashi hakuri ya saketa. Sai dai bai kai ga ƙarisawa wajen ba ya tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya kamar mutum mutumi.

Ita kuma ya ƙara shaketa da kyau da kyau, tin tana iya ganinsa har ta fara gani dishi dishi. Babu imani babu tausayi ya yi wurgi da ita ta tafi ta bugu da jikin swan chair dake ɗakin nasa ta faɗi kasa.

A wahalce ta saki wani irin azabbabben kuka mai tsuma zuciyar mai imani ba irin black heart ɗinsa ba, shi ko kaɗan bata bashi tausayi ba. Bai bata damar ta yi ƙoƙarin jawon numfashinta ba ya sanke amfani da magic ɗinsa ya janyota gabansa tana zube a ƙasan, shi kuma yana tsaye kamar wanda aka sassaƙa, ransa a matuƙar ɓace ne.

Ko kaɗan bai ji kamar zai tausaya mata ba, kafarsa guda ɗaya ya ɗaga ya sauke mata saman wuyarta, ya taketa ba tare da kalli in da take ba. Wani irin bargon azaba ne ta ji ya lulluɓeta, da gaske niyar kasheta ya yi, hasashen Ronnie ya saɓa hanya da ya ce mata Black Tiger ba zai iya kasheta ba, ashe dai sai in black heart ɗinsa bata motsa ba, tsab zai aikata fin kisa.

Sweetie ta shiga gonarsa dayawa, dama kuma already ransa a ɗan ɓace yake sakamakon addaba mashi da duniyar sheɗanu suka yi, suna kutsawa cikin ruhohin tsafinsa suna birkita mashi lissafi, abin yana bakanta mashi, yana ta ƙoƙarin ya rufe dik wata hanya da zasu iya riskar ruhohin tsafinsa ita kuma ta zo zata kawo mashi wargi, shi ne ya tattare haushin waje guda dikka ya sauke a kan!.

Bai ɗauke ƙafarsa daka samar wuyarta ba har sai da yaga ta daina numfasawa ta ɗauke diff rai ya yi halinsan! Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Sannan ne ya ɗauke ƙafarsa tare da yunƙurin zai yi ball da ita ta fice mashi daga ɗaki, sai kuma ya tina idan ya yi hakan gawar tata zata tarwatse mashi a cikin ɗaki ta ɓata mashi waje, dan haka sai ya yi amfani da magic ɗinsa wajen ɓatar da ita, kafin kyaftawa da bismilla babu ita babu rabarinta, ta ɓace a wajen.

Sannan ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dakatar da bugawar numfashin Ronnie, ya yi kamar ya sumar da shi, dan in ba haka ya yi ba yau zai iya kashe Ronnie dan ɓacin rai, saboda yasan ba zai bar shi ya kwana lafiya ba, a kanta zai hana kowa barci ya yi ta kuka, so gara ya yi mashi haka zuwa da safe ya tashesa, kafin nan kuma zai yi ƙoƙarin ganin ya shafe mashi tinaninta a babin rayuwarsa gabaɗaya, e lallai akwai aiki babba.

Team Ronnie ina kuke, me kuke tinanin zai faru? Za'a shafe kwakwalwar Ronnie, damuwata ɗaya shi ne ya batun musuluntar da ya yi? Kenan zai koma krista?😥💔

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wannan yafi komai ɗaga mun hankali, bana san ya koma krista wlh............😥💔

To bari dai mu leƙa Dubai kila kafin mu dawo abubuwa zasu ɗan yi sassauci.

••••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••🔥

Zaune Sharifat take a bakin bed É—in dake cikin A&E room É—insu, ta buga uban tagumi tare da zubawa Leesharh dake kwnace a saman bed É—in idanu tana kallonta, yau tsawon kwana uku kenan da Ramish yasa hannu aka saketa saboda ba wayarta bace, Bilal ne ya É—aukota ya dawo da ita, Dr Raj yana kula da ita, shi ne Dr É—inta, shi ma sai da Bilal ya sanya baki ne ya yarda yake dubata, da farko ya ce shi ba zai iya duba lafiyar wadda ba'a san asalinta ba, infact shi baya ma san ganinta, sai da Bilal ya umarcesa a kan hakan sannan ne ya yarda ba dan ya so ba!.

Tsawon wannan kwanaki ukun Leesharh bata san in da kanta yake ba, da farko ma Dr Raj ya ce ta mutu, sai daga baya suka iya jiyo sautin bugawar zuciyarta can ƙasa ƙasa kamar yana san dakatawa ya dai'na aiki.

Allah sarki ta ji horon manyan kai, sai da ta zaɓi mutuwa a kan hakan, a gaskiya Ramish mugu ne bashi da imani wlh, dama ga shi kullum yana maganar kada daddynsa ya yarda da kowa, kai gaskiya guy ɗin nan Ramish bashi da daɗi, ya azabtar da ita over.

Dikkan jikinta bandeji, an mammanneta ta ko'ina kamar wata pacin tayar mota, hannunta na dama ma ya samu karaya, wai a haka ma fa dan Bilal yana dakatar da Ramish É—in, da ya jima da kasheta.

Sai kuka shafiat take yi hawaye bibbiyu, kwanaki uku Leesharhnta taki motsawa, tin tana sa rai har ta fara karaya, jikinta dik ya mutu ta fara tinanin ko dai mutuwa da gaske Leesharh ta yi basu sani ba?.

Yanzu kun gano daga in da Omaid and Obaid suka gado mugunta da iya horor da mutane ko?

Shi kansa Abu Abdussalam sai da ya razana a lokacin da Bilal ya dawo da ita, sosai ya yi wa Ramish faɗa a kan yi wa mutum ɗan adam irin wannan horo babu daɗi, ya ce ko namiji bai yarda ya sake hora shi kamar haka ba ballanta mace wadda ita sam babu gurbin wahalarwa a jikinta, ya rinƙa sassauta zuciyarsa gudun yin danasani gaba.

A É—an fusace ya ce da Abbie. "Abbie danasani fa ka ce?!". "Kwarai danasani My son".

Kara É—aure fuska ya yi kafin ya ce. "Babu wata danasanin da zan yi a rayuwata, dan haka ni ka dai'na faÉ—a mun hakan".

Da yake Abbie yasan halin kayansa sai ya koma sigar rarrashi. "Haka ne son, bana fatar ka yi danasanin nima, amma please ka rinƙa sassautawa, kaga macece fa ita, amma haka ka horata kamar ka riki kartin maza ƴan ta'adda".

Kansa a ƙasa ya jinjina tare da cewa. "Amma menene banbancin wanda ya so tasan bomb a wannan hall ɗin da ƴan ta'adda?".

Shiru Abbie ya yi, dan babu banbanci, gara ma Æ´an ta'adda da sauki a kan wanda zai tashi bomb cikin wannan taro da sama da mutum 1000 zasu rasa rayukansu, har da makotan hall É—in dik zasu iya kamawa da wuta su haÉ—a da mutanen dake ciki.

Miƙewa tsaye ya yi ganin Abbie ya rasa bakin magana. "Good night Abbie". Ya faɗa ba tare da jiran abin da zai ce ba yasa kai ya nufi waje. Da kallo Abu Abdussalam ya bisa har ya fice, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga hannu ya furta zafafan addu'oi kamar haka.

"Ya Allah ka shirya mun my son ɗina, Allah ka sassauta mashi wannan zafin zuciya tasa, Allah ka kara kare mun shi daga dik wata sharri, daga karshe Allah ƙasa ya kara zamtowa mai son na gasken gaske wato Allah ka haɗa zuƙansu shi da Sharifat na yi masu aure".

Shi kuwa Ramish, bedroom ɗinsa ya wuce, white jallabiyar jikinsa ya cire, ya rage daga shi sai sexy short and singlet............ My people's wai meyasa Yah Ramish yake san sexy kaya kamar wani mai aure ne?...🤔

Short É—in ta kama shi sosai, dai'dai irin........ Na dai yi shiru kada ace na cika saka ido.

Toilet ya nufa dan ya yi wanka ya yi shirin yin barci. Bilal kuwa baya nan ya fita.

After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsadaya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face É—inta t............

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E..…...............17

After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsada ya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face É—inta tana tsaye a bakin kofar shigowa, ta kasa gaba ta shigo ciki ta kuma kasa yin baya ta fita waje.

Kamar bai ganta ba haka ya yi, ya cigaba da abin da yake yi har ya kammala, bakin bed ya wuce ya zauna, cike da class ya É—auko wayarsa, number da yake san kira ya shigar, babu suna number, hakan na nufin ba'ayi saving É—inta ba.
Chapter 65 · 0% Book details