Sashe 95
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kalaman Khadijah sun taɓa zuciyarta, haka zalika wannan abin da ya faru yaja ta kara jin tsanar uncle Jahiz, lallai ba shakka a yanzu ta yarda Khadijah ta ɓoye mata babban al'amari fiye da wanda ya faru da ita abaya, tabbas akwai wata a ƙasa, wlh ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba uncle Jahiz ne a cikin wannan hoto, kuma tana kan bakarta babu gudu ba ja da baya. Tashin sense, wai wani irin ruɗanine wannan? Mekuke tinani? To dai ku kwantar da hankulanku, komai bala'in ruɗani da zaku shiga alkalamina zai warware maku gaskiya, zan zaƙulo maku meyake tsakanin uncle Jahiz da Khadijah and meyasa Zee ta ce shi ne a jikin hoton, shi kuma ya nuna kamar ba hakan bane? To mu dai je zuwa, lokaci ne zai warware mana.
Saman chair dake kusa da bed É—in ya zauna, a tinaninsa kukan da Khadijah take yi na murnar ganin Zee ne, dan ya ga ita ma Zee É—in tana ruwan hawaye, sai ya zuba masu idanu yana kallansu.
Massage ne ya shigo wayarsa, hakan yasa wayar ta ɗan yi ƴar ƙara. Zarota daga aljihunsa ya yi kallansa a kan Khadijah, shi dai yasan wlh ya taɓa kallan wannan fuska, kuma shi bai taɓa zuwa Nigeria ba sai wannan zuwan nasu, to a ina ya taɓa kallanta kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta.
"Ka samemu a meeting room". Shi ne sakon da ya shigo wayarsa, uncle Abbas ne kuma ya turo mashi wannan sako. Yana gama karantawa ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce masu su kasance a tare da yamma zai dawo ya ɗauki Zee. Dik cikinsu babu wadda ta iya amsa mafi, basu da bakin magana.
Bai wani damu ba yasa kai ya fice da sauri, yana fita Khadijah ta hau jerawa Zee tambayoyin a ina ta haÉ—u da wannan mutumi? Yadda take jera mata tambayoyi zaku fahimci hankalinta a tashe yake.
"Khadijah ki faɗa mun gaskiya, dan girman Allah ki fitar da ni duhu, ni ban ce karya kike yi mun ba, amma dan Allah ki sanar dani abin da yake a ɓoye a karkashin zuciyarki, ki sanar dani alaƙar Jahiz da wannan hoto na cikin akwatinmu, dan girman Allah ki faɗa mun shi ne baban baby Junior?".
Jin karshen zancen Zee yasa ta yi saurin kai hannunta saman cikinta, sai a lokacin tasan ma babu cikin a tattare da ita, a tsorace ta kai kallanta a kan Zee. "Zeezee ina cikina? Ina yake?".
Zama a gefenta Zee ta yi, cikin nitsuwa ta fara kora mata bayani yadda komai ya wakana har suna tsinci kansu a wannan hospital ɗin. Shiru Khadijah ta yi tana jinjina al'amari na ubangiji, idan Allah ya tashi amsa addu'arka sai ya haɗaka da bayinsa da baka taɓa zatan haɗuwa da makamantansu ba, kuma su taimaka maka, lallai ne ba shakka addu'a bata faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, wannan jinkirin kuma shi ake kira da jarabawa ta Ubangiji, Allah zai jarrabaka da jinkirin amshi yaga zaka cigaba da yarda da tawakkali da shi ne ko dai imaninka bai yi karfi ba?! Lallai ba shakka su Khadija sun yi hakuri, sun kuma ɗauki wannan jinkiri a matsayin jarabawa wanda a yanzu Allah yake basu sakamakon hakurinsu cikin ruwan sanyi, tun da momma ta ce sai an bi masu hakkinsu hakika ba makawa sun san ikon Allah ne da ya amsa addu'oin da suka jima suna yi.
"Zee yanzu dai ki kyaleni na huta, idan na kara samun sauki sai mu yi magana". Cewar Khadijah. Na'am da hakan Zee ta yi suka cigaba da jinjina girman Allah.
•••••••••••••••••••••••••🔥
A ɓangaren Jaish kuwa, gobe Monday zai koma bakin aikinsa, sai dai fa har yau kudurinsa na bincike a kan wannan ma'aikata da suka tsunduma shi cikin wahala yana nan a ransa, bai janye ba!!.
After one day. Aneesa, Fanan, Chuchu ne suka shirya cikin uniform É—insu na school. Chuchu ta sha kukan rashin Auta, da farko har ta ce ita ba zata je school É—in bama, daga baya da Yah Jawad ya rarrasheta sai ta shirya suka tafi, da kansa ya kaisu, sannan shi ma ya dawo ya shirya zuwa office. A tare da Jaish suka tafi kamar yadda suka saba.
Sarina kuma bata da class,.tana guda. So gidan ya rage daga Sarina, uncle Jahiz, uncle Taheer, uncle Abbas, su momma, King, Guyson yana nan, su twins, sai Zee da suke asibiti. Aunty MieMie tana part É—inta.
••••••••••••••••••••🕊ï¸
Momma da Mama Haulat ne zaune a bedroom na monma suna tattaunawa a kan irin dressing É—in da yakamata su yi wa Mahnoor a lokacin da zasu kaita gaban su King.
Mama Haulat ta kawo jerin kayayyaki na alfarma masu bala'in kyau da tsada da yakamata su shiryata a ciki domin kaita, momma tana dudduba hotunan kayan ne, dikka cikin waÉ—an da ta yi oder su daga Dubai ne, tun jiya aka kawo kayayyakin kusan mota guda.
Mammie da Sarina kuwa, suna nasu shirin dan su zo part ɗin King su kalli Mahnoor, su kalli dame ta fi Fanan? Sun san cewa King ya ce nan da karfe 8 na safe dai'dai a kawo mashi ita ya ganta kafin ya fita fada, shi ne suma suke sauri dan su zo su ganta, saboda sun san idan King ya aminta da ita yadda momma ta kwallafa rai a kan sonta ba lallai su rinƙa samun damar ganinta ba, kunga in King ya aminta da ita zata koma part ɗin Jaish ne, to da ni da ku dai mun san dik rashin kunyar mai rashin kunya baya tinkarar part ɗin Jaish, bayan Auta da Guyson, King and Yah Jawad, sai momma da mama Haulat ne kawai suke iya shiga part ɗinsa, ko su Omaid basa kaunar dosar wajen, dan kun san dalili.
So sun san tana shiga part ɗinsa ba zasu taɓa samun damar ganinta yadda yakamata ba.
Uncle Jahiz, uncle Abbas, King, Akka su ne zaune a cikin parlon King suna jiran momma, King ya buƙaci da Mummyn Chuchu da Mama and Mammie dik su zo. Akka ta samu lafiya yanzu, jikin ya yi kwari, sai dai fa masifa ya karu, yaseen kana taɓota kaɗan yanzu ka shiga talatin, sauke haushin rashin Spender zata yi a kanku.
To King ya bata labarin Jaish ya yi aure, shi ne ta ce wlh bata yarda ba, dan haka dole a warware wannan aure, da kyar autanta uncle Jahiz ya shawo kanta a kan ta yarda ta kalli Mahnoor ɗin ko sau ɗaya ne, taga idan bata dace da Jaish ba sai a warware auren, to shi ne dalilin hallararta a parlourn King, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin shiga ta alfarma, eh mana uwa ga manyan kai ba, ta dake cikin alkyabbar na girma, sai wani kafafa take yi, har da cewa ko ta ga Mahnoor fa ita ba zata taɓa yarda da wannan aure ba, uncle Jahiz da yake yana bin bayan Momma dan tana rufa mashi asiri bakinsu ɗaya, sai ya ce da Akka e dai su bari Mahnoor ɗin ta zo aganta.
Wlh uncle Jahiz da momma bakinsu É—aya, ita ke goya mashi baya, harta batun tafiyarsa kwallan kafa ita ta tsaya mashi, da Akka taki yarda, amma da momma tasa baki sai suka fi karfin Akka dole ta yarda, so in short dik abin da ya É—ebo rufewa suke ita da shi abinsu, shiyasa kuka ga suna mugu mugun shiri da juna, ya fi santa fiye da sauran matan King.
Saida momma ta tsaya ta hantse ta zaɓawa Mahnoor wani haɗaɗɗen gown mai kama da weeding gown, daga ta sama daidai da ita zuwa waist ɗinta, kasa ya yi bala'in buɗewa kamar umbrella, rigar launin pink ne da ratsin golden, ga wasu ƙayatattun duwasun alfarma masu kyalli da suke walwali suka kara ƙawata kayan rigar, sannan ga wasu manyan zanen flowers a jikin kayan, rigar ta haɗu, ga tsada kamar me.
Wasu half cover masu kwalliya da duwatsun lu'ulu'u momma ta zaɓa mata, takalmar launin golden kalar kwalliyar jikin rigar, ai ku daga jin kwalliyar dutse mai daraja wato lu'ulu'u a jikin takalmar kun san kuɗinsu ya wuci baki ya faɗa.
Dankareran alkyabbar launin golden kalar takalmarta momma ta fidda mata, alkyabba ce wanda King Badeen wato mahaifin momma É—in ya saya mata a lokacin da za'a kai ta gaban King Abdul Malik mahaifin King Zuhair kenan, a lokacin ya saya mata su guda shidda, to da guda É—aya ta yi amfani sauran biyar É—in sunan sabbi gal, a lokacin da tasa wannan alkyabbar sai da kowa yasan e lallai Æ´ar the most powerful King ta fito, alkyabbar ce wanda ba'a samunta a ko'ina, kwalliyar jikinta da duwatsun lu'ulu'u aka yisu, haÉ—uwar alkyabbar baki ba zai iya faÉ—arsa ba.
Mama Haulat sai da ta sha jinin jikinta jin cewa momma zata bawa Mahnoor wannan alkyabba mai dajara tasa, domin kuwa ita tasan darajar waÉ—an nan alkyabbars É—in, momma kuwa dama matan Æ´aÆ´anta ta ajiyewa, sai kuma Allah yasa tana kaunar Mahnoor É—in, kunga kuwa fin haka ma zata iya yi mata.
Dik jikin mama Haulat ya yi sanyi ganin kyautar momma ga Mahnoor, amma haka ta miƙe ta karɓi alkyabbar, nauyi sosai yake da shi, saboda duwasun lu'ulu'u da aka kawata kyalliyarsa da shi. Haka ta nufi waje da shi, kai tsaye ta je ta ɗauko kayanda momma ta zaɓa za'a haɗawa Mahnoor ɗin da su.
Kai tsaye É—akin gyara ta wuce da su. Momma ma wanka ta je ta yi ta shirya, sam babu faÉ—uwar gaba a tattare da ita a kan wannan matsala, domin ita É—in macece mai jajircewa a lamuranta, bata san faÉ—uwa ba, tana da yakinin zata yi nasara.
Su mummyn Chuchu dik sun hallara a parlourn King momma kawai ake jira, Sarina da shegen gulma har da wani zuwa ta zauna kusa da uncle Abbas, ta wani kwanto a jikinsa dik dan gulma, kamar da gaske haka take jinsa a ranta, kawai tsabar san kallan Mahnoor ne. One funny thing kuma shi ne yau sai ga Sarina da alkyabbar, saboda su King suna wajen, sai ta yi shigar mutunci, ni ko na ce ashe rashin kunyar tata ta karya ce ƴar ƙaniya.