← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 242

Sashe 68

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba King ya shiga duniyar da ba'a iya magana sosai, sai kawai ya gyaÉ—a mata kai alamar ya yarda, da kyar ya iya amsawa da ya yarda. Wani irin daÉ—i ta ji da har yasa ta shiga kara rikita shi da kyau.
Haka suka kashe junansu da soyayya na tsawon lokaci har suka raya darensu kafin babyn Khadija dake kwance a gefensu ya fara kuka. Da kyar King ya iya saketa ya koma gefe ya kwanta yana jin wani irin farinciki, ita kuwa ta fishi shiga farinciki saboda ta samu ya amsa mata buƙatarta, ko ya dawo cikin hayyacinsa bai isa ya musa mata ba, saboda ya rigada ya amsa, ta nan momma take cin galaba a kansa a kullum, amfani da karfin sha'awarsa take yi ta cinma buƙatarta, ba faɗa bare ɓata rai da kunci, cikin ruwan sanyi.

(Ina team Ramish? Yanzu na gano a ina Yah Ramish ya koyo wannan iskancin na sanya sexy night sleeping dress, gadan jaraba aka yi,😅 da alama King ya gada wajen hegen feeling 🥱😅 ba ruwana kar ace na ce, bari in yi ta nan🥱)

Gyara kayan jikinta momma ta yi, ta É—auki babyn Khadija ta sauko kasan bed É—in, King ya yi aiki iya aiki sai ya kwanta yana binta da ido har ta zago ta side da yake, dukawa ta É—an yi, kyakkyawar sumbata ta bashi a kumatu tare da ce mashi good night.

Zata juya ya yi saurin riko hannunta, idanunsa a kan face É—inta, kamar mai raÉ—a ya ce. "Zaki dawo?".

Me king yake nufi da zata dawo?...….......🙄 Kash ashe fa surukina ne baban Guyson ɗina, bari dai na yi shiru to kada ace na yi rashin kunya na je ɗakin sirirki da daddare na kallan mashi sirrinsa....🤭🥱😅

Momma da yake itama tana cikin yanayi mai sugar sai ta amsa da zata dawo. Sake hannunta ya yi tare da yi mata alamar ta matso da hannu. Yana yi kamar wanda yake a cikin maye.

Ba musu ta matsa dab da face ɗinsa, sumbata ya bata a kumatu kai ɗumi yana kallan face ɗinta, miƙewa ta yi tana ɗan sakar mashi murmushi ta nufi waje. Sam king bai kalli babyn Khadija da kyau ba.

Kai tsaye ɗakin mama Haulat ta nufa da babyn, yunwan dare ya tashesa. A saman dadduma ta isko mama Haulat tana karatun Alqur'ani mai girma, kwantar mata da babyn ta yi a saman bed, sannan ta ce. "Ki bashi madararsa yana jin yunwa, sannan da safe ki sameni a ɗaki ina da magana dake". Bata jira amsarta ba ta yi saurin ficewa dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta su cigaba daga in da suka tsaya, dan basa gajiya da juna, momma tana shan gyara, kayan gyaranta daga Dubai ake kawo mata su, shiyasa King baya raga mata.................🥱

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

4:00 na asuba, Jawad ne ya fara farkawa daga nannauyar barci da ya É—aukesa tin karfe 3 na dare, barcin awa É—aya ya yi, yanzu haka bai so farkawa ba ya daure ya tashi saboda tafiya da yake gabansu.

Bai waiwayi Chuchu ba ya wuce toilet dan ya yi wanka ya yi shirin zuwa masallaci ya zo ya gabatar da rakatainil fajir.

Sai zuba barchin wahala Chuchu take yi, ta jima bata samu barci irin na yau ba. After some minutes ya fito ya shiga dressing room.

Arabs jallabiya ya sanya a jikinsa launin ash colar, cikin bedroom ɗin ya dawo. A hankali ya haye saman bed dan ya tasheta. Hannunsa dikka biyu yasa ya tallabota a kirjinsa, fuskarta ya zubawa idanu yana matukar jin tausayinta, Allah sarki ta sha kuka da kunci a lokacin da aka ce Rizwan za'a aura mata, bata gama warkewa daga wannan kukan ba ta ɗaura da na ɓatar Auta, har ta yi rama idanunta sun kara girma.

Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallanta kafin ya matso da face ɗinsa dab da ita, ya ci burin dik ranar da ya mallaketa ba zai taɓa ɗaga mata kafa ba sai ya ɓareta a ledarta saboda ta jima kyanta yana rikitasa, ya jima yana mafarkinta suna chaskale, sai dai shi kansa a yanzu ba zai so ya yi mata komai ba saboda tashin hankalin da suke a ciki.

Sumbatar É—an bakinta ya yi hakan yasa ta É—an motsa, kamar mai raÉ—a ya furta "Jannawad".

Cikin magaggin barci idanunta a rufe ta ɗan yi miƙa kaɗan tare da amsa mashi da na'am.

"Tashi ki yi wanka ki yi sallah sai mu tafi ko?".

Eyelashes É—inta ne suka fara kerma alamar tana san buÉ—e idanunta, sannan ta É—an tsuke bakinta kaÉ—an. Sosai ya ji hakan a ransa, sai ya ji mamar ya manna mata kiss.

A hankali ta waro idanunta a kansa, haka kawai ta tsinci kanta da sakar mashi cool murmushi. Sam bai yi expecting hakan daga gareta ba, ya yi zatan da kuka zata tashin masa kamar yadda ta yi barcin, amma sai yaga akasin haka. Wani irin bargon farinciki ya ji ta lulluɓesa har ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.

A shagwaɓe ta ce. "Yah Jawad barcin fa bai isheni ba".
Tsintar kansa ya yi da jin tongue É—insa ta yi mashi nauyi, kura mata idanu ya yi sosai, tin da aka fara maganar bikin Rizwan sai yau ya ji sanyi ta ratsa ransa.

"Yah Jawad tinanin me kake yi?". Ta sake jefa mashi tambayar tana kai hannunsa saman kyakkyawar sajensa dake kwance luff.

"Tinaninki nike yi my Jannawad". Cikin salon soyayya ya faɗi hakan ........ Kara ƙayata murmushinta ta yi, a hankali ta fara shafa sajensa izuwa saman lallausan kumatunsa.

Wani irin shock ya ji har tafin kafarsa, tsikar jikinsa ne ta fara tashi yana jin wani irin bakon yanayi.
"Yah Jawad Allah ina sanka sosai". A ɗan shagwaɓe ta faɗa. Da kyar ya iya cewa. "Da gaske?". Ya jefa mata tambayar yana kallanta kamar zai cinyeta da ido.

ÆŠan turo baki ta yi tare da girgiza mashi kai alamar a'a ba da gaske ba tana wurga mashi kallo mai cike da hararar soyayya, sanna ta zame hannunta daga kan kumatunsa irin ta yi fushin nan.

"Sorry my Jannawad, kada ayi fushi dani, zumar soyayyarki na lasa yasa word É—ina suke kubce mun"............... Bata yi mashi magana ba, ta mayar da kanta saman kirjinsa ta kwnatar, ta rungumesa da kyau tana turo baki.

"Meyafaru kuma rigimammiyata?". Ya yi maganar yana kai hannunsa saman face É—inta.
"Ni Yah Jawad mun ɓata fa".

"Ba zaki iya ɓatawa dani ba ai". With confidence ya yi maganar. "Meyasa ka ce haka". Ta tambaya tana riko hannunsa dake saman kumatunta.

Matso da face É—insa dab da ita ya yi, kamar zai raÉ—a mata magana a kunne, sai kuma ya canza hanya a in da ya kai É—an bakinsa saman nata. Cike da so da kauna haÉ—e da salo ya fara bata hot kiss, abin da ya jima yake tsumayi, in baku manta ba har gizon yana yi mata kiss idanunsa suke yi mashi a baya kafin aurensu.

Yana yawan mafarkin yana kissing na É—an bakin nan nata, ashe zai yi hakan da izinin Allah. Bata hana shi ba, dan ita ma tana dakon wannan rana, lips É—insa suna burgeta sosai, dan haka sai ma ta tayashi, cikin nitsuwa ta fara bashi kiss mai zafi ita ma.

Ba ƙaramin kara rura wutar sha'awarta a ransa ta yi ba, zame hannunsa dake cikin nata ya yi, cikin nitsuwa ya mayar saman kanta, a hankali ya zame hukar kayan barcin dake jikinta, gashin kanta ya fara watsawa yana ƙara matseta a jikinsa.

Ita kuma hannunta É—aya ta zira a bayansa, É—ayan kuma a saman shoulder É—insa, ta kara narkewa a jikinsa tana binsa da salo na musamman, ta datse idanunta irin wai kunyarsa take ji, shi kuma ya kura mata ido yadda abin zai fi kara mashi armashi.

Sun ɗauki a kallah 5 mins haka kafin cikin dabara ta zame bakinta daga nasa, dan ta lura bashi da niyar saketa. A fili ya furta alhamdulillah, dan ya ɗanɗani abin da ya jima yake tsumaya. Ƙoƙarin barin jikinsa ta fara yi ba tare da ta buɗe idanunta ba. Dan rashin kunya wai kunyarsa take ji.

Da sauri ya rikota, kamar zai saka mata kuka ya ce. "My Jannawad ina kuma zaki tafi".

Da sauri ta buɗe idanunta jin yau ya yi magana a shagwaɓe, sai ta ji kamar bashi ba, ya yi mata kamar muryar guyson. Sarkafewa idanunsu ya yi cikin na juna, kamar zata yi kuka a shagwaɓe ta ce. "Yah Jawad wanka zan je in yi in ɗauro alwala fa".

"Kasancewarki a jikina ya fi wankar, lokacin sallama da saura, Please stay with me ko da na 20 mins ne kin ji?".

"Mezaka bani to idan na tsaya?". Ta yi maganar tana É—aga mashi gera......"Mekike san in baki?"........ Manuniyar yatsarta ta É—aga ta saita kirjinsa da shi. "Kai nike so".

HaÉ—e goshinsu waje guda ya yi. "Ni ai mallakinki ne my Jannawad"......

"Yah Jawad kasan me?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai sani ba. Ɗan kawar da kallonta daga saman face ɗinsa ta yi, kamar mai raɗa ta ce. "Your lips is so sweet wlh, kuma fa....." Sai kuma ta yi shiru ta ƙasa ƙarisa maganar.

"Kuma fa me?". Cike da farincikin jin maganarta ya yi tambayar, sai ya ji kamar ya maida ta cikinsa dan daÉ—i.

Bata yi magana ba, sai ta ɗan miƙe kaɗan, ta kai mashi sumbata a saman lips ɗinsa. Ya fahimci wani kiss ɗin take so kuma tana jin kunyar faɗa mashi, wanda ya yi mata bai isheta ba, dan haka sai bai bari ta zame bakinta daga sumbatar ba ya capki lips ɗinta ya dasa daga in da ya tsaya.

Ajiyar zuciya ta sauke dan ta ji daɗi, ya iya kiss mai mantar da mutum in da yake shiyasa ta nemi kari. A hankali ya kwantar da ita a saman bed ɗin bakinsu manne da juna. Rumfa ya yi mata da kirjinsa, ya sanya hannunsa a wuyarta yana ɗan shafawa izuwa shoulder ɗinta, a matse yake yana san taɓa tula tulanta amma yana shakkar yin hakan.

Ita kuma ta tura hannayenta a cikin gashin kansa, cike da kaunarsa ta fara wasa da gashin, bukata ya biya ta mallaki abin kaunanta.
Chapter 68 · 0% Book details