← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 242

Sashe 36

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dik tsananin taurin zuciya da jarumta haɗe da dakiya irin na King sai da ya shiga tsananin tashin hankalin da yake ƙoƙarin fita hayyacinsa a lokacin da suka tabbatar da bata a cikin Kingdom ɗin, dan dik wasu sassasa da mutum zai iya zuwa a cikin kingdom ɗin nan sai da suka je suka duba.

Kowa ya tashi daga barci har da su Mummy, King ya tashi kowa, commander Zafar kam shi ne mutum na uku da King ya fara tasa daga barci bayan uncle Abbas da uncle Taheer.

In short Akka ce kawai ba'a sanar da ita abin da yake faruwa ba, ita ma saboda bata da lafiya ne kada ciwon ya kara tsananta suna iya rasata a kan hakan, shi ne yasa suka ki sanar da ita.

Jigum jigum suka zauna cikin parlourn King, su commander Zafar kuwa sun gama kewaye kota ina da warrios a cikin kingdom É—in anata kai komo wajen nemanta.

Lokacin da commander ya zo sanar da Hoorain ga halin da suke ciki gimbiya Zunaira ta ɓata, sai ya tarar da shi da zazzaɓi mai tsananin zafi, jikinsa ta yi zafi jaw kamar wuta, hakan yasa ya fasa gaya mashi halin da ake ciki, ya ɓoye mashi, ya ce ya zo duba shi ne kawai.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Gabaɗaya family hankulansu in ya kai miliyan ta ya tashi, harta maman Yah Ramish ta shiga damuwa matuƙa, mummyn Chuchu har kusan kwallah ta yi, Momma kam ba'a magana, tana tsaye taki zama, kamar wanda aka sassaƙa.

Kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare zaune a cikin parlon King, lokacin da aka yi kiran sallar asuba ta farko King ya fito waje hararbar kingdom ɗin, dan yana zargin warriors da commander zafar ya wakilta wajen nemanta a dik wasu lungu da saƙo na kingdom ɗin basu duba da kyau ba, so sai ya fito da kansa dan ya duba.

Momma ta so binsa, sai dai kunsan a doka irin tasu ba zata fita waje ba, killacesu ake yi, matan sarki bayi da warrios basu da damar ganinsu, suna da ƙaidoji da dokoki masu karfi.

So Mummyn Chuchu ta riketa ta hanata fita.

Dik yadda King yake tinani abin ya wuci nan, dan babu in da basu duba ba babu ita babu labarinta, da kyar uncle Abbas ya rarrashesa suka koma É—akunansu dan su shirya zuwa masallaci.

Yau gabaɗaya zargin Momma a kan maman Yah Ramish yake, dama ta jima tana zarginta, kawai tana dannewa ne saboda bata san tashin hankali, amma yau a kan ɓatar Zunaira wlh ba zata ragawa kowa ba, dole ta fito da zarginta ta ɗaura a kan wanda zuciyarta take raya mata!!.

Lokacin da su King suka dawo daga masallacin sallar asuba, babu ɓoye ɓoye suka sanar da matan cewa Auta fa bata cikin kingdom ɗin nan, ta ɓata, dan haka kowa ya zage da yin addu'ar Allah ya bayyanata.

King yana sanar da su gabaÉ—aya parlourn ya dauki shiru mai tsananin girma fiye da kowanne kuka. Momma zube gwiwowinta a kasa ta yi, nan take hawaye suka fara gudu ba kakkautawa kamar ruwan kogin da ya ketare iyaka a saman face É—inta.

"Ba zan iya yarda ba! Ba zan yarda cewa Zunaira bata cikin kingdom ɗin nan ba! Ba zan iya yarda ta ɓata ba!"....... Haka ta fara sambatu, muryarta na kara tsananta kuka.

King da aka san shi da jarumta, yana tsaye a gefe kamar wanda ya rasa hanyar tunani. Idanunsa cike da hawaye da ba ya so su zubo, amma ba zai iya hana su ba. Ya harÉ—e hannunsa a saman kirjinsa, yana kallon momma ya kasa yin magana.

Guyson ne ya ce. " Dad Momma wai me na yi wa duniya har za'a kashe ni da irin wannan bakin azaban ciwo mai tsananin zafin? Da a É—auke Zunaira ai gara ni a kasheni!"............ Ya tambaya da muryar da ta nuna karayar zuciyarsa. Guyson mai saurin kuka yau dai hawaye taki fitowa, sabdoa azabar dake cikin ransa ba zata iya baiwa hawaye gurbin fita ba!.

Yah Jawad wanda idanunsa yake yi mashi gizon Auta tana tsaye kusa da guyson tana murmushi ne ya kasa iya furta word. Kamar ma baya cikin hayyacinsa sosai.

Su uncle Taheer sun kasa yin magana, sai kawai kukan zuci da suke yi. Fanan da ta manne da Chuchu ce a cikin ranta ta ce. "Auta ta kasance mai kawo dariya da farinciki a kan fuskar kowa dake gidan nan, ta sanya zuƙatan kowa a nitsuwa, sanyi idaniyar kowa, yanzu ace babu ita? Kai anya zasu iya ɗauka kuwa? Gurbin ta tamkar rami ne mai zurfi wanda babu abin da zai iya cikawa a zuƙatansu".

Kowanne daga cikin su yana tuna abubuwan da ta yi na alkhairi, irin murya mai daɗin da ke jansu cikin farinciki, yadda take cika gida da rayuwa da ƙauna.

Chuchu dai ganin abin kamar mafariki take yi, hakan yasa bata iya furta word ba, tana dai binsu da ido, gata nan gata nan kamar wadda aka sassaka ta kasa motsawa.

Momma kuwa kara fashewa da kuka mai sauti ta yi, hakan ya ja hankalin mummyn Chuchu a kanta, da sun afka duniyar tunanin ina Auta take? Jin kukan Momma yasa suka yi saurin karisowa in da take.

A tare Mummyn Chuchu da Maman Yah Ramish suka tsugunna a gabanta, a tare suka kai hannu suka rungumota.

Cikin ɗaga murya momma ta ce da mama kada ta sake taɓata!. Tashin hankali.

Nan fa kallo ya koma kansu a cikin parlourn, yadda Momma ta yi maganar ya girgiza kowa. King da yake tsaye kaman wanda aka sassaƙa ma sai da ya ji gabansa ta faɗi ya dawo cikin hankalinsa.

Mama da bata gane me Momma take nufi ba, a tunaninta saboda raɗaɗin rashin ƴar tata ce yasa take sambatu, sai bata saketa ba, sai ma ta yi ƙoƙarin goge mata hawaye dan ta rarrasheta.

A tsananin fusace momma ta kwace kanta daga riƙon mama, take ta fara huci kamar zakanya tana jin yunwa, cikin zafa ta ce. "Idan kika sake taɓani dik abin da na yi maki ke kika nema!!". Babbar magana!.

Ganin hakan yasa su Jawad gabaÉ—aya suka matso kusa da su, so suke yi su kwantarwa da Momma hankali da kalamansu, amma dikkansu babu wanda yake da kalmar da zai iya tinkarar momma da shi.

Dan haka sai dai suka matso suka tsaya jugum jugum kaman wasu gumaka.

Allah sarki Chuchu da ta ɗauki abin matsayin mafarki ba gaskiya ba, dik da haka hawaye ne yake gudu a saman face ɗinta kamar ruwan pampo, tana tsaye kamar wadda aka sassaƙa, da alama bata a cikin hanyacinta.

Wai a haka sun É—auka sace Auta aka yi, to idan suka san ta bar duniya mai gabaÉ—aya me kuke tinanin zai faru? Akwai bala'i gaskiya.

Da kyar King ya iya motsa laɓɓansa da suka yi mashi masifar nauyi ya furta kowa dake cikin parlourn nan ya je su kyale shi daga shi sai Momma bari su yi magana.

Babu musu kowa ya nufi waje, Mummyn Chuchu ta saki momma ta miƙe, a babban parlour suka haɗu suka zauna jugum jugum.

Chuchu ta kasa motsawa har sai da Yah Jawad ya tallaɓota ya ja suka fita.

King da Momma kawai aka bari a cikin parlon King, harta Guyson mummyn Chuchu ta ja shi sun fita wajen, kamar ba mutum ta rike ba, dik ya sake mata jiki kaman wanda ya sume, Allah sarki bawan Allah, da alama ya fita hayyacinsa ne.

King da momma sun ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa ta sirri, kafin daga bisani King ya rarrasheta tare da gaya mata wanda yake zargi da sace Auta wato king Al-Mustapah kenan, kuma ta kwnatar da hankalinta cikin ƙanƙanin lokaci za'a dawo mata da Auta lafiya lou In Sha Allah, yanzu za'a shirya dakarun yaki domin tinkarar Daular Qahtaniyawa, tun da sun tsokalo yaki dole a yakesu.

Aunty MieMie dai bata da labarin dik abin da yake faruwa, tana can ɓangarenta tare da mijinta. Tsabar tashin hankali yasa suka manta da ita ba'a sanar da ita ba!.

Momma da kyar ta hakura ta yi shiru, hakan ma dan King ya yi mata alkawarin dawo da Auta cikin kwana É—aya ne.

Cikin bedroom ɗinsa ta shiga ta kwanta, shi kuma ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin tafiya fada, nan ya buƙaci Commander Zafar da ya kira mashi Hoorain ya kuma haɗa kan mayaƙa tawagar farko.

Me zai yi wa Hoorain kuma?.

===========================🔥

Karfe 9 daidai gabaÉ—aya manya manyan jiga jigan masu faÉ—a a ji a cikin fada suka haÉ—u, hankalin kowa in ya kai miliyan a tashe yake, dik sun nitsuwa tsit suna cikin alhini, dik wanda ya É—aga idanu ya kalli fuskar King ba zai so ya sake É—aga idanu ya kallesa ba, saboda fuskar a É—aure take, uban kwarjininsa ta kara bayyana, zarra ga marasa adalci da san gaskiya kenan.

Yana dake saman kujerarsa, yau babu wargi bare wasa, su commander Zafar dik sun shiga taitayinsu, kowa yana nan bisa ƙaida, dik sun tattaro hankulansu a kan King Zuhair, shi kawai ake jira da ya yi magana.

Dai'dai lokacin da Hoorain ya dimfaro babbar kofar fada da nufin ya shigo ciki dan amsa kiran da King ya aika ayi mashi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan baya a cikin hayyacinsa sosai, dik ya firgice, tamkar wanda aka zarewa laka, yana yafiya yana jan kafafu tamkar ba sadauki Hoorain assistant commander ba, jarumi mai tafiya cike da zarra da kwarjini mai razanar da zuƙatan dik wasu warriors dake cikin kingdom ɗin, amma yau ya taho tamkar mace yana wani jan kafa.

Masu gadin kofar fada har sun bashi hanya, ya matsa gada da su kaÉ—an har ya kusa shiga fada, kunsan dai'dai in da suke tsaye domin gadin kofar akwai É—an tazara tsakaninta da kofar, a kasar stage na hawa suke tsayawa, kofa kuma tana sama.

So sun bashi hanya zai wuce, ya haura saman step É—ai É—ai har uku zai taka na huÉ—u kenan ya tsinkayo muryar King ya fara magana cikin kakkausar murya da zafa, dama ga voice É—insa da kaifin bala'i, hakan ya yi gaggarumin É—aga hankulan su commander.
Chapter 36 · 0% Book details