← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 242

Sashe 100

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka Momma ta sanar da Mahnoor abin sa yasa Jaish ya ce bai sansu ba a yanzu, dan haka kada su ji haushinsa ko su ga laifinsa, ya so ta ne a lokacin da baya cikin hayyacinsa, daga karshe ta ɗaura da cewa. "A yanzu ma In Sha Allah zai so ki, zan tayaki yakin neman shawo kansa, kada ki sare ko ki cire rai, mu nan gidan jajirtattune, kema jajircewa zaki yi ki jure har mu yi nasara, sai abu nagaba da zan faɗa maki, in dai ba kin lura ransa a ɓace ba to in ya ce ki bar gabansa ko ki tashi a kusa da shi kada ki tafi, amma idan ransa a ɓace wannan kam ki tafi in ba haka ba ayi ɓatacciya, ki yawaita kasancewa a tare da shi, a kullum karfe 9 na dare yana shan cappuccinon, ni kuma nike haɗa mashi da kai'na, ki zo ki rinƙa ɗauka mashi kina kai mashi, kada ki yarda yana zaune a waje shi kaɗai, kada ki ji tsoronsa dan a labarinku na baya na ji kina tsoronsa, to a yanzu ki ajiye tsoron nan ki rinƙa kusantarsa sosai".

"Muhimmin abu nagaba shi ne, yanzu ki sani dik wata ɗawainiya nasa zai dawo kanki, kama daga kai mashi abinci, sanya shi ya ci, shinfiɗa gadonsa, mace mai dabara bata bari kowa ya ga makwancin mijinta, dan haka kada ki bada kofar da zai ce a dawo mashi da kuyangu masu yi mashi hidima a zuwan ke baki iya gyara mashi shinfiɗa ba, ki koyi yi mashi shinfiɗa da kyau, ki ɗara dik kuyangun da suke yi mashi hidima a baya yin komai yadda yakamata kuma yadda zai ƙayatar da shi, dik Haulat zata koyar dake kin ji ko?".

Kai ta gyaÉ—a tana amsawa da e ta ji.

Sosai ta fayyace mata dik wasu abubuwan da Jaish yake so da wanda baya so. Dik abin da take faÉ—e yana shiga kunnuwan Mahnoor yadda yakamata. Suna tsaka da hiran ne Omaid and Obaid suka shigo cikin É—akin baki É—auke da sallama.

Momma ce ta amsa masu sallamar tana jinsu da kallo.

Saman gadon Omaid ya haye yana turɓe fuska ya kwanta a can gefe. Shi kuwa Obaid sarki a rashin hakuri, wani kallo mai kama da harara ya wurgawa Mahnoor. "Momma who is she? She looks like Aunty Chuchu". Ya yi maganar yana kare mata kallo.

Baki É—auke da sallama guyson ya shigo, dikkansu suna cikin white arabs jallabiyas masu bala'in kyau, yau sun fito a larabawansu sak.
Saman gado kusa da Omaid guyson ya haye yana turo baki, cikinsa ce take ɗan yi mashi ciwo kaɗan kaɗan, da alama ciwonsa ce take san tashi. Yana kwanciya kallonsa ya sauka a kan Mahnoor da ta yi ƙasa da kanta tana ta satar kallansu Omaid, a ganinta sak suke kama da Jaish, kun san jini ba wasa ba, sun yi mata bala'in kyau, sai dai ta shiga ruɗani wajen ƙasa tantance Omaid and Obaid mutun ɗaya ne ko biyu saboda kamanninsu.

Zaro idanu guyson ya yi, da ɗan karfi ya furta. "Momma wannan ba matar Yah Jaish ɗin nan ba ce?". Ya yi maganar yana miƙewa zaune an fasa kwanciya, yaga ta goge ta yi kyau kamar ba ita ba........ Lallai guyson yana da basira sosai, bai fa wani jima da sanin Mahnoor ba, amma dik wannan gyara da ta sha ya iya ganeta.

Wani irin ɗan iskan dariyar ƙeta Obaid ya yi kafin ya ce. "Yah Jaish ɗin ne da mata? Tab hau kenan". Ya kai karshen maganar yana sake watsewa da dariya.

Shi kansa Omaid jin zancen sai da yasa ya miƙe zaune. "Da gaske Yah Jaish ya yi aure?". Ya yi tambayar yana zare idanu.

Guyson ne ya wurgawa Obaid harara kafin ya ce. "To dariyar me kake yi sarki?". Zama Obaid ya yi a saman sofa, cike da iyashege ya fara faÉ—in. "Yah Omar ba dole in yi dariya ba, wai Yah Jaish da mata? Amma wannan ta shiryawa azabansa ko? Dan dik gidan nan bayan Yah Ramish babu bakin mugu biyunsa, wlh i pity for his wife".

Omaid ne ya capki zance da cewa. "Waye ya ce maka ma akwai wadda zata iya zaman aure da shi? Mutumin da bayan bada umarnin babu wani abin da ya iya, su kuma mata suna san soyayya da kulawa haɗe da lallaɓawa kamar jarurai, shi kuma yana abu kamar bosawa bashi da wani shaukin love".

Tab wato Omaid ɗan duniya ne, ko daga ina ya san shaukin love kuma? Kana ganinsa kaman shiru shiru ashe A ne shi ma, dama fa masu shiru shirun nan hmmm idan suka yi wata tsiyar sai ƙwaƙwalwa ta kasa ɗauka.

Momma dai binsu da kallo kawai take yi abinta.

Harara Guyson ya wurgawa Omaid kafin ya ce. "Kai daga ina ka san shaukin love É—in?".

Obaid ne ya amshi zancen da cewa. "Tab ai Omaid Æ´an'matansa sun kai uku a school, har faÉ—a ake yi a kansa sosai, love yake bugawa over"........... Momma ce ta katsesu da cewa. "Kai kuma Æ´an'matanka nawa?"....... ÆŠan É—aure fuska kaÉ—an ya yi. "Momma ni ai bana soyayya, me zan yi da mata? Bani da lokacinsu gaskiya".

Girgiza kai kawai guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor. "Kada ki biyewa waÉ—an nan, kin yi kyau sosai, ina sisterki da ta yi mun kallan matsayin Yah Jaish É—in nan take?".

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da Mahreen tana ɗakin da aka yi masu gyaran jiki....... "Kada ki takura kanki wajen sunkuyar da kanki da sunan kina jin kunyarnmu, mu kannen Yah Jaish ne, kinga mu kannenki ne, ki ɗaukemu a haka kin ji?". Cewar guyson again, yaro mai sanyin hali.

"Waye kaninta?". Cewar Obaid, a kule ya yi maganar. Hararar wasa guyson ya wurga mashi kafin ya ce. "Mu mana, mune kannenta". Kallon uku saura kwata ya bita da shi kafin ya amsa da. "A'a sai dai ku, amma ni wannan ƴar karamar yarinyar ba zan ce mata aunty ba, na fita shekaru fa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa fuuuu ya nufi waje.

Da kallo dikkansu suka bisa har Mahnoor ɗin ma, shi a dole ransa ya ɓaci ance shi kanin Mahnoor ba zai ɗauki hakan ba.

Dab zai fita Jaish yana sako kai zai shigo. Karo suka É—an yi, da sauri ya ja baya a ransa yana cewa shikenan yau ranata ba zata yi kyau ba tun da na haÉ—u da Yah Jaish. A fili kuma sai cewa ya yi. "Good afternoon Yah Jaish".

Kallon tsab Jaish ya yi mashi kafin ya amsa da. "Afternoon, from where to where?". Fuska a É—aure tamau ya yi maganar. Guyson ne ya fara yi mashi dariya, suna bashi dariya yadda suke nitsuwa a gaban Jaish, zaka rantse da Allah malaman da'awa ne idan ka gansu a gaban Jaish ko Ramish, a bayansu kuwa ko shaiÉ—an sai ya sara masu a rashin mutunci.

Matsawa kusa da Mahnoor guyson ya yi, yana dariya ƙasa ƙasa ya ce. "Kinga dik iskancin nan nasu mijinki maganinsu yake yi, tsoronsa suke ji kamar su mutu, baki ga sun nitsu ba?".

Ita kanta sai da abin ya so sakata dariya, yadda Obaid ya rinƙa tada jijiyoyin wuya yanzu a nan, amma daga ganin Jaish kamar wani kurman da ya wuni bai ci abinci ba ya zama, ya nitsu tsit.

Cikin in ina Obaid ya amsa da. Daga wajen momma É—aki kuma zai tafi ya kwanta. "Ka aikata wani abin ko?". Jaish ya faÉ—a yana wurgawa momma dake kallonsa ido. Wato Jaish yasan halinsu sarai, basa zama basu yi wani laifin ba, shiyasa dik in ya haÉ—u da su sai ya ce sun aikata wani abin.

Wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji na jin sanyayyar muryar mijin nata, wani irin azabbabben sonsa ne yake kara taso mata, ji ta yi tana san ɗago kai ta kallesa amma tana tsoron su haɗa ido, kuma tana kunyar momma ta kamata tana kallansa, sai kawai ta danne ta ƙara yin ƙasa da kai, amma tabbas tana kewansa, yanzu an kusa sati biyar rabonta da su kasance a hare kenan.

Sarai momma ta fahimci har yanzu Mahnoor tana tsoron Jaish sosai, kamar ma yanzu tsoron nasa karuwa ya yi a ranta, lallai sai ta tsaya tsayin daka ta cire mata wannan tsoro idan suna san yin nasara.

Wani irin kallo Jaish ya wurgawa Obaid har sai da ya haÉ—iyi wani yawu mai wuyar wucewa, sannan tin kafin Jaish É—in ya sake yin magana ya yi saurin faÉ—a mashi dik abin da ya aikata, wato guyson ya ce Mahnoor Auntynsu ce shi kuma ya ce ba Auntynsu bace dan ya fita shekaru, dan haka ba zai ce mata Aunty ba, tsab ya faÉ—i abin da ya yi.

Momma da guyson sai murmushi suke binsu da shi. Jin abinda Obaid ya faÉ—a yasa ya ja siririn tsaki tare da karisowa ciki, dan a cewarsa shi ma ai bashi da haÉ—i da Mahnoor É—in bare ya ji babu daÉ—i dan sun ki accepting É—inta sun yi mata rashin kunya.

Saman sofa Jaish ya zauna, shi kuma Obaid ya yi saurin ficewa waje. Cikin girmamawa Omaid ya É—agawa Jaish gaisuwa, amsa É—aya ya yi hankalinsa gabaÉ—aya a kan momma.

Ƙasa Omaid ya yi, da sauri ya bi bayan Obaid, dan basa zama inuwa guda da Jaish. Guyson kuma cigaba da hira da Mahnoor ya yi ba tare da damuwa ba, dama abin da yasa a kauye ya ji kyamarsu ma, saboda datti ne, yanzu kuma sun yi tsab dan haka bashi da wata matsala da su.

Tin Mahnoor tana noƙewa bata yi mashi magana har ta fara sakin jiki suna hira ƙasa ƙasa, har murmushi ya sakata yi, ko ɗaya kuma bai ambaci sunanta ba, Aunty yake ce mata cikin girmamawa, ita ma ta tambayesa sunansa, ya ce mata Omar amma ana kiransa da Guyson, dan haka sai ta fara ce mashi Yah Omar saboda ya fita shekaru, yanzu kusan 19 years yake da shi.
Chapter 100 · 0% Book details