← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 242

Sashe 69

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai'dai lokacin da suke zuba wannan soyayya tasu shi kuma uncle Jahiz yana hospital wajensu Khadija, asuban farko ya tafi wajensu. Zee ta farfaɗo sai dai ta ki yin magana a gabansa, mamakinsa ne kuma ya hanata yin magana, saboda shi ne best player ɗinta a ƴan kwallan kafa, bata taɓa tsammanin zata gansa a zahiri ba, sai ma take ganin abin kamar mafarki kamar kuma zafin ciwo yasa yake yi mata gizo tin da shi ne a ranta.

Sai dai kuma fa, ganinsa ya tayar mata da hankali a in da ya dawo mata da mutuwar babanta sabo, ta tina yadda suke kallansa ita da babanta a tv a tare. Yau kwananta uku da farfaÉ—owa, sai dai a kullum ya zo wajenta kuka kawai take yi idan ta gansa, taki yarda ta bashi dama ya yi magana da ita.

Idan kuma ya bar hospital ɗin sai ta yi shiru har tana tambayar nurses ina ƴar uwarta da ɗanta? Kullun amsa ɗaya suke bata shi ne ɗanta yana cikin family part, ita kuma Khadija tana ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu.

Kullum Zee bata gajiya da tambaya, jikinta yana ta kara warwarewa tana samun lafiya yadda yakamata, dan kwararrun likitoci ne suke kula da ita.

•••••••••••••••• FOREST•••••••••••••••••🔥

Shiru ta tsaya tana kallansa bata motsa ba, yana isa gabanta ya jefar da takobin hannunsa a ƙasa ya ɗagata sama ya matsar da ita daga wajen, yana matsar da ita kifiyar da aka saitata aka harbeta da shi ya wucesu sai cikin ruwan koramar.

Sauketa ƙasa ya yi tare da juyawa ga in da aka yi harbin kifiyar, sai dai kash bai ga ko alamar mutum ba, wanda ya yi harbin ya gudu ya bar waje. Amma wa kuke tinanin ya yi wannan harbin?.

Dawo da kallonsa a kanta ya yi. Har lokacin bata motsa ba, idanunta a kansa babu ko kyaftawa. ÆŠan lumshe idanunsa kaÉ—an ya yi. "Ki yi hakuri ranki ya daÉ—e". Har yanzu fa bai iya tina face É—insa ba'a rufe take ba.

Ganin bata motsa ba yasa ya kai hannunsa saman shoulders ɗinta ya ɗan girgiza a hankali yana ambatar sunanta. Wani irin dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali. A fili ta furta. "Hoorain ban taɓa ganin kyakkyawa irinka ba, anya baka fi kowa kyau a duniya ba kuwa?".

Ai a miliyan ya kai hannu saman face ɗinsa, jin bai rufe face ɗin nasa ba yasa ya ɗan yi ƙasa da kai yana ɗan ciza laɓɓansa alamar bai so haka ba.

My people's dik yadda zan zayyana maku haÉ—uwar Hoorain ba zaku fahimta ba, kamar shi ya yi kansa, kyakkyawan gaske.

Ga tsawo da cikar halitta, yana da kafaɗa mai faɗi, ƙirji mai tsari, ya sa ya zama kamar wanda aka zana. Fatar face ɗinsa fara ce kamar madara, hakan tana bayyana yadda yake mai tsafta da kamshi. yana da laushi da kyan gani, kamar ba mayaki ba, sai sheki skin ɗinsa yake yi, alamar yana kula da kansa sosai. Fuskarsa tana da siffar mai ladabi, very innocent haka, da ganin yana yin face ɗin zaka fahimci ba zai yi yawan magana ba, hancinsa mai tsari kuma dogo mai ban sha'awa, leɓɓansa na sama yana da ɗan kauri kaɗan, na ƙasa kuma ɗan laɓalaɓa haka, irin laɓɓan yana da masifar kyau. Idanunsa suna da siffa mai ɗaukar hankali, suna kama da almond, tare da fari mai tsabta da ban sha'awa
Gashin kansa baƙinkirin ko, yana taɓo idanunsa kaɗan ta gaban goshinsa, amma yana da tsawo ta bayansa, yana wani irin sheki yana curlyn kamar na baby's, kamar yadda ake gani a yanayin fashion na zamani.

Yana da kwantaccen saje bakin kirin ɗan madaidaici a gefe da gefen face ɗinsa. Yanayin nutsuwa mai ɗaukar hankali, akwai cikakkiyar kamala a face ɗinsa, amma yana cike da kwarjini da karsashi, tafasasshen jini na zakunan mayaƙa, ga ƙarfin zuciya. Wannan da baya sanya hukar yaki idan yana cikin jama'a, ba ya buƙatar yin ƙoƙari dan ya jawo hankalin mutane a kansa, kwarjininsa na halittarsa zata ja mutane kusa da shi. Hoorain ya haɗu matuka gaya.

Ganin ya yi ƙasa da kansa bai furta komai bane yasa cikin hanzari ta kai hannayenta dikka biyu a saman lallausan kumatunsa, cike da tsantsar kaunarsa ta fara faɗin. "Hoorain ka yi magana mana".

Auta ta so shi bata san kamanninsa bama bare ace yanzu ta gansa a yadda bata zata ba, dan ya wuci kyan da ranta yake ayyana mata, ai wani sabon kaunarsa ne ya kara narkuwa a cikin zuciyarta.

Ba kamaramin sabon bakon alamari ya ji ba a lokacin da ya ji saukar hannayenta a saman kumatunsa, ƙasa iya ɗago kansa ya yi bare ya kalleta, ya rasa ma a wani matsayi zai ajiye kansa.

"Hoorain dan Allah ka yi mun magana ka ji? Ka yi magana ko zuciyata zata yi sanyi". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

Shiru babu alamar zai É—ago kansa ma bare ya yi mata magana. Matsawa dab da shi ta yi. "Ka ji babu daÉ—i ne dan na kalli face É—inka?".

Nan ma bai amsata ba.
"Ka yi hakuri ban zata dan na kalli face ɗinka zaka ɓata rai har kaki yi mun magana ba". Ta kai karshen maganar tare da zare hannayenta daga kumatun nasa, ranta ya ɗan sosu, da sauri ta juya zata bar wajen saboda wani irin kuka da ya zo mata mai wuyar dakatarwa, tana san shi amma yana walaƙantata har haka, ta yi magana yaki amsa mata, idan da yasan yadda wannan abin yake ƙona mata rai da ko kusa ko alama ba zai yi mata ba.

Tana juyawa sai ji ta yi ya capki hannunta, cak ta tsaya tare da ƙoƙarin jiyowa garesa, da karfi ya fisgo ta faɗa saman warriors chest ɗinsa, saboda wani irin wutar santa dake azalzalar zuciyarsa, yau ya kai makurar da ba zai iya dannewa ba, zuciyarsa ta yi cikar da in bai bari ta yi amai ta amayar da abin dake cikinta ba zata iya fashewa, yau dai babu wani dama da zuciyarsa zata iya sake bashi, ji yake tamkar ya mayar da ita cikin ransa ko zai huta da abin da yake ji a ransa.

Bata ankara ba ta jita saman faffaɗar kirjinsa, da sauri ta waro idanunta waje, abin da bata taɓa zata ba. Tana ƙoƙarin tantance gaskiya ce ko karya ta tsinkayo sayayyar voice a cikin kunnenta yana faɗin.
"I'm so so sorry ranki ya daɗe, tuba nike yi, ba zan iya cigaba da danne abin da yake cikin zuciyata ba, ba zan iya shanyewa ba, dan haka ina mai baki hakuri da kalaman da zasu fito daga cikin bakina, ban san a yadda zaki ɗaukesu ba, na san matsayina da naki ba ɗaya bane, amma dik da haka ba zan iya ƙasa faɗa ba, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki yi hakuri".

"Ina.............. Wayyo ya Auta zata ji idan ya bayyana mata sirrin dake ransa? Abin da ta jima tana tsumayi! Ya waɗan nan masoya zasu tsinci kansu a yau? To su dai suka sani, sai Monday, bari in je in kora maltinata mai sanyi in huce, nima zuciyata ta kwanta ta nitsu............🥱

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

18

Ina sanki, ina sanki soyayya maras misaltawa, soyayya mara iyaka, ina kaunarki, ina jinki a jinin jikina, a kowace second zuciyata tana bugawa da sunanki, kece kawai nike kallah in ji ni a wata duniya ta daban, kina so na ko baki sona wannan dik bai dameni ba, abin da nasani kawai shi ne ina sanki, kuma zan iya mutuwa a kanki, sannan zan cigaba da sanki har bugun numfashina na karshe!!". In out of control ya rinƙa zuba kalaman!.

Tin da ya fara magana zafafan hawayen murna suka fara wanke mata fuska, fabaÉ—aya ji take yi kamar bata duniya, har wani iri take ji a cikin zuciyarta tamkar an É—aura mata ice block ciki. Sambatun zafafan kalaman kaunarta ya cigaba da zuba mata babu kakkautawa, yau ya samu damar amayar da abin da ya kwashi shekaru yana cinsa a zuciya.

Jin É—umin hawayenta suna zuba a kyawawan fararen kafafunsa ne yasa ya dakata da zuba mata kalaman kauna, a hanzarce ya É—an rabata da jikinsa dan ya tabbatar da kuka take yi ko akasin hakan.

Ganin da gaske hawaye sun wanke mata fuska ne yasa ya yi saurin sakinta, kansa ya dafe sa karfi, cike da danasanin biyewa zuciyarsa ya amayar da abin dake ransa ya fara faÉ—in.

"Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri! Ban yi tinanin kalamaina zasu yi maki zafi su sanyaki hawaye ba, kasa iya rike kaina yau na yi shiyasa, tuba nike yi". A tinaninsa dan ya ce yana sonta take kuka, yana ganin kamar zata ga ya ƙasƙantar mata da matsayi ne, bai kai ya sota ba shiyasa ya shiga bata hakuri!!.

Duka ta kai mashi a kirjinsa da É—an karfi. Cigaba da bata hakuri ya yi yana danasani, Allah sarki zuciyarsa har ta raunata ganin yadda ta shiga damuwa a ganinsa.

Duka ta sake cigaba da kai mashi a kirjinsa tana kuka da hawaye bibbiyu, yana tsaye bai hanata ba, sai ma hakuri da yake bata yana faÉ—in ta dakesa sosai in dai har hakan zai sa ta huce.

Cigaba ta yi tana yi tana ƙara sautin kukanta mai taɓa zuciyar mai sauraro. Sai da ta gaji dan kanta da dukansa, sannan ta kama rigarsa wajen saitin kirjinsa, ta ƙanƙame sosai tare da kwantar da kanta a kirjinsa tana wani irin shessheka mai taɓa zuciya. Cikin kuka mai sauti ta ce. "Why Hoorain? Why, why sai da ka azabtar da zuciyata, ka wahalar da ni sannan zaka bayyana mun sirrin dake ranka? Meyasa? Meyasa baka faɗa mun da jimawa ba? Menayi maka ka bani wahala har haka?". Tana maganar tana bubbuga kirjinsa dake kamar dutse.
Chapter 69 · 0% Book details