← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 242

Sashe 192

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhm uhm ba na ce kai ma ka mun kaki ba, naku sa yin fushi da kai, haka jiya na ce ka mun murmushi ka ce baka iya ba ko?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Komawa ya yi ya kwanta, salanta yasa ya manta da yana san bin bayan Abbonsa, ɗan mirginawa ya yi ya kwanta ruf da ciki, cike da tsantsar madarar kaunarta ya ce. "Ban iya bane ne, amma kema kin san da na iya dole zan yi maki, but ki koya mun yadda ake yi zan yi maki". In a low voice sosai ya yi maganar, kamar wani yana yi mashi laɓe..... "My Hero ni nasan ba zaka taɓa iya yi ba, ɗan garama shagwaɓar kila zaka iya kwatantawa"......... Murya kamar yana cikin mayen madarar kauna ya ce. "To mu yi video call sai ki koya mun shagwaɓar, zan yi maki, kece fa, ai dolena in yi". Bin kayan jikinta da kallo ta ɗan yi kafin ta ɗan turo baki kaɗan. "My Hero ka bari zuwa dare ko anjuma sai mu yi video call ɗin, yanzu babu k........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi, saboda ta ji nauyin ce mashi babu kayan arziki a jikinta, kuma tasan idan ta faɗi hakan ma kishinsa ne zai motsa ya yi fushi, dan shekaran jiya da suna waya ya jita tana magana da Robbot mai kawo abinci a take a wajen ya ce mata wanene, da buɗar bakinta sai ta ce mai girki ne, aikuwa taga kishi, dan cikin ɓacin rai har mantawa ya yi ya daka mata tsawar a kan me zata yi magana da mai girki namiji? And babu masu girki mata ne sai maza? Take ya hau ya fara masifar da bai san ya iya ba, ya kuma ya manta cewa princess ɗinsa ce, kishi ta rufe mashi idanu. Da kyar ta shawo kansa, da kyar ta samu ya ɗan sassauto har ta sanar da shi Robbot ne ba mutum ba, dik da haka ya ce baya san ta rinƙa magana da shi, ai namiji ne koma Robbot ɗin ne, dole ta yi alkawarin ba zata sake ba, ta kuma bishi da love word masu zafi, a takaice dai a wannan lokaci bai iya yin soyayyar ba, dik da kalaman da ta zuba mashi, ransa ya rigada ya ɓaci sai kawai ya ce mata sai anjuma, ya katse kira ya zauna yana huci shi kaɗa.

Wannan dalilin yasa bata ce mashi babu kayan arziki a jikinta ba, dan kishin zata motsa, zai ce akwai maza a gidan, tasan rigimarsa bata karewa a kan kishi, har yau idan ya kirata sai ya ce ina wannan Robbot É—in, kuma yana tambaye fa kawai dan ya ji shin tana kusa da shi ne ko dai ta yi nesa da shi kamar yadda ya ce mata, kai Hoorain ba dai kishi ba, ko da yake jinin Modarawa haka suke dikkansu! Balai'n kishin tsiya daga mazan har matan!.

Kamar zai tambayeta meyasa bata san su yi video call a yanzu, sai kuma ya basar da cewa. "To shikenan Allah ya kaimu, ki gaida mun da Pretty and Yah Omerish". Da okey ta amsa mashi kafin ta ce. "To ka bani na barci". Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke har sai da ta jiyo shi kafin ya manna wayar da É—an bakinsa ya bata sumbata. ÆŠan lumshe idanunta ta yi tamkar da gaske ya yi wa kumatunta, a hankali ita ma ta bawa wayarta sumbatar, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har a ransa ya ji kamar da gaske ta yi mashi, ya ji daÉ—i sosai. Da kyar ya iya katse kiran, ya jima a kwance kafin ya tashi da kyar ya bi bayan Abbonsa.

A ɓangaren King kuwa, shirye shirye suka fara yi babu kama hannun yaro, suna gama zama yasa Momma ta kira Smart ta bashi umarnin a kan ya dawo da Auta, nan da gobe su dira a kingdom of power, sai dai King ya ce kada su kuskura su sanar da Smart ɗin auren Auta za'ayi, a ɓoye mashi sai ranar ɗaurin aure ya ji a masallaci, ita ma Auta a ɓoye mata sai an ɗaura auren sannan a bayyana mata, a dawo da ita ta shiga dilka da halawa game da kunshi da sauran gyare-gyare.... Kam bala'i, lallai King ya shirya da zafansa, wato sai an ɗaura aure zasu sani, tab akwai cakwakiya.

Momma ta ji zafin hakan, amma yazamar mata dole ta bi umarnin King, dole su hakura.

-------------------------------------------------🔥

Rasa mafita yasa shi nufar kofar da nufin ya buɗe kawai. Sai addu'a yake yi Allah yasa ba shigowa ciki Omaid zai yi ba, ga shi ya cire kayan jikinsa, ga mace kwance a saman bed ɗinsa, me za'a zarga kenan? Ya gefawa kansa tambayar. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yasa hannu ya buɗe door ɗin. Suna haɗa ido Omaid ya ce. "Yah Omar barci zaka yi ne?". Ai bai san time da ya gyaɗa mashi kai ba, alamar e barci zai yi. "Dama na zo mu yi hira ne fa, yau na ɓata da Obaid, amma tin da barci kake ji no need, bari in je wajen Momma kawai". Kara langwaɓar da kai guyson ya yi, ya ƙara shagwaɓe fuska alamar da gaske barcin yake ji. A hankali ya jinjina kai yana ƙaƙalo hammar dole. Juyawa Omaid ya yi yana yiashi good night. Ai yana barin wajen ya mai da kofa ya garƙame tare da juyawa da gudu ya koma cikin ɗakin, saman gadan ya haye ya zauna tare da buga uban tagumi tana tinanin meyakamata ya yi ne?. Nan fa ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsar ya bari sai dare ya yi sosai, kowa ya yi barci sai ya mayar da ita bedroom ɗinta. Na'am ya yi da wannan shawara, sannan ya fara binta da kallo, gabaɗaya ta tafi da tinaninsa, bare ma ɗan bakin tsiwar nan tata, ga shi ɗan ƙaramin amma sai iya fito da magana. Hannu ya kai saman ɗan bakin nata ya ɗan ja da ɗan karfi kafin ya ce. "Masifaffa kawai!". Ya yi maganar idanunsa a kan yatsun hannunta dake zara zara ƴan sirara. Haka ya yi ta bi yana karewa surar jikinta kallo har dare ta tsala, sannan ya miƙe ya zura jallabi a jikinsa. Ya nufo waje, sai da ya gama leƙe leƙensa ya tabbatar babu kowa, sannan ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita bedroom ɗinta. Wani irin ajiyar zuciya ya rinƙa saukewa time da ya dawo bedroom ɗinsa, saman bed ya haye da nufin ya yi barci, yau ko sleeping dress ba za'a saka ba, sai dai kuma barcin sam sam taki zuwa, tinaninta ne kawai fal a cikin ransa har kusan asuba, yarasa dalilin dayasa yake tinaninta sosai haka. Daga karshe dai ya miƙe ya ɗauro alwala tare da hayewa saman dadduma ya fara nafilfili tin da kyan Mahreen ya azalzali zuciyarsa ya hanasa rintsawa.

-----------------------------------------------🔥🔥🔥

Ko daga ina ya koyi yiwa mata wanka? To dai yau ya yi wa Mahnoor wanka, kuma da kansa ya bata kayan da yake so ta saka, sannan ya rungumeta suka kwanta a tare. Zuciyarsa fara tas yau, ya yi barci mai shegen daÉ—i, ita ma ta yi barci mai shegen daÉ—i, yau gata ga Hammanta. Washegari da safe, bayan sun yi sallar asuba dama sun koma barci, karfe 7 ta farka, cikin sanÉ—o ta kwaci kanta daga garesa, a hankali ta sauko kasan bed É—in, kai tsaye ta nufi waje, bedroom É—inta ta koma, alkyabbarta ta É—auko ta É—aura a saman kayan jikinta, cikin sauri ta fita ta nufi bedroom na momma, wai dan ma kada momma ta gane a tare da mijinta ta kwana, irin ta nuna a part É—in momma ta kwana, dan sun yi da momma É—in a kan ba zata koma wajen Jaish ba sai ya zo ya bada hakuri, shi ne wai zata yi wayau.

Zaune ta isko momma a saman King sofas set masu bala'in kyau na cikin bedroom É—inta, hannunta rike cup na cappuccinon tana sha. Binta da kallo ta yi, sosai Mahnoor ta shiga shakku da kame kame ganin irin kallon da momma take binta da shi. Daurewa ta yi ta kariso gabanta ta tsugunna dan ta kwashi gaisuwa. Still binta da kallon mamaki Momma take ta yi. "Ina kwana Momma?".

Shiru momma bata amsa gaisuwar ba, wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji, addu'a ta shiga yi Allah yasa ba fushi Momma take yi da ita ba. A dai'dai wannan lokacin Omaid ya shigo, a kusa da Momma ya ƙariso ya zauna. Yana sauke kallansa a kan Mahnoor ɗin ya ce. "Momma wannan mahaukaciyar fa?". Shiru dai Momma bata tankasu ba, kallanta a kan Mahnoor babu ko kyaftawa, kuma ba kallan tuhuma take binta da shi ba face kallan mamaki, abin abin dubawa ne!.

Zama Mahnoor ta yi a kan kafafunta, ta rasa abin yi, sai kawai ta yi ƙasa da kai tana jiran hukuncin da za'a yanke mata....... Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo, yana sanye da white arabs jallabiya, a kusa da momma shi ma ya je ya zauna, ya wani ɗaure fuska kamar ba Jaish da ya gama holewarsa daren jiya ba, har mamakinsa Mahnoor ta yi, ya wani basar kamar bai ganta a wajen ba, cikin ladabi da biyayya ya ɗagawa Momma gaisuwa.

Nisawa ta yi tare da maido da kallanta a kansa, a hanzarce ya yi ƙasa da kai yana ɗan shafa kansa. Amsa mashi gaisuwar Momma ta yi tana kare mashi kallo tamkar mai san gane wani abin. "Momma dama zan je office ne na ce bari mu gaisa first". Ya faɗa yana satar kallan Mahnoor dake kallan ƙasa. Tini Omaid ya natsu tsit kamar babu shi a wajen, da zai yi wa Mahnoor walaƙanci, da ganin Jaish yasa ya janye kalamansa ya bita da ido kawai........ "To shikenan, idan ka je office ɗin ka gyara shirin dake office ɗin naka, dan jeren da ka yi a wajen bai yi ba sam sam". Cewar Momma. A hanzarce ya ɗago ya kalleta jin abin da ta faɗa. Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta yi mashi alama da Mahnoor da ido. Da sauri ya yi ƙasa da kai, kunyar rashin kunyar tasa ta motsa!..
Chapter 192 · 0% Book details