← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 220 OF 242

Sashe 220

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Smart kan Auta ya nufa, Abdussalam yana rike da ita yana ta famar girgizata yana kwallah, ya tattala mata ruwa a kanta ya kai 5 bottle, hakan yasa suka yarda da ta mutu É—in ne, ruwa ba zai tasheta ba sai dai ALLAHN da ya yi ruwan ne zai iya tashinta.

Wani irin gigitaccen tsawa da Smart ya dakawa Abdussalam har sai da yasa gabaɗaya waɗan da suke cikin parlourn suka natsu, a zabure Abdussalam ya ja baya da gudu. Bai bi ta kan kowa ba ya ɗauki gawarta ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya nufi kofar fita, dik an rasa mai bakin iya ce mashi uppan. Har ya kai bakin kofa ya juyo ya kalli King ido cikin ido. "Ka jira dawowata, sai ka ɗanɗani irin azabar da ka ɗanɗanawa Zunaira a zuciyarta kafin mutuwarta, kuma sai ka faɗa mun dikkan amsoshina!!!". Yana kai karshen maganar ya ja hannun guyson da yake tsaye a bakin kofar tamkar an sassakasa, kamar wanda aka zarewa laka, tin da ya yi ihu sau ɗaya bai sake ko motsawa ba, amma ransa na jikinsa kuma ba suma ya yi ba.

Shi kuwa King Allah ne kaÉ—ai yasan irin halin da ya shiga, ji ya yi tamkar bashi a duniya, Zunaira ta mutu? Ina kin yarda ya yi kamar yadda har yau commander Zafar yaki yarda da Hoorain ya mutu, an je an binne Hoorain, har kabarinsa su Ansar su je da shi, amma yaki yarda É—ansa ne, dan shi yana ganin Hoorain a gizo. To haka shi ma King a yanzu yaki yarda Zunaira ta mutu, ya shiga wani irin hali na tsakanin rayuwa ko mutuwa, wato shi ma a yanzu yana É—anÉ—ana abin da commander yake É—anÉ—ana, sai dai kuma dik da ta mutu wlh bai yi danasanin hanata auren Hoorain ba! Ko kaÉ—an bai ji mamar bai kyauta ba da ya hanata Hoorain tashin sense!!.

-------------------------------------🔥

Suna fitowa suka ci karo da Jaish and Omaid da Obaid suna biye da shi a baya. Cike da tashin hankali Jaish ya tambayi Smart me yake faruwa?. Ko dakatawa Smart bai yi ba bare yasa ran zai samu amsa daga garesa, kai tsaye ya nufi wajen motocin gida. Bayansa suka bi gabaɗayansu Jaish yana faɗin ina zai je da ita? Bai amsa mashi ba sai ya ce ya yi maza ya bashi keyn motarsa bari ya wuce da ita, dan ba za'ayi jana'izarta a nan ba, ran Smart ya ɓaci over.

Jaish bai yi musu ba ya ɗauki mashi keyn motarsa, sai dai a tare suka nufi airport, da jet ɗin Smart ɗin zasu yi amfani. In short kai tsaye ya ɗauki gawar Auta zuwa Dubai, rabonsa da Dubai tin wani zuwa da ya taɓa yi bincike a kan Ramish, tin lokacin bai sake zuwa ba, yanzu tsawon shekaru wajen 10, amma yau saboda mutuwar Auta ya wuce da gawarta can. Bai sanar da momma zai zo Dubai ba, babu wanda ya sani sai Jaish and guyson da suka tafi a tare, Omaid and Obaid ma sun barosu a kingdom ɗin sai kuka suke yi, ya ɗauki guyson ne ma dan yasan sai ya yi jinya, kada ya tafi ya barshi matsala ta afku da shi.

Tin kan su hau jirgi ya kira Ramish a waya, ya sanar da shi ya zo airport ya ɗaukesu, ya ɗan yi mamakin jin sun zo Dubai, amma sai ya shirya tsab cikin suit masu bala'in tsada, ya ce da Leesharh bari ya je airport yana zuwa. Da yake ita tasan me a gidan, tasan tana tare da bakar azzaluma yarinya mai ɓadda kama a matsayin tsohuwa, sai ta shiga tashin hankali da damuwa over, a tsorace take ya tafi ya barta da wannan tsohuwa.

Hannayenta ya riko cikin nasa yana kallan face ɗinta. "Aesh ba zan jima ba, babban yayanmu ne ya zo, shi kawai zan je in ɗauko kin ji?". Shiru ta yi kanta a ƙasa, kamar mai tinanin wani abin, tana zaune a saman bedside drawer ɗinsa, shi kuma yana zaune gefen bed ɗin suna fuskantar juna.

Kafin ya ankara sai ganin hawaye ya yi yana ɗiga a ƙasa, ashe kuka take yi da ta sunkuyar da kanta ƙasa.......... "Aesh lafiya kuwa? Meyasa kike kuka?"........ Shiru bata amsa shi ba, ita tasan bala'in da zata shiga idan ya tafi, tsoron matar take ji......... "To zaki bini mu je tare ne?". Ya jefa mata tambayar yana sakin hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta. A gaggauce ta gyaɗa mashi kai alamar e zata bishi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To shi ne sai kin yi kuka? Ai da sai ki faɗa mun kina tsoron gidan ne mu tafi tare". "Kina tsoron mutanen da suka zo ɗin nan ko? Ba zasu sake dawowa ba In Sha Allah, so feel free and enjoy your life with your husband to be In Sha Allah". Ya kai karshen maganar yana ɗan leƙa face ɗinta.

Wani irin shessheƙa ta yi kafin ta kai hannu tana goge hawaye, ta kasa yin magana. Ƙasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "Yau ɗaya naga abin da kike tsoro Aesh, dik yadda aka yi akwai abin da yake baki tsoro kuma yake ɗaga hankalinki a gidan nan! To faɗa mun menene sai in kawar maki da shi kada ki rinƙa jin tsoro". ....... KAI WATO RAMISH MA FA AKWAI ƘWAƘWALWA, A RANSA YA JI AKWAI ABIN DA YAKE BATA TSORO NA DABAN, BA WAI DAN MUTANEN CAN SUN KAWO MASU HARI BANE, AKWAI WANI ABIN DAI!!.

Da yake ita ma tana da basira sai rashin yin tinani kafin ta yi abu, sai ta ce mashi. "Yah Ramish tin da ka iya gano cewa akwai abin da yake bani tsoro, to ka gano ko menene da kanka ba sai na faɗa ba". "Haka kika ce?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e haka ta ce. Ɗaura yatsarsa a saman kumatunta ya yi. "Zaki gani, cikin ƙankanin lokaci zan gano". Ya faɗa yana ɗan ja baya kaɗan daga kusa da ita. Tab kunga Leesharh ta yi amfani da basira a nan ko? Tasa zai fara binciken me abin tsoratarwa a gidan, idan Allah ya taimakesa sai ya kama tsohuwar nan da hujja dumu dumu, kamar Leesharh tana highlighting ɗinsa a kan abin ne.

"Shirya ki zo mu je, saura bai wuce 20 mins jirginsa ya sauƙa ba". Ya faɗa yana kallanta. Miƙewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi magana ba. Da kallo ya bi bayanta, idanunsa a kan mazaunanta dake motsawa a hankali, nisawa ya yi tare da haɗiyar siririn yawu kamar wadda aka ajiyewa kayan fresh marmari a gabansa!.

Tana fita suka yi karo da tsohuwar nan, gabaɗaya tray ɗin hannunta ya faɗi kasa abincin da ta shiryawa Ramish ɗin ya zube ƙasa. A razane Leesharh ta ɗago ta kalli face ɗin matar kafin ta mayar da kallonta a kan kayan abincin da suka watse a wajen. Idan ran tsohuwar nan ya kai dubu to ya ɓaci, sannan hankalinta ya tashi sosai, Leesharh ta lura da hakan, sai ta ce. "Mama kada ki damu ba sai kin ɓata rai ba, Yah Ramish ba zai ci abinci a gida ba yau, zamu ci a waje, ki gyare wajen kawai ki je ki huta abinki". Ta kai karshen maganar tare da wucewa zata bar wajen.

Ai tsabar ɓacin rai tsohuwar nan bata san lokacin da ta kai hannu ta damko wuyar rigar Leesharh ta baya ba, tana zazzare ido ta kasa yin magana. Ko kun san meyasa bata yin magana? Saboda muryan yara ne da ita, za'a iya gane ba tsohuwa bace, shiyasa ta yi acting matsayin kurma, yanzu kunga ne dalilin da yasa na ce maku tun da take kula da Leesharh bata taɓa yin magana ba?.

Da mamaki Leesharh ta juyo da kallonta a kan matar. A miliyan ta saketa tare da girgirza kai alamar tana bawa Leesharh hakuri kenan, mamaki kamar zai kashe Leesharh, me dan an ɓarar da abinci zata tashi hankalinta? Sai kace babu wani abinci a gidan? Abin da mamaki!. Alama tsohuwar ta nuna mata a kan zata iya haɗa masu wani abincin yanzu ba sai sun ci a waje ba!.

Shiru Leesharh ta yi tana san gane nufin tsohuwar nan a kansu, meyasa ta damu da abinci yau bayan a da ko ta kawo masu basu ci ba bata damuwa, wata rana ma a waje suke fita su ci, bata damuwa sai yau? To why? Leesharh ta jefawa kanta tambayar, lokacin guda ta ɗan ɗauke wuta. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta saki wani ƙayataccen murmushi, kai ta jinjinawa tsohuwar a kan ba damuwa ta shirya masu wani abinci, a cikin ranta ta ce. "Zaki san da jinin Nigeria kike yi, yo mu da dik duniya ta jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwa mu bare ke da iskancin naku ma bai da lasisi, mu kuma Najeriya dik iskanci masu iskanci sai ya jira, sai da suka sara mana, ni kaɗai na isheki ba sai Yah Ramish ya sa baki ba, zaki gane ke karamar ƴar iska ce, ba zan taɓa bari ki san nasan komai a kanki ba! Cikin ruwan sanyi zamu yi amfani dake mu kama iyayen gidanki, ai ke yanzu kina da amfani a wajenmu, zan taya shi bincike wajen yin amfani dake". JAMA'A KU TAFAWA NIGERIA!! KU TAFAWA LEESHARH!! HABA AI JININ NIGERIA BADAGA NAN BA, KOWA SAI YA JIRA ALLAH KUWA!!.

Wucewa ta yi tana tinanin in dai tana san yin magananinsu to dole ta kasance tana da kusanci da Ramish sosai, ta hakance zata sanyasu su da kansu su kama kansu. Da wannan tinani a ranta ta yi wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen arabs abaya, ta ji yayansa zai je ɗaukowa, sai ta shirya da kyau dan kun san siririki ne Smart........... 😅
Chapter 220 · 0% Book details