← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 242

Sashe 52

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ciki ya rakasu, ya kuma gargaÉ—i Pretty a kan kada su yarda su fito waje, dan yasan halinta sarai da shegen san zama wajen ruwa, kullum sai ya gargaÉ—eta a kan fitowa waje, amma kuma kullun idan ya kawo masu ziyara a waje yake samunta, shegen san zama wajen koramu dake aman ruwa ne da ita. Kamar wata Æ´ar ruwa!.

Da kansa ya rufe masu kofar ramin nasu dan ma kada su fito, sai dai kash yana tafiya Pretty ta ce da Auta ta zo su je wajen korama su zauna hai, ita bata san zaman cikin nan, ta fi san waje. Auta kuwa ta bita suka fita, wajen wata korama mai aman ruwa suka je suka zauna suna kallan ruwa......... Pretty sai shirin Allah.

•••••••••••••••••••DUBAI••••••••••••••••••🔥

Kwance Sharifat take a saman bed É—inta, ta ci kuka har ta godewa Allah, yau tsawon kwanaki tara kenan ba tare da Leesharh ba, tana cikin damuwa da alhinin hakan sosai sun rigada sun saba.

Gobe zata koma school, dama rashin Leesharh ya ja mata zazzaɓi har na tsawon kwanakin nan bata je school ba, idan kuka ganta sai kun tausaya mata, da alama ba'a taɓa breaking heart ɗinta ba sai a wannan karon baiwar Allah.

Miƙewa ta yi zaune, tinanin guyson ne ya faɗo mata a ranta, ta tina kullum sai ya tambayeta ina Leesharh, Allah sarki yakamata ta sanar da shi kalar cin amanar da Leesharh ta yi masu. Can tinanin maganganun su Omaid a kan Leesharh ya faɗo mata ranta, kenan ya tabbata su Omaid suna da gaskiya, dama tin da suka ɗaura idanunsu a kanta suka ce she looks like a criminal, Guyson ya yi ta yi masu faɗa, ashe kuwa zancensu haka ne.

Tun da aka kama Leesharh bata yi waya da kowa ba, wayarta ma a cikin jakarta da suka je taron nan da shi ta barshi, dan haka sai ta sauko kasa daga saman gadon. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bags rack É—insu. Tana sanye da Pakistan a jikinta, ta É—aura gyalen kayan a matsayin É—an'kwali.

Wani irin jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita, da kyar ta iya kame kanta ta tsaya da kafafunta. A hankali ta zuge zip ɗin jakar ta buɗe.

A miliyan É—ari ta kai hannunta ta murza idanunta tana kara zarosu waje, sam bata san lokacin da bakinta ta furta what!! Ba, da karfi ta yi maganar. Nan take jikinta ya fara kerma, a hanzarce ta zira hannunta a cikin jakar ta fito da wayoyinsu. Wayarta ce da na Leesharh. Da karfi ta furta. "Kenan da gaske kamar yadda Yah Bilal ya ce mun Leesharh ta ce wancan wayar ba nata bane kenan hakan ce? Kenan tana da gaskiya ba wayarta bace wancan?".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah sarki su Yah Ramish sun azabtar da baiwar Allah a banza!".

Cikin É—aga murya ta yi maganar. Jikinta har tsuma ya fara yi, burinta ta ganta a gaban Ramish ta sanar da shi wancan waya da gaske ba na Leesharh bane, tabbas Leesharh ba muguwa bace, dama ta kafe a kan wayar ba tata bace, ashe tana da gaskiya.

Nan take ta ji karfi ya zo mata, dik wani kasala ya gudu. Da gudu ta juya ta nufi hanyar fita daga É—akin. A dab kofar fita suka yi karo da Ummie zata shigo ta dubata. Ai tsabar farincikin da zumuÉ—in ta isa ga Ramish bata tsaya bin ta kan Ummie ba ta yi waje a miliyan.

Bata zame ko'ina ba sai part ɗinsu Bilal, Ummie na kiranta amma ina bata saurara ba, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne ya rinƙa tsere a saman face ɗinta, ji take kamar ta ɗaura hannu bisa kai ta yi ta zunduma ihu mai sautin gaske ko zata ɗan samu sassauci.

Dr Raj kawai ta iso a cikin parlournsu, yana zaune ya tasa laptop a gaba yana bincike a kan wata cuta da ake yawan korafi a kanta a hospital É—insu, kamar sabuwar cuta ce da ta keta tsaron likitoci, so a matsayinsa na babban likita ya dukufu a kan neman maganinta babu dare babu rana.

Ko sallama babu ta afko masu cikin parlon, a yadda ta shigo da wani ne zai razana sosai, amma da yake jinin Modarawa ne shi É—in ko kaÉ—an bai razana ba, sai da ma ya É—auki 1 min kafin ya É—ago da kallonsa a kanta, izzar sarauta ta motsa.

Kallo mai wuyar fassaruwa ya wurga mata, ta wani shigo kamar wadda aka koro, ko sallama babu. Nan take ta sha jinin jikinta, dama idan ba Yah Rizwan ba babu mai sakar mata fuska a cikinsu, shiyasa sam bata wani yinsu sosai.

Bai ce mata ko uppan ba ta fara Æ´an kame kame tana É—an juye juye, still dai bai ce ko sannu ba, ya mayar da kansa a kan laptop É—insa ya cigaba da aikin dake gabansa.

Tsabar tsarguwa da tsorata bai tambayeta ba ta fara magana a rikice tana haÉ—e word....... "Yah Raj dama Yah Ramish nike nema, dama zan bashi wayar Leesharh ce wlh ba ita ta..............".

A miliyan ta haÉ—iye sauran maganganun a cikinta bata kai karshe ba saboda sauka da idanunta ya yi a kan Ramish dake tsaye bakin kofar shigowa cikin parlourn daga bedroom side É—insu.
Ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, Bluetooth mai kyau da tsada ce manne a kunnensa, da alama waya yake yi, amma saboda tsabar nitsuwa irin nasa daga sharifat har Dr Raj babu wanda ya iya jin abin da yake faɗe, ƙasa ƙasa cike da class da nitsuwa yake wayar.

Yana sanye da sexy sleeping dress a jikinsa, tamkar wani mai aure, ga idonsa kamar dai, to na dai yi shiru, amma da alamar tambaya fa a tattare da shi, sai tashin kamshi yake yi, da alama bai jima da farkawa daga barci ba, yanayin kayan barcin nasa idan ka gansa sai gabanka ya faÉ—i, shiyasa nace kamar wani mai aure, da alama wlh Yah Ramish É—an duniya ne sosai, gabaÉ—aya gaban rigar a buÉ—e take, faffaÉ—ar kirjinsa a waje, dik macen da ta gansa haka sai kirjinta ya buga, kai ko namiji ya gansa a haka sai kirjinsa ya buga bare mace, ka gansa cikin full kaya ya rufe ko'ina nasa ma sai ka ji ka faÉ—a da shi bare kuma ya buÉ—ewa mutane gaban kirjinsa dan iya hege.

Sharifat da ta zama kamar wadda aka sassaƙa a waje ya wurgawa hegun sexy eyes ɗin nan nasa yana cigaba da magana da wanda suke waya. Yadda kuka san idanunsa allura suka yi mata, wani irin zabura ta yi da ya kalleta, da karfi ta furta. "WAYYO ALLAH". Ta yi maganar tare da juya mashi baya.

Allah sarki a take ta birkice kamar wadda aka zarewa kaso hamsin cikin É—ari na hankalinta.

Dr Raj da ya ji ta furta wayyo Allah ta, sai ya É—ago da kallonsa a kanta, dai'dai lokacin ta juyawa Ramish baya hannayenta sai kerma suke yi. Ganin yadda ta juya baya da sauri yasa ya juya ya kai kallansa a kan kofar da zata sadaka da bedrooms side É—insu, dama tin da yaga ta yi irin wannan juyi ya yi tinanin Ramish ta gani, dan shi kaÉ—ai take yi wa irin wannan abin.

Ganinsa a tsaye yasa ya mayar da kallonsa a kan laptop É—insa, dan a cewarsa sun fi kusa, baya shiga shirginsu. Tana san gudu ta bar part É—in, tana kuma san yi mashi magana dan ta ceto Æ´ar uwarta Leesharh, sai dai ba zata iya juyowa ta sake kallansa a irin wannan shiga ba, yana É—aga mata hankali kuma yana rikitata, ga shi wandon sleeping dress É—in ma sai wanda ya gani, ku baku ji sunan kayan bane ma, sexy sleeping dress, ai daga nan zaku gane ba kayan arziki bane, na masu aure ne, shi kuma shirgegen gwauro da shi ya zo ya wani saka su.

(Sai su Yah Rizwan sun yi mashi fyaɗe da tsakar dare kila zai dai'na saka kayan ma'aurata 😅😅😅😅😅 na faɗa a saka mun gas🥱😅 ni bana tsoron Ramish da💪🌝)

Dr Raj ya cigaba da aikin gabansa, shi ma Ramish juyawa ya yi ya koma cikin room ɗinsa, saboda dama ya leƙo parlourn ne dan ya duba Bilal yana nan ko baya nan.

Jin alamar ya bar wajen yasa ta wani sauke nannauyar ajiyar zuciya wanda har sai da Dr Raj ya jiyota, amma ko a gefen takalmarsa ya cigaba da abin da yake yi.

A hanzarce ta juyo, kirjinta na dukan uku uku ta bi bayan Ramish da kallo, har ya kurewa ganinta, komai nasa abin burgewa ne. Wani irin ta ji a ranta, wani ɓangare na zuciyarta yana ce mata ta bi bayansa, wani kuma yana ce mata ta koma cikin ɗakinta.

Juyawa ta yi da nufin ta koma É—akinta, sai kuma ta tuna Leesharh tana cikin azaba, nan take ta ji zuciyarta ya karfafa, tausayin Æ´ar uwarta ya ratsata, da sauri ta bi bayansa tana karanta dik addu'ar da ya zo bakinta.

Tana sako kafarta cikin room ɗin nasa shi kuma yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa zai shiga wanka, ya bawa kofar shigowa baya.

Sai da ta ji gabanta ya faÉ—i time da taga faffaÉ—ar bayansa kamar madara. A bakin kofa ta tsaya kamar wadda take jira ace pet ta yanka a guje ta fita, like tana tsoron cikin É—akin dai.

Sarai ya ji motsinta, sai dai bai juyo ba, ya cigaba da abin da yake yi, tsabar tabbatar bashi da kunya wandon jikinsa yake ƙoƙari zamewa, dan shi babu ruwansa da tana tsaye, meyaka kawota ɗakinsa? Ko ɗakinta ne?.

Kamar ta dalla ihu take ji, shi ko kamar wanda bai san da halittarta a wajen ba.

Ai bata san time da ta juya a miliyan zata fita ba ganin ya zame wandan jikinsa, tana juyowa kuma suka ci karo da Bilal da yake ƙoƙarin shigowa yanzu. Da karfi sosai ta juya, hakan yasa ta bugesa da karfi, wani irin baya baya ta yi zata faɗi. Cikin sauri ya damko wuyar rigarta dan taimaka mata kada ta faɗi.
Chapter 52 · 0% Book details