← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 242

Sashe 131

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tina waÉ—an nan kalaman yasa ta cire hijabin jikinta ta mayar da shi d-room É—insa, sannan ta dawo ta haye saman bed É—in, kwanciya ta yi haÉ—e da rufe idanunta tana tinanin abin da zai faru idan ya fito ya sameta kwance a saman bed É—insa.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A gefe guda kuwa, Dr Raj da ya bi Akka yaga babu wata matsala, ga kuma su uncle suna tare da ita, sai ya yi saurin ficewa daga É—akin, dan dik hankalinsa yana a kan yarinyar da suka yi karo É—azun. (Zee) Burinsa kawai ya sake sanyata a idanunsa dik da bai san wacece ita ba.

A karon farko yau ya yi wa garden sallama da É—an sauti. A lokacin Zee tana kwance saman sofa ta takure jikinta waje guda, har barci ya fara É—aukarta, dama kun san ta ce ba zata koma part É—in mama ba, gara mata ta kwana a waje, so shi ne ta yi kwanciyarta a nan har barci yana shirin É—aukarta.

Ganin alamar bata ji sallamarsa bane yasa ya sake yi mata sallama cikin natsuwa. A ɗan razane ta waro idanunta. Da yake ta fara barci sai bata iya gane wanene bane dik da hasken dake wajen. Ganin mutum yasa ta yi saurin miƙewa zaune idanunta a kansa, tana san tantance wanene?.

Wucewa ya yi izuwa saman sofa ya zauna yana kallanta shi ma, sai yanzu ta iya gane ashe mutumin da take mafarki ne a yanzu, wannan ɗan barci da ya ɗauketa har mafarkinsa ta fara yi. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Good evening".

Kallanta da yake yi irin kallan nan ne na ke special ce da kika sace zuciyar jinin Zuhair lokaci guda. Ta tafi da imaninsa ta yadda kunnuwansa suka ƙasa iya jiyo mashi sanyayyar muryarta tana ɗaga mashi gaisuwa. Sai da ta sake ɗaga mashi gaisuwar sannan ne ya fahimci ashe magana take yi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa mata.

Ganin alamar zama ya zo yi a wajen yasa ta miƙe tsaye domin ta koma ciki, sai satar kallansa ta kasan ido take yi, taga ɗan kyakkawan mamansa kani a wajen Ramish namu na amana.
Step biyu ta É—an taka zata taka na uku kenan ta tsinkayo sexy voice É—insa yana faÉ—in. "Ina kuma zaki je?".

Cikin natsuwa ta juyo, dik da bata san wanenne shi ba tana respect É—insa sosai. "Ciki zan koma". Ta bashi amsa tana É—an É—ago kallanta dan ta saci kallansa da kyau, tana san ganin face É—insa sosai amma bata san su haÉ—a ido. ........... "Ciki kuma?". Ya maimaita maganar da alamar mamaki a saman face É—insa. Kasancewar da turanci ta É—aga mashi gaisuwa sai kawai ya cigaba da yi mata magana da English É—in.

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e ciki. Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "To kafin dai ki shiga cikin z ki bani abata da kika sace kada ki tafi da ita". Ya yi maganar yana kara gyara zama haÉ—e da É—an wasa murya.
Zaro idanu sosai ta yi, take tsoro ya bayyana a saman face É—inta, a É—an ruÉ—e ta ce. "Wani abu kenan? Ni ban É—auki komai ba wlh". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka.

Miƙewa tsaye ya yi, a hankali ya yi step biyu ya matsa kusa da ita sosai, ƙasa ya yi da murya kafin ya ce. "Kawai ki bani abata tin kafin kowa ya jimu, kin san da cewa a wannan masarauta dik wanda ya yi sata cire mashi hannu ake yi ko?".
Kai ta girgiza alamar bata sani ba tana zaro idanu.
Kara taka step É—aya ya yi ya sake matsawa kusa da ita sosai, kashe muryansa kaÉ—an ya É—an yi, kun san doctors da shegen iya soyayya da iya magana. Da sauri ta É—an ja baya ganin ya matsota sosai, har cikin ranta ta ji tsoron kalamansa, dan ta É—auka da gaske an sace mashi wani abin ne zai kala mata sharri.

"To in baki sani bama yau kin sani, dik wanda ya yi sata datse idanunsa muke yi, ga shi ke kuma kin mun sata, amma babu komai ki dawo mun da abata da kika sace zan rufa maki asiri ba zan sanar da kowa ba bare a cire maki hannu". Yana maganar yana kara matsawa kusa da ita.

Kara tsananta tsorata ta yi, a hankali ta fara ja da baya tana san matsawa daga kusa da shi, dan yadda ya matsota ɗin nan kwarjininsa ya kara yi mata yawa. Sai dai kuma dik in ta taka taku ɗaya ta matsa baya, shi kuma zai taka taku ɗaya ya matsa kusa da ita, a haka suka rinƙa yin baya baya tana ce mashi ya yi hakuri ita wlh bata yi mashi satar komai ba, shi kuma yana ce mata a'a bai yarda ba sai ta bashi abarsa da ta sace kafin ta tafi.

A haka har suka kurewa bangon wajen, a É—an tsorace ta juya taga sun isa wall glass dake wajen rumfar, a tsorace ta juyo da nufin ta kallesa sai ta ga ya matsa dab da ita sosai, har suna iya jiyo numfashin juna, ya kuma yi mata rumfa da faffaÉ—ar kirjinsa yana kallan face É—inta. Lokaci guda ta ji ta yi nadamar fitowarta, gara mata É—akin mama ashe a kan wajen nan, dik sai ta shiga tashin hankali, a tinaninta wani abin zai yi mata.

Narai narai da idanunta da suka ciko da kwallah ta yi zata yi mashi kuka, dik zafinta dai shi ta kasa zazzaga mashi masifa ko ta faÉ—a mashi san ranta, ya yi mata kwarjinin da ba zata iya yin hakan ba. Yana tsaye ya dafa hannunsa É—aya a jikin bango ta bayanta, É—ayan kuma yana rike da wayarsa yana kallnta.

Sai da ya ga hawayenta sun fara salwanta a banza suna bin saman kuncinta ne ya É—an waro idanu kaÉ—an, calmly ya furta. "Ashe haka kike da tsoro da saurin kuka?". Ya yi maganar ba tare da ya zare kallansa daga kanta ba.

Cigaba ta yi da kukanta bata bashi amsa ba, dan bata da abin faÉ—e. ÆŠan nisawa ya yi tare da furzar da iska mai É—an É—imi daga bakinsa, sannan ya ce. "To ai ke bama ki tambayi abin da kika sace mun É—inba da kika tsaya kina mun asarar hawayenki".

Sai a lokacin ta ɗago manyan idanunta kaman na kawunta Sadiq, a cikin nasa idanun ta sauke kallanta, lokaci guda sai ta ji kukan nata ya tsaya cak sakamakon wani irin kallo da ya wurga mata mai narkar da zuciya, bata san time da ta shanye kukan ba, sai ji ta yi hawayen sun dai'na zuba. Da sauri ta yi ƙasa da kanta, kun dai san mu Nigerians da kunya kamar me muke.............🥱

Zira wayarsa a cikin aljihun wandan sleeping dress dake jikinsa ya yi, sannan ya sanya hannunsa ya riƙo hannunta ɗaya, ƙasa ya yi da murya cikin wani irin salo mai kwantar da hankali ya ce. "Malama wadda ban san sunanta ba, kuma ɓarauniyata maza bani abata da kika sata, dan babu in da zaki je sai kin bani kayana". Yana magana yana ɗaga gera guda kamar wani...................🤫

Muryarta na sarkafewa saboda kuka, ga wani shessheƙa da take yi, kun san mutuniyar akwai zuciyata, so sai shessheƙa take yi alamar zuciyar tana a kusa, da kyar ta ce. "Allah ni ban sace maka komai ba, dan Allah ka yi hakuri ka barni in ta fi ciki". Ta yi maganar cike da san ta kwace hannunta daga rikon da ya yi mata, saboda a takure take, bata saba ba.

Shi kuwa kara rikota da kyau ya yi, a karo na biyu ya sace cewa. "To ai baki ma tambayi abin da kika sata mun É—in ba"........ Kawar da kallanta daga kansa ta yi tare da cewa. "Me na sace maka to?".
ÆŠan rankwafo kanta kaÉ—an ya yi, dan ya fita tsawo sosai, a dai'dai saitin kunnenta ya kawo É—an bakinsa, kasa kamar mai raÉ—a ya ce. "Zuciyata kika sace mun, kuma sai kin bani ita kafin ki tafi daga nan".

Abin ku da ita ba soyayya ta taɓa yi ba, hasalima kunga ta tsani maza, so bata san komai ba, sai ta zaro idanu sosai, cike da ruɗani ta ce. "Zuciya kuma?". ......Kai ya jinjina mata alamar e.
"Ta yaya ake satar zuciya kuma shi da yake cikin jikin mutum?". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kansa...... Ya fahimci tabbas wannan yarinyar bata san me soyayya ba, infact bama ta taɓa yin soyayya ba, ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba, dan dama kun sansu da bala'in kishi, sun fi dik wasu nau'i na larabawa kishi, so sai ya ji daɗin ya yi sa'a shi zai fara koya mata soyayya kuma ya aureta da wuri dan ma kada wani ya ganta ya ce yana so.

Tab kuna ganin King zai aminta Dr Raj ya auri Zee kuwa? Kun dai san shi da kabilanci ko? Ya aka yi na Mahnoor da Jaish ma? Kuma kun ji ya ce dikka Æ´aÆ´ansa a cikin Æ´aÆ´ansu uncle Rahab zasu yi aure ko? To muje dai zuwa, zamu gani yadda za'ayi.

"Kin taɓa yin soyayya?" Ya jefa mata tambayar cike da fargabar amsar da zata bashi, dan in ta taɓa yin soyayya Allah zuciyarsa zata yi ciwo sosai saboda kishi, dik da yana ganin alamar kamar bata taɓa yin soyayyar ba, amma dai gara ya tambaya ya ƙara tabbatarwa. Sai harbawa zuciyarsa take yi kamar wanda zai shiga court kuma yana sa ran hukuncin kisa za'a yanke mashi, dik saboda fargabar amsar da zata iya fitowa daga bakinta ne fa.

Kai ta girgiza mashi kafin ta buɗi baki ta amsa da. "No, ban taɓa yi ba kuma bana sha'awar in yi".................... Wani irin daɗi da ya lulluɓe zuciyarsa ne har bai san time da ya ɗan matse hannunta da yake rike da shi a cikin nasa ba, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke a bayyane har sai da yasata kallansa a cikin ido.
Chapter 131 · 0% Book details